Pɑge 77 & 78

18 2 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 77- & 78*

*_(BANI DA LAFIYA, KUYI HAKURI BANYI EDITING BA) _*

Kayan drink ya sayo a kasuwar su Martina carton biyu, ruwan Paro lemon lacasera, peach, cock fanta duk na cikin cans. Daga nan 'yan kaji na kasuwar ya isa, kajin broilers guda goma da zabi biyar yasa aka gyara masa aka zuba a leda.

Sai buhun shinkafa ta cikin garara da carton din taliya da macaroni, man girki na turkey jarka daya, wanann sune kayan abincin sallar da ya hadowa su Hassanah, aka zubo masa a mota ya dawo wajen da ya bar Hassanar. Yana karasowa kuwa saura kadan a gama mata komai. Jira ya yi kamar tsawon mintuna talatin sannan aka kammala yi mata duk abinda za'ayi mata.

Tamkar amaryar da zata shiga daki gobe haka Hassanah ta koma, Habib ya biya kudin suka dauko hanyar gida. Shigarta motar keda wuya ta ga buhun shinkafar nan da sauran kayayyakin da ya sayo, bata tambaye shi ba, shima kuma bai ce mata uffan ba.

Bayan sun iso kofar gida ne yace da ita, “Ya ya za'a shigar da wannan kayan ciki?”

“Okay bari na nemo yara su dauka.”

Fitowa tayi daga motar ta kira wasu yara nan dake wasa a kusa da kofar gidan, suka dauki kayan suka shiga dasu duka suna murna suna masa godiya.

Babu wani mamaki da tayi, domin ya riga ya saba, tunda ta gansu a cikin mota ta tabbatar su ya sayowa. Haka halinsa yake baya jin nauyin fidda kudi ya yi hidima.
Inna ma ba tayi mamakin kayan ba  domin idan da sabo kam ya kamata ace sun saba da kyautar Habib. Dan haka farin ciki da murna shine abin yi.

Bayan gama shigar da kayan, Hassanah da Habib suka shiga tare, Inna tace, “Oh! Habib kai dai baka gajiya, irin wannan kaya haka? Ga wasu can ma ko fara taba su ba'a yi ba, to an gode Allah ya yi albarka.”

“Babu komai Inna ai mune da godiya da kula damu har muka girma muka zama na gari.”

Bai jima ba ya mike ya fito Hassanah ta biyo bayansa rakiya kamar yadda ta saba.  A kofar gidan dai dai da suka sake tattaunawa.

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora