༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 61 & 62*
Cikin murmushi kanta sunkuye tace, “Dama Inna ce tace kada na sake karbar kudin.”
“Aiko ba za'ayi haka ba, dole ne ki karbi kudinki na aiki, wannan shine ka'ida.”
Mami tace, “Ki rabu da ita tunda tace ba zata karba ba.”
“Kamar ya ya na rabu da ita, hakkinta ne fa, wahala take kuma sai a ƙi bata ladan aikinta?”
Hajiya na gama wannan maganar ta mike ta nufi sama. Kabir kuwa gyara zama ya yi sannan yace, “To ina tsarabar da kika zo min da ita?”
“Kai dai, sai kace idan an baka zaka iya ci. Ka ga marece ya yi bari mu shiga kitchen kafin a kira sallah, koda yake ke Mami baki da lafiya ko, bari ni na tashi.”
“A'a muje taren ai naji sauki tun da rana ma.”
Mikewa suka yi suka shiga kitchen, Usainah ta dubi Mami tace, “Gaskiya yayan nan naki bashi da dama, ko kunya baya ji sai ya yi ta faɗin abinda ya gadama.”
“Indai yaya Kabir ne kam zaki gaji da gani, yanzu ma ya dan rage a kan da can, kuma dan ma ya ga ke din me kunya ce kina nuna jin kunya shiyasa baya wasu abubuwan.”
“Hmm! Lallai kam a gaishe shi.”
“Kuma kin san me, wallahi yana da tsananin kishi. Kashinsa har ya fi na mata, sai kinyi a hankali.”
Suna aikace-aikace suna ta hirarsu har suka kammala komai, suka jera a kan tebur sannan suka yi sallar magariba.
*_BAYAN WATA DAYA_*
Ana sa ran ko yau gobe za'a ga jinjirin watan Ramadan, watan azumi. Al'ummar musulmai sai hada-hadar saye-sayen kayan azumi suke kamar yadda aka saba. Kasuwanni sunyi cikar kwari, mutane sunyi fitar farin ɗango, kudu da arewa gabas da yamma duk inda ka waiga jama'a ne.
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."