Pɑge 45 & 46

23 1 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 45 & 46*

Misalin karfe 4:15pm, bayan idar da sallar la'asar keda wuya, Habib ya dauko Malam Ibrahim da kuma wani ƙanen hajiyar ana kiransa Alhaji Musa suka iso gidan su Hassanar.

Waya Habib ya yi, ya sanar da ita cewa sun iso fa, suna kofar gida. Ita ma isar da saƙon tayi ga Baba, da yake yana gida. Da aka idar da sallar dawowa gida ya yi, ya duba ko baƙin sun iso, saboda haka takalmansa ya sa ya fito. Malam Ibrahim da Alhaji Musa ne suka fito daga motar, Habib bai fito ba.

Bayan sun gama gaisawa Baba yace, “To bisimillah!”

Ya shige gaba suna biye dashi a baya har zuwa masallacin unguwar, inda a can ne sauran mutanen ke zaman jiransu Malam Ibrahim din. Gaisawa aka fara yi sannan liman ya jagoranci addu'a.

Bayan an gama addu'a Baba ya dubi Alhaji Idi da liman yace, “Waɗannan sune magabatan yaron da yake neman auren Hassanah.”

Liman yace, “To Masha Allah, sannunku da zuwa.”

Nan dai aka yi dukkan abinda ake yi bisa al'ada aka gama. Aka bada kudin dukiyar aure, sannan aka saka rana watan Muharram, ya kama watanni bakwai kenan. Daga karshe Baba yake sanar da mutanen cewa, “Ai yaron Ɗa ne ga marigayi Alhaji Sa'eed Na Kowa.”

Gaba ɗayansu mamaki kama su ya yi, har da Alhaji Idi wanda tunda aka zauna bai ce uffan ba. Fuskarsa a ɗaure baya fara'a. Liman ya sake jagorantar rufe zaman da addu'a tare da fatan Allah ya tabbatar da lamarin, Allah ya bada yadda za'ayi. Aka yi musabaha aka watse kowa ya kama hanyarsa. Hassanah ta taka matakin farko na zama amarya ,saura kuma 'yan baya.

*_BAYAN SATI DAYA_*

Yau ranar lahadi ce, kuma ita ce dai-dai cikar sati biyu, wato ranar da Usainah take zuwa ganin gida. Tun sassafe ta tashi ta gama duk aikace-aikacenta, tayi wanka ta shirya tsaf! Tana jira a ɗan ƙara jimawa sannan ta taho.

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora