Pɑge 85 & 86

19 2 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 85 & 86*

Dariya Habib ya yi sannan yace, “Ranki ya dade ai girmanki ne, ko jakunkuna kike so za'a cika miki, ya sallah?”

“Hmm! Sallah alhamdulillah, ga ta an fara shagali.”

Hassanah ta zauna ta dubi Mami tace, “Sannunku da zuwa, ashe kuna hanya. Ya gida ya su hajiya, da fatan kunyi sallah lafiya.”

Mami tace, “Lafiya lau, ai mu fishi muke dake tunda kin ƙi kawo mana ziyara sai dai mune muke zuwa.”

Hassanah tayi dariya tare da cewa, “To ayi hakuri ai zan zo ne, lokaci ne babu isasshe.”

To nan dai akayi gaishe-gaishe, Habib da Kabir suka gaisa cikin fara'a da sakin fuska.

Habib ya dubi Usainah tare da cewa, “Wannnan ne angon namu kenan?”

Murmushi tayi bata ce komai Habib ya cigaba da cewa, “To Masha Allah, Allah ya sanya alkairi. Yallabai ina maka fatan alkairi.”

Habib ya fada tare da miƙawa Kabir hannu suka sake yin musahaba, shima Kabir yace, “Nagode nima ina maka fatan alkairi.”

Inna da Baba ne suka shigo falon, Habib da Kabir suka zame ƙasa daga kan kujeru suka gaida su cikin matukar ladabi da girmamawa. Mami ma ta bi sahunsu Kabir din wajen gaida su Innar, tare da yi musu barka da shan ruwa.

Jim kadan bayan an gama gaishe-gaishen Kabir yace, “To zamu wuce.”

Inna tace, “Da wuri haka ko hutawa baku yi ba, kamar ana korarku. Ai dai kun tsaya ku ci abinci ko?”

Hassanah ta karɓe zancen da cewa, “Wace irin tafiya kuma ana zaune ƙalau, yanzu fa kuka zo? ”

Tana fada ta mike ta nufi kitchen, sai ga ta da abinci kashi-kashi ta aje ta koma ta zo da lemuka da ruwa.

Kabir ya sake cewa, “Wallahi tafiya zamu yi, daga nan ma wani wajen muka nufa, akwai guraren da zamu je da yawa nan gaba. Amma gobe zamu dawo ai.”

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now