*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
😘Um Nass 🏇
Page 36
Ƙauyan Kwalam
Tunda motar su ta shiga cikin garin bugun zuciyar Luyya ya ƙaru, bin ko ina na garin take da kallo, babu wani abu da ya sauya agarin, yana nan dai ayanda ta fice ta barshi, idanma akwai sauyi to bai wuce na manyata da dattijan garin suka ƙara yiba, sai kuma yaran da ta tafi tabarsu duk sun dawo samari.
Komin daɗewar shekarun da aka ɗauka bazata taɓa manta gidansu ba, da kwatance ta nuna musu gidan, har suka kawo ƙofar gidan, yara na biye dasu suna ilo.
Jin hayaniya aƙofar gidan su yasa Babuji fitowa yana daddogara sanda, tsufa ya ƙara kamashi wanda sai da taimakon Sandar yake iya tafiya.
Ganin mota sabuwa aƙofar gidansa da kuma baƙin mutanen da suke fitowa acikinta yasashi yin mamaki.
"Bayin Allah ba nan bane gidan mai garin ai, sai kun ɗanyi gaba. Kai Kallamu mi yasa baka kaisu gidan Mai garinba?"
Ya ƙarasa maganar yana nuna wani yaro wanda bazai haura shekara goma ba "Su suka zo nan da kansu, basu tambayemu ba."
Hawaye ne yake zuba akan Idon Luyya, da gaske mahaifinta takega agabanta. Babuji ɗin daya haramta mata shiga gidansa tsawon shekaru goma, sautin muryarsa ce ta dawo mata kunne kamar alokacin yake bata umarni _"Kema kinsan idonki da kunya ki shigo min gida, bana buƙatar balagurbi acikin Zuri'ata. *Fita*."_ maganar da Babuji ya mata awancan lokajin ta sake dawo mata akanta.
Kai ta fara girgizawa tana ƙoƙarin komawa cikin motar, hannunta taji an riƙe wanda yasata tsayawa gami da juyowa, Alh. Isah tagani yana riƙe da hannun nata yana girgiza mata kai fuskarsa ƙunshe da murmushin ƙarfafa mata gwuiwa "Wanan shine mahaifinki Ruƙayya, ki kalla da kyau, yana buƙatar tallafawa adai-dai wanan lokacin. Shekaru sha biyar rabanki da ganinsa, ina tare dake aduk wani motsin da zakiyi."
"Abu Usama..!"
"Muje."
Abun daya faɗa yana datse ko wata magana da take son fitowa daga bakinta, yajata har gaban Babuji ɗin, da yake ta faman binsu da kallo.
"Baba wajanku muka zo. Mu baƙine daga Haɗejia."
"Haɗejia! Ikon Allah ku ƙaraso daga ciki, lallai maraba, kunsha hanya, maraba."
Ya faɗa yana shiga cikin gidan da musu nuni da hanya alamun su biyo bayansa.
Binsa sukayi abaya har suka ƙaraso tsakar gidan, anan ya fara ƙwala kira "Ballu! Ballu!! Fito da abin shimfiɗa munyi baƙi ne ashe."
Fitowa tayi hannunta ɗauke da bujukura (Tabarma mai faɗi) ta shimfiɗa musu tana kiran "Lale maraba da baƙi, ku zauna."
Zama sukayi akan taburmar ita kuma ta shige ɗaki ta ɗebo ruwa mai sanyi a kafarar da take ɗakin, cikin kwanan sha mai kyau ta kawo musu.
Ɗauka Alh. Isah yayi ya sha sanan Usama ya sha, Luyya kam sai kallon iyayen nata take amma ta kasa ko motsi, gefe ɗaya kuma Ismaha Zainab ce take riƙe da hannu Hassan da Hussain sai wurga ido take tana aika kallonta tsakanin tsofaffi biyun, wanda ta kasa ban-bance alaƙar da take tsakaninta da su.
Bayan gaisuwar da sukayi Babuji yayi gyaran murya ya fara magana "Asanina dai bani da ƴan uwa ko guda acikin garin Haɗejia, amma kuma lamari da iko na Allah sai gashi ance nayi baƙi daga garin." ya faɗa yana murmushi wanda yake nuna dattakon sa da kuma Girmama baƙin nasa."Haka ne kam." Alh. Isah ya faɗa yana murmushi, sanan ya nuna Luyya da hannun sa "Amma wanan baku shedata ba itama?"
Sai alokacin suka ƙura mata ido, suka kafeta da shi, can kuma kamar an zaburi Ballu ta miƙe tsaye ta ƙaraso kusa da ita "Ruƙayya!""Ruƙayya kuma?" babuji ya faɗa yana ƙoƙarin tashi daga inda yake yana matsowa wajansu.
Kai Ballu ta gyaɗa sai kuma ta shafa fuskarta "Eh Ruƙayya fa! Wanan Ruƙayya ɗina ce Malam, ni dama nasan Ruƙayya tana raye malam, zo kaga wallahi wanan Ruƙayyarmu ce, duk sauyawar da zatayi bazan kasa ganeta ba." sai kuma ta fashe da kuka tana rungumeta.
Itama kukan tasa tana ƙara maƙale Ballu "Innarmu!" ta faɗa cikin Muryar kuka.
Sun ɗauki lokaci ahaka kafin su saki juna, kowa awajan cike yake da tausayin su, Babuji ma kasa haƙura yayi saida ya matsa yana shafa kan Luyya yana faman kiran "Ikon Allah, ikon gaske, ashe da rabon ina da sauran kwanan da zan ƙara sakaki acikin idona Ruƙayya." yana maganar yana share hawayen da yake zuba akan idonsa.

YOU ARE READING
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...