*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©by *😘Um Nass 🏇🏼*
SHIMFIƊA
ƘAUYEN KWALAM
RINGIM L.G.ADurqushe take akan gwuiwoyinta tana faman kuka da gunji, ayayin da yake tsaya akanta yana ta faman balbaleta da masifa, kai take girgizawa tana qara sautin kukanta, hakan ko kaɗan bai sa yaji tausayinta ya kuma tsagaita daga faɗan da yake mataba.
"In dai har abin da idanuwana suka gane min gaskiya ne, to na tabbata babu wani abu da yayi saura na yarda atsakani-na-da-ke, zan kuma nesanta kaina daga duk wani abun da zai sake haɗa fuskata da taki."
Hawaye ne ya ci gaba da zuba acikin idanuwanta, hannayenta biyu tana haɗesu waje guda, magana take sonyi amma ta gagareta fita akan laɓɓanta, so take ta samu damar kare kanta daga mugun zargin da mijin nata yake son mata, amma kamar ana qara kulle mata bakin nata ne, sai dai kallon da yake mata ƴa qara tsoratar da ita ta, hakan yasata aro dauriya da juriya ta fara magana "A'a Idris ko wani abu yakan buqaci bincike da samun tabbaci akansa, amma ba tare da ka nazarci komiba ka yanke hukunci hakan ko kaɗan bai kamacekaba sam-sam."
Hannu ya ɗaga yana jijiga jiki kamar wata mace "Ke ai ya kamaceki da kika kasa tsare kanki, na ɗauka qarya ne abun da su Tani suke faɗa ashe tsagwaran gaskiye ce Tsirararta ashimfiɗe acikin maganarsu, dan haka yau ɗin nan zan kawo qarshen matsalata ba sai anje ko inaba, na gode Allah da ya nuna min gaskiya."
Saurin qarasawa kusa da shi tayi tana qara yawaita hawayenta qafafuwansa ta riqe tana fatan ya bata dama ɗaya ya kuma kalleta da idanuwan basira, uzuri take son yayi mata akan tantance gaskiya akan kalamanta, numfashi take fitarwa akai-akai tana magana cikin dashewar murya "Ka dubi girman Allah Kada ka yanke min hukunci cikin fushi da ingizawar sheɗan ba tare da ka binciki komiba, kada idanuwanka su rufe daga ganin abun da baka da tabbaci akansa Idris, ina iyaka qoqarina wajan kare kaina daga duk wani mugun abun da zai kawo shamaki atsakanin yardar da take tsakanina da kai, dan Allah kada ka aikata abun da zaka zo kana dana sanin yinsa daga baya."
Haureta yayi da qafarsa hakan ya sata wuntsulawa baya ta buga kanta da wani dutse nan take kan ya fidda jini, zafi da raɗaɗin da take ji yasata dafe wajan cikin kaɗuwa da tashin hankali ta sake kai kallonta gareshi, fuskarsa babu ɓurɓushin rahma ya fara nunata da ɗan yatsansa manuniya "Na tsaneki Ruqayya na tsani komi da zai fito daga bakinki, dan haka baana buqatar wani qarin lokacin da zan baki wanda zai jefa zuciyata cikin wata damuwar, wanda nake cikinta ma ta isheni dan haka kafin na fito ki tattara komi da yake mallakinki kibar min gidana, na sakeki saki Uku."
Qirjinta ta dafe da qarfi take jin bugawar zuciyara tana barazanar fitowa daga qirjinnata, haka kuma ta fara bubbuga kunnuwanta da suka fara mata amsa kuwa da qara mai Amo, dafe kunnen tayi tana kai kallonta gareshi, kai ya gyaɗa mata yana qara tamke fuskarsa haɗe da bata tabbaci akan maganarsa, dai-dai lokacin wata yarinya ta fito daga ɗakin wanda ba zata wuce shekara Uku ba, hannunta acikin bakinta tana tsotsa ganinsa ya sata saurin qarasawa ta maqalqale rigarsa ta fara magana wanda bata fitowa "Babu alawa bitcik" hankaɗe yarinyar yayi ya turata kan Ruqayya cikin rashin sa'a kansu yayi gwara nan yarinyar ta fara tsandara ihun kuka, cikin mamaki da qarfin hali tace "Idris muguntarka ta wuce kaina harda erka da ka haifa da cikinka."
Tsawa ya kwatsa mata ya fara nunata da hannunsa "Akul ɗinki ki qara dangantata da ɗiyata, dan ni kokonto nake akan ba ɗiyata bace, dan ko kaɗan bata kama dani, dan haka ki kwasheta kije can ki nema mata ubanta ki kuma tabbatar kin bar min gidana kafin na dawo, munafukar Allah Annamimiya kawai." yana qarasa faɗar haka ya fice Fuu kamar Iska yabar gidan, da ido suka bishi wani dunqulelen abu ne ya tsaya mata amaqoshinta hawayen da take shirin yi suka ɗauke daga cikin idanuwanta.
Miqewa tayi ta shiga ɗaki bata jimaba ta fito da lilliɓi akanta sai kayanta a er qaramar jaka gana mazgo ta ɗauko ɗiyarta da take ta faman binta duk da cewar tana tafiya da girmanta hakan bai sata qin ɗaukantaba asalima goyata tayi da zani ta janyo ɗakin ta rufe, kana ta janyo qofar gidan, juyawa tayi ta masa kallo na qarshe sanann ta fara tafiya cikin sauri ganin idanuwan mutanen garin akanta da alama sun fahimci abin da yake faruwa da yawa suna tsaigumi akanta, qara sauri tayi tana hawaye akan fuskarta, ta shiga gidansu Da sallama abakinta.
Sai dai kafin ta kai ga zama taji an kwatsa mata tsawa "Kema dai kin san idanuwanki da kunya ki shigo min gida, dan haka ki fice ki bar min gida, bana buqatar balagurbi acikin zuri'ata."
A hautsune ta juyo ga kallonta ga wanda yake maganar Fuskarsa babu alamun rahma akanta cak hawayen da yake zuba akan fuskarta suka tsaya "Babuji" Fuska ya qara tamkewa ya mata nuni da qofa "Fuce ki bar min gidana" kallon gidan tayi ta kai kallonta ga Mahaifiyarta wanda kanta yake sunkuye ko da bata ɗago kaiba tasan ba zatayi maganaba, dama can haka take balle kuma yanzu amma yanayinta ya nuna tsantsar damuwa da alama hawaye yake zuba akan idonta.
"Innarmu kina ji babuji na korata, kema kina zargina baki yarda daniba, idan duk duniya zata juya min baya taqi yarda dani na ɗauka ku zaku rungumeni ku min uzuri ku yarda da gaskiyata." Muryarta akwai rauni acikinta hakan yasa Innarmu ɗago kanta itama idanuwanta cike da hawaye, murmushin yaqe ta mata wanda da gani yafi na kukan ciwo "Allah yana tare da ke Ruqayya na tabbata idan akwai wanda ya cuci wani atsakaninku sakayya zata fito, ki tafi ko inane amma ki bar masa gidansa, Addu'ata zata riskeki aduk inda kike." tana gama faɗar haka ta shige ɗakinta, kallonta ta kai ga Mahaifinta wanda ya qara gumtse fuska "Fita" ya mata nuni da qofa, juyawa tayi tana murmushi da hawaye wanda yafi kuka ciwo...🌹🌹🌹🌹
Gani dai na sake dawowa cikin Labarin ISMAHA ZAINAB duk da abaya nayi tsammanin kaiwa wasu shekaru kafin nayishi, amma kuma saiga labarin yayi karo dani ya kuma tadani akan nemo alqalami dan fiddashi asauqaqe, amma ban muku alqawarin ganin yawaitarsa ba ya danganta da ɗan lokacin da na samu kaɗan ko mai yawa, duka dai zamu kai ga inda ya kamata ace munje acikin tafiyar In sha Allah.#Um Nass
#MBW
#Vote nd cmnt
#Da amana
ESTÁS LEYENDO
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...