*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©by *😘Um Nass 🏇*
_√Ote me on Wattpad @UmNass_
Babi na 35
A gajiye liƙis ya ƙarasa gida, kai tsaye ɓangaran sa ya shiga, ya sake watsama jikin sa ruwa, saboda zafin da yake ji.
Ga kuma tarin tausayin Ismaha Zainab da ya gama cika ko wani sashi da lungu na zuciyar sa, ashe da akwai babban dalilin da yasa taƙi amincewa da tayin soyayyar sa, ashe duka tsawon lokacin da yake tunanin ta aƙasan ransa tana fama da wata matsala mai yawan gaske.
Har ya fito abanɗakin zuciyar sa na cunkushe da tarin tunani, wani sashi kuma na zuciyar sa na godema Umman sa wajan jajircewar da tayi har ya tafi wata duniya karatu, wata ƙila da har yanzu ana kame-kamen wanda zaiyi Ruƙiyya wa Ismuha Zainab ɗin sa, da kuma wani ƙato ne zai gane masa ko wata sura ta jikinta.Jallabiya ya zura ajikinsa, bayan ya shafa mai ya kuma bi ko ina na jikin sa da turaruka masu ƙamshi. Ɓangaran iyayen sa ya nufa, yasan har sun gaji da baza idon ganin sa, daga zuwan sa yau ya fita, fitar da zai iya kiranta da sa'a ko kuma rashinta.
Da sallama akan laɓɓansa ya shiga palon gidan, cikin haɗuwar baki suka amsa masa, sanan suka zuba idanuwan su gareshi.
"Ashe ka jima da dawowa ma? Mu muna nan muna jiran dawowarka da muka ji shuru, gashi baka ɗora layinka akan waya ba balle mu kira da shi." Abban sa ya faɗa yana faɗaɗa murmushi wanda da gani najin daɗin ganin sa ne.
"Eh! Ban jima da dawoba Abba, wanka kawai nayi."
"Masha Allah, barka da baka ɓata ahanya ba ai."
Ido ya waro waje kafin yayi murmushi mai sauti "Ɓata kuma Abba? Ai ko Jidda bana jin zata ɓata agarin nan balle ni."Dariya Umma sukayi ita da Jidda kafin ta sako musu baki cikin hirar "Ai Jidda sai taje ta dawo kai baka dawo ba, saboda shekarun da aka ɗauka baka nan, saɓanin ita da ta rayu agarin ta kuma tashi acikin sa."
Kai ya gyaɗa cikin yarda da maganar "Duk da haka nima sai da nayi shekaru kamar nata agarin kafin na fice acikin sa."
"Amma ai akwai sauyi da yawa da aka samu wanda babu kai acikin sa."
"Kaɗan ba." ya faɗa yana ƙoƙarin tashi daga kusa da ita, ya koma kusa da Abban su.
"Koma yaya ne an samu ai, shine harda tashi."
"Umma fa! Maganar ki ne akan ɗiyar ki fa, bakya so ace tayi ƙasa."
Dariya sosai suka saka masa ganin yanda yake maganar yana kwaɓe fuska, hadda jiddan da take zaune awajan itama saida ta dara "Ƙyale su yarona, da baka nan bakaji yanda suka cika ni da kukan rashinka da sukayi ba, amma kaga yanzu suna taɓa ka, dama bakin su yayi tsami suna son su fanshe tsamin da yayi ashekarun da baka nan."
"Aifa naga alamar hakan Abba." ya faɗa yana zama kusa da shi."Bani labarin inda kaje, Ka dace dai inji?" Abba ya tambayeshi yana wara hannun sa alamun tambaya.
Murmushi yayi sosai, sanan ya fara murza goshinsa "Ina jin Yunwa, Jidda kawo min abinci naci."
Da sauri ta tashi ta shige kitchen, sai alokacin ya kalli Abba da ya kafe shi da ido, murmushi yayi yaci gaba da murza goshin sa "Bazan iya cewa na dace ba Abba, amma dai na taki sa'a da ban wuce yau ba.""Kamar wata irin sa'a kenan?"
"Umm! Kamar yanayin gari da kuma wuraren da suka sauya, sosaifa." ya ƙarasa maganar yana murmushi, shima Abba dariya yayi mai sauti, gane yandA maganar ɗan sa ta dosa.
"To shikenan Allah ya taimaka, idan lokaci yayi dai ya zama nine na farkon zagaya garin."
"Abba mana!" ya faɗa yana ƙara murza goshin sa. Da alamu hakan ya zama ɗabi'a da halayyar sa."Hirar mi ake aka ware ni? Sai sautin dariyarku kawai ake ji."
"Hirar ce tsakanin Aboki da abokin sa, babu ke aciki." Abba ya faɗa yana murmushi.
Dai-dai lokacin da Jidda ta ajiye farantin abinci agaban Musaddiƙ.
Baki ta taɓe "Ai shikenan, danma dai ina da tawa ƙawar balle nayi takaici."
Buɗe filas ɗin abincin yayi tuwon shinkafa ne sai miyar bushasshiyar yakuwa, da ta sha kifi sai man shannun da yake ta buɗaɗa ƙamshi, ga kuma farfesun kayan ciki, gefe ɗaya kuma lemon kwakwa ne da abarba acikin jog "Masha Allah, wanan gara haka Ummanmu, yau akwai shagali kenan." yana murmushi yake maganar ya sauƙo aƙasa yana tanƙwashe ƙafafuwan sa.
Dariya suka masa sanin yanda yake mutuƙar son tuwon shinkafa da miyar kuɓewa bushasshiya, idan ya same su baya barin su.
"Bari na tayaka Yaya nah." Jidda ta faɗa tana gyara zamanta itama, kai ya gyaɗa mata kawai.
Haka suka ci gaba da hirarsu cikin soyayya da kulawa, suna cin abincin anayi ana barkwanci cike da nishaɗi.
VOCÊ ESTÁ LENDO
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...