*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB💍*
©BY *😘Um Nass 😘*
_FOLLOW ME ON WATTPAD. @UmNass_
® *NAGARTA WRI.ASSOCIATION*
BABI NA HUƊU (page 4)
Kamar mai jin tsoron ta haka ta ƙara takurewa a waje ɗaya tana kallon yanda take sauƙe numfashinta a hankali, ta ɗauki tsawon lokaci bata samu ƙwarin gwuiwar rarrafawa dan ta tinkari Ismaha Zainab ba, domin gani take kamar ba ita ba, ido ta lumshe cikin fatan ace mafarki tayi ba a zahiri ba "LUYYAH Abinci anci." Ta tsinkayi muryar Ismaha Zainab adai-dai lokacin da take faɗawa jikinta, firgici gami da tsoro yasa ta buɗe idonta Tarr a kanta, ita ɗince jikinta tsaf babu alamun ƙasa ko ƙura kamar a lokacin ta mata wanka, kanta ta bibbiga sannan ta sake kallon inda ta faɗi ta kwanta amma babu ita babu alamun ta, kafin tayi wani yunƙuri ta tsinkayi muryar ɗan Almajirin da yake kai kawo tsakanin masu siyan Abincin ta "Innar Ismah gashi ki zuba ma Muntari yace har da na jiya zai fanshe, ga jaka guda na duka zaki zuba masa taliya da ɗan-wake."
Kallon ta ta kai ga tarwatsattsiyar fantekar da Innar su kamalu tayi jifa da ita amma cikin mamaki da al'ajabi taga babu ita a wajen, asali ma wajan a share yake fess kamar ba'a taka shiba, waige ta farayi nan taga Fantekar a mazaunin da ta saba ajiye ta idan zata siyar da abincin, zuciyarta ce ta tsinke da tsoro mai tsanani, nan tayi saurin ture Ismaha Zainab daga jikinta amma kuma hannayenta suka kasa yin hakan, da sauri ta sauƙe kallonta a kan fuskarta, itama kallonta take ido cikin ido wani abune a cikin ƙwayar idon nata mai kalar blue da taruwar ruwa mai sirkin maiƙo a cikin idon, nan take jikin Ruƙayyan yayi sanyi laƙwass kwata-kwata tunaninta ya ɗauke tama manta da abin daya faru a tsakanin lokacin, sai sake tsinkayar muryar ɗan Almajirin tayi "Innar Isma jirana yake yace da sauri fa."Saurin zuwa tayi gabansa ta karɓi kuɗin "Oh Garba kai dai kace baka son Uban gidan ka ya daɗe a waje" ta faɗa tana murmushi, shi ma dariya yayi yana ƙara mata bayani ya ce' "jiya ai yasha wuya da ya makara a tashi, asali ma haka ya yini sai da dare yasha shayi da burodi a wajan Na Inna, duk da haka bai ji yanda yake soba, dole yau ya gimtse barcin sa ya taho da wuri saboda kar a sake mai-mai."
Dariya take sosai sannan ta miƙa masa abincin cikin kwanon roba da gani ya haura na adadin kuɗin daya buƙata "gashi kace yayi ƙoƙari ya cinye duka idan ma bai ƙoshi ba ya aiko a ƙara masa wani, har sai yaji ya cike ramin da ya haƙa."
Ido Garba ya ƙwalalo waje cikin mamaki kafin yayi dariya "aradu koshi raƙumi ne yaci wanan Abincin ya ƙosa har dare bai biɗar wani abun ba." Murmushi tayi bata ce masa komi ba har ya fuce, sai a lokacin Ismaha Zainab ta ƙaraso kusa da ita tana faman turo baki "Luyyah nima anci abinshin." juyawa tayi tana kallon ta cikin kulawa da murmushi a kan fuskarta ta janyo ta haɗe da ɗora ta a kan cinyarta kana ta zubo mata taliya dan tafi sonta, da hannunta ta fara bata tana ci tana murmushi, abin yana ɗaure mata kai ganin yanda Ismaha Zainab ta buɗe ciki tana cin abincin sosai, wanda ta zuba mata ta cinye tass kana tace a ƙaro mata ɗan-wake zata ci, shima wanda ta zuba mata sai da ta cinye shi, gashi kuma bata buƙaci ruwa ba, saɓanin a baya duk lokacin data ke cin abinci tana korawa da ruwa asali ma shan ruwan yafi cin abincin ta yawa, amma kuma yau an samu ban-banci da tazara ta yanda bata buƙaci ruwa ba har cin nata yayi nisa, magana take so ta mata ko gardamar zuba mata abincin amma kuma kamar an ɗaure bakin asali ma samun kanta tayi da jin daɗin ganin yanda take cin abincin hankalinta kwance.Tana gama ci ta sauƙa a kan cinyarta ta nufi ƙofar fita, kasa mata magana tayi har ta fice, sai a lokacin tunaninta ya dawo a kan mi yasa bata tsaida ita ba, sam Ismaha bata ƙaunar fita waje balle yin wasa da yara amma kuma sai gashi yau da kanta ta fice har tana gudu cikin kazarniya da kuzari, tagumi ta rafka a wajan tana son tuno wani abu amma kuma ta gagara tuna ko miye ne, a haka Garba yazo yana kai kawon mata ciniki kafin wani lokaci abincin nata ya ƙare tass, shima ta zuba masa nasa ya ci, har wannan lokacin babu Ismaha Zainab babu alamar ta. Dole ta tashi Garba akan yaje ya nemo mata ita.
******
Da gudu suka gifta mutane wajen suna ihu da kuka kamar sa tada garin amma babu wanda ya kula da su, asali ma babu wanda ya ankare da wanzuwar su a wajen, haka suka ƙarasa gidan nasu nan suka warwatsu yashe a ƙofar ɗakin Innar su kamalu, wanda garin gudu tayi hantsilawa yayi biyar a waje, ko ina a jikinta ciwo yake mata, hawaye shaɓe-shaɓe a kan fuskarta "Kin cuce ni Tani, ina zaman zama na kika angiza ni nazo mu tafi Ruƙayya taƙi jin magana ta, ashe rabon na janyowa kaina wahala da azaba ne." hawaye ne ya ci gaba da tsere a kan fuskarta wanda tayi futu-futu da ƙasa, da ƙyar ta ƙara jan ƙafafuwanta ta kai jikin bango ta jingina tana maida numfashi.
"Uhmm Innar kamalu nima banyi tsammanin zamu tadda wannan azabar ba wallahi, duka ta ko ina jikina duk shatin bulala, anya wanan yarinyar ba Aljanah bace, dan Aradu idona baya tantance ko kamannin ta sai sauƙar duka da naji."
Hanci Kululu taja ta face majina cikin tsoro da fargaba ta fara magana "Kinga Tani ki raba mu da batu a kan wannan, mu muka kai kanmu da bamu jeba da ba abin da zai same mu, Allah yasa bakin wahalar mu kenan, nan gaba sai musan shirin da zamu yi."
Shuru Innar su Kamalu tayi bata tanka musu ba, a ranta tana kissima martanin da zata ɗauka a kan Ruƙayya da ɗiyar ta "Tabbas yarinyar nan tafi kama da ƴan ruwa, ni tun farko bana jinta a jikina, ashe ba jinina bace." Innar su kamalu ta faɗa tana sharce gumi a kan fuskarta. Nan aka shiga kallon-kallo tsakanin Tani da Kululu suna masu jinjina maganar Innar su kamalu a kan gaskiya tsagwaranta.*******
Tafiya yake yana ta faman ƙwala mata kira Ismah Abu kina ina ne, sai da ya shiga gidajen da suke maƙotaka da su, amma babu ita babu dalilin ta, gajiya yayi ya dawo gida ya sanar da ita "Innar Ismah bata gidajan dake kusa fa, na duba babu ita." ido ta fiddo waje cikin tashin hankali ta sai ta kallonta gare shi, "Na shiga uku ni Ruƙayya, Ina zatje a wannan garin.?"
Kafin tayi shuru ta tsinkayi maganar Ismaha Zainab ita kaɗai take tafiya tana magana "Ai munyi faɗa da kai, kalka ƙala min magana." tana gama faɗar haka ta wuce su ta shige ɗaki tana kumbure-kumbure ba tare data kulasu ba, baki buɗe suka bita da kallo daga Ruƙayyan har Garba Almajiri.....🥀🥀🥀🥀🥀🥀
_To fa gamu dai cikin tafiyar taki kaɗan ya rage labarin Ismaha Zainab ya sauya sallo, ku daure ku ɗauƙo ko wata mutuntaka taku da nagartar da take a tare daku sai ku magantu dan ra'ayin kanku. Ina miƙa tarin gaisuwata ga ɗaukacin masoya na masu bibiyar labari na a duk inda kuke ina muku Ƙaunar Ƙauna Fisabilillah_
#Um Nass
#plx Cmnts, vote, share
#NWA
#DA AMANA
BẠN ĐANG ĐỌC
ISMUHA ZAINAB Completed
Phiêu lưuAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...