༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 81 & 82*
Shi kuwa Mustapha jikinsa ya gama warwarewa sosai, domin har ya cigaba da yin azumi, ya yi na jiya da na yau karshe. Kuma da alama ya dauki dangana, ya hakura ya mika ƙoƙon bararsa wajen Allah da ya sauya masa da mafi alkairi.
Washe gari sallamarsu daga asibiti, Nurse ɗin nan ta kira shi da yammaci take ƙara yi masa ya jiki. Suka dan taɓa hira daga karshe take ce masa, “Sai na zo karbar goron sallah na ko?”
Mustapha ya yi murmushi tare da cewa, “To ba komai sai kin zo din, amma kuma baki yi kama da masu cin goro ba sai dai a baki chewing ko sweet.”
“Hmm! Me zai hana naci goro?”
“To ai na ga ku likitoci kuna gargaɗi a kan cin goro, kin ga kuwa me dokar bacci ai baya ɓige da gyan-gyaɗi ba.”
“Hmm! Hakane kam, amma dai ni ina cin goro, dan haka a tanadar min masu kyau farare ƙal!.”
“To shikenan kada ki damu, insha Allah za'a ajiye miki har ma guzuri sai kinyi da wasu, ki zo da babbar jakar da zaki zuba a ciki.”
“Allah koh, gaskiya kana da abin dariya sosai.”
Hira me ɗan tsayi suka yi babu laifi daga karshe suka yi sallama. Zuciyar Nurse cike da nishadi da jin dadi, a karon farko ta fara tura masa wasu saƙonni na musamman, fatanta dai Allah yasa ya karɓi tayinta kada ya watsa mata kasa a ido. Domin wasu mazan miskilai ne, idan suka ga mata sun karya bullensu sun nuna suna sonsu sai su fara ja musu rai da wulakanci.
Hakan yasa 'yan mata basu cika nuna suna son maza ba, saboda gudun wulakanci. Wannan shine tunanin da wasu 'yan matan keyi ciki har da ita Nurse, to amma tana ganin kamar Mustapha baya daga cikin irin waɗancan mazajen. Hakan ne ma ya bata ƙwarin gwiwar saka soyayyarsa a zuciyarta.
Nurse ta faɗa kogin soyayya💝😂😜, to Allah yasa a dace.
*_YAU TAKE SALLAH_*
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."