༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 103 & 104*
Dariya Mustapha yayi, dakyar ya dago kai ya kalleta saboda kunya yace, “Doctor baki da dama wallahi.”
“Ai gaskiya ne bana son kana zama da yunwa, ka taso tun daga Gwammaja ka zo nan sannan kace wai a koshe kake, wannan ma ai wasa ne. Kula da kai shine burina, dan haka duk abinda ke nan naka ne sai ka cinye shi.”
“Hmm! Zanci dai wanda zan iya amma...”
Ta katse shi da cewa, “Ya isa ka ci kawai ka bar magana.”
Haka nan dai ta tilasta masa ya rika cin farfesun kajin kadan-kadan a hankali. Ba wani me yawa yaci ba, ya sake cewa, “Alhamdulillah! Cikina ya cika fal! Nagode.”
“Haba me ka ci a nan, gaskiya idan baka cinye ba, ba zaka fita daga dakin nan ba.”
Yayi murmushi tare da cewa, “Shikenan zan kara ci amma bari na dan huta.”
Murfin lemon Five Alive ta balle ta zuba a cup ta mika masa tace, “Ga lemo ma baka sha ba.”
A zahiri cikin nasa a cike yake soasai, amma baya son suna ja'inja haka dai ya karbi cup din ya kurbi lemon, kurba daya ya ajiye tare da cewa, “Doctor kada fa cikina ya fashe, ya cika over.”
“To shikenan na yarda ka koshi, amma kafin ka tafi sai ka kara.”
Ta fada tana masa wani irin kallo, ta tsura masa ido sosai ko kiftawa bata yi, matsawa kusa dashi tayi ta fuskance shi, yanayin kallon da take masa ya wuce tunani. Hatta da yanayinta ya canja, ta saki jiki dashi tamkar miji da matarsa. Sakonni ne birjik a cikin wannan kallo da take masa.
Shima martanin kallon ya rika mayar mata kawai ba tare da yayi magana ba, zuwa can ta sauke numfashi sannan tace,
“Ina alkawarina da kayi min?”Nisawa yayi tare da cewa, “Subhanallahi, wallahi na manta, goron sallarki ko?”
“Eh mana, amma baka manta ba fa, ka zo dashi ni na ganshi sai dai idan rowa zaka min?”
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."