BABI NA BIYU

687 41 0
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

©by *😘Um Nass 🏇🏼*

®NAGARTA WRI..ASSOCIATION

BABI NA BIYU (Page 2)

Da saurin ta ta ƙarasa fitowa, tana jin sautin kukan ta har ranta, ta ɗauki tsawon lokaci  a ƙofar gidan, sanan taja ƙafafuwanta ta bar gidan, kai tsaye gidan su ta nufa a inda ta tadda mahaifiyar ta a zaune tana tankaɗe gari, gefe ɗaya kuma mahaifin su ne yana duba wasu litattafan sa. Ɗagowa sukayi suna kallon ta cikin mamaki dan bata saba zuwa a irin wannan lokacin ba, tafi zuwa da yamma ko dare wani lokutan ma idan mijinta yana gari bata fiya zuwa ba.
"Lafiya Ruƙayya? Ina kika baro Isim ɗin?". Mahaifiyar ta ta tambaya tana dakatawa daga tankaɗen da take yi, murmushin yaƙe ta yi sannan ta tsugunna ta fara gaida su "Ina kwana Babuji? Innarmu ya kuka tashi?".
"Alhmdulillah lafiya lau muke". Babuji  ya amsa yana kallon fuskarta.
"Ina kika baro min matar ta wa?", ya tambaye ta yana ɗan murmushi itama murmushin tayi kafin ta fara magana' "tana wajan Innar su Kamalu".
"Amma na ga bata saba da suba, asali ma ƙiwa take musu, mi yasa kika bar ta salon kisa wani cutar ya kamata?". Innar mu ta faɗa cikin faɗa-faɗa, kai ta girgiza cikin murmushin yaƙe mai kama da kuka "so nake ta saba da su Innar mu, ƙiwar da take musu ta yi yawa gashi suna son ta suma, shi yasa na fara kai ta can ɗin dan ko ina akaje aka dawo sune dolen ta."
Kai ta girgiza cikin takaici "eh duk da su ne dolen ta Amma ai tayi ƙanƙanta a bar ta a wajan su, duka ma nawa yarinyar take da har yanzu bata kai shekaru biyar ba, wannan zalinci ne daga ke har Innar su Kamalun da ta biye miki ta karɓi yarinyar duk da kukan da zata yi mata, ita ai bata da asara da damuwa idan wani abun ya same ta, amma kuma ke ce da asara idan maƙo yayi sanadiyar mutuwar ɗiyar ki." Daga haka ta cigaba da tankaɗen ta ba tare data ƙara tanka mata ba.
Jin maganar Innarmu ba kaɗan ba ya tsorata hakan ya sata ɗaukewar numfashi na wasu lokutan, babu yanda za tayi yanzu kam ta riga tayi sake, tana kuma addu'a a kan Allah ya kare mata ɗiyar ta a duk inda take. Can ta juya kallon ta ga Babuji "Babuji shin akwai aibu a cikin sana'a ta ne da mutane suke ta sauya maganganun su a kaina?", ɗagowa yayi daga duba littafin da yake yana kallon ta. "Ban Fahimci maganar ki ba Ruƙayya, wani abu mutane suke faɗa a kan ki?".
Kai ta sunkuyar ƙasa tuni hawayen da ke idonta ya zubo "Innar su Kamalu ke magana akan sana'ar ta wa wai ina cika gida da maza, dole na zaɓa ko aure na ko kuma sana'a ta."
"Mi yasa zata sanya miki doka? Bayan kuma da sanin mijin ki kike wannan sana'ar, idan ta hana ki neman kuɗi zata ɗauki nauyin ki ne? Ko kuwa shi ɗan na ta ne zai ɗauke miki ko wani nauyi na ki? Bayan shi ba mazauni bane a gari balle ya fuskanci wata matsala taki ya iya magance miki ita." Innar mu ce take magana cikin ɓacin rai da takaicin maganar su Innar Kamalun, hannu Babuji ya ɗaga mata "A'a Ballu suna da gaskiyar su suma, duka nawa Ruƙayyan take da zata na sana'a irin ta tsoffin mata, kina ga yanda kullum gidan ta yake a cike da maza ana layi, nima dai na goyi bayan su a kan ta nemi wata sana'ar tayi amma banda wannan."
Baki buɗe suke kallon Babuji kafin nan Innar mu ta cafe maganar' "Tafɗijam kai ma kasan wannan abu ne ba mai iyuwa ba, Allah ya rufa mata asiri wajan sana'ar ta tana samun alheri sannan kuma kace ta sake wata, faɗa min mi zata siyar a wannan garin wanda zai maye mata gurbin sana'ar ta? In dai ba baƙin ciki irin na mutum ba kowa a garin nan yasan maza a ƙofar gidan ta suke tsayawa, iyaka su tura yara da kuɗi a karɓo musu abincin", miƙewa tayi tsaye tana kallon Ruƙayya "Duk wanda zai ƙara miki suka a kan sana'ar ki to kice ya ɗauki nauyin ko wata buƙata taki, a ciki har da mijin ki Idirisun, idan taƙamar su saki ko wani abu ba a kan ki a ka fara zawarci ba, zaki samu maza dubu suna jiran ki."
"Dakata-dakata Ballu wani irin magana ne haka, kina so ki zama tsani guda na wargajewar zaman lafiya a gidan ƴar ki, yanzu idan kika ɗora ta a kan wannan mummunar aƙidar kina tunanin akwai mai aurar ta ne, shi zawarcin daɗi ne da shi aka faɗa miki? To ki jini da kyau muddum ta kaso auren ta sai dai tasan inda zata zauna amma ba a gidana ba". Yana gama faɗar haka ya tashi ya fice abinsa yana faɗa kamar zai aro baki. Da ido suka bishi a yayin da Ruƙayya ta ɓalle da sabon kuka, lallashin ta Innar mu take tana bata haƙuri a kan kada ta ɗauki maganar Babuji da gaske barazana ce kawai yake yi, taci gaba da sana'ar ta tunda Allah ya dafa mata, daga haka tayi sallama ta tafi a kan kada a kai Ismaha Zainab bata nan.

ISMUHA ZAINAB CompletedDonde viven las historias. Descúbrelo ahora