BABI NA 25

756 67 3
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

©BY *😘Um Nass 🏇*

® *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

BABI NA ASHIRIN BIYAR (Page 25)

Kallon bulalin taci gaba da yi, sanan ta kai kallon ta ga Sa'adatu wanda take ƙara sautin kukan ta. Allah ne kaɗai yasan irin azabar da za'a musu yau, ayanda ta kalli tuleliya Jummai na ɗaga bulalin fuskar ta babu ɓur-ɓushin rahma, tasan dole t dakesu sosai.

Kai ta girgiza cikin tausayin Sa'adatu da sauran ƴan aji biyar ɗin, ta fara magana "Allah kalku bali ta dakeku. Kun tsaya kuna ta kuka tun kafin tazo kusa da ku."
Ɗagowa sukayi suna kallonta cikin jin haushin ta Sa'adatu ta buga mata tsawa "Ki wuce ki tafi ɗaki kafin ranki ya ɓaci! Haba yarinya sai azababban surutu, ina ruwank i da kukan mu." ta faɗa cikin ƙarfin hali tana aika mata da harara.
Tashi tayi kamar zata tafi sai ta koma kusa da wasu ta zauna, ta rafka tagumi hannu bibbiyu.

Cikin isa da ƙasaita Jummai ta ƙaraso ta fara kiran sunayen wanda suka kai mata ruwa, su talatin tace su ware gefe, sanan ta juyar da kallon ta ga tarin ɗaliban da basu kai mata ruwan ba, murmushi tayi wanda da ganinsa na muguntar da ta tanadar musu ne "Wato ku tabbatu shahararu ko? Har wuyanku yayi kauri da girman da zanyi nema akai min ruwa amma kuƙi kaimin ko?"

Saurin girgiza kai sukayi cikin haɗuwar baki suka fara magana "A'a Anty Jummai dan Allah kiyi haƙuri."
"Kumin shuru banzaye, ƙazamai, kucakai, an faɗa muku ina buƙatar haƙurin da zaku bani ne? Ku kalleku wasu gajoji daƙiƙai daku. Maza ku hau layi." ta faɗa tana ɗaukan ɗaya daga cikin bulalin bishiyar da aka zubar mata agaban ta, tuni jikin su ya ƙara ɗaukan rawa, masu raunin xuciya kuma sun fara kuka acikinsu.

"Jiranku nake, kada ku ɓata min lokaci." nan suka shiga ture-ture wasu na baya wasu na gaba, ganin hakan yasa Ismaha Zainab miƙewa ta nufi gaban ta. Kallon ta Siniyo Jimmai tayi cikin mamakin abin da ya kawota wajan awanan lokacin, duk da gabanta ya faɗi, sanin cewar ita ba mutum bace kusan zata kirata da Aljanah ifirituwa, Amma hakan baisa ta nuna ba asalima fuska ta tsuke, cikin shan kunu da dakiya ta fara magana "Ke kuma Uban mi kike anan wajan? Ba nace kowa ya tafi ɗakinsu ba?"

Kallon ta Ismaha Zainab tayi sama da ƙasa kafin ta riƙe haɓarta, kamar mai tunani "Naga ke ɗaya ce zaki dakesu duk da suna da yawa." Kai ta gyaɗa tana aika mata da harara murya ta rage sanan ta ɗan yafito ta da hannu "Bakya tsolon hannun ki yayi miki ciwo?"

Takaici ne ya kama siniyo Jummai, dan da fari ta ɗauka wani abun arziƙin zata faɗa mata, harda rage murya "Abin da yafi gajiya zanyi, shegiyar yarinya mai siffar aljannu, idan baki matsa ba ta kanki zan fara dukan." ta faɗa cikin kurari ba dan zata daketan ba, dan har yanzu bata manta wuyar data shaba wajan dukanta.

Baki Ismaha Zainab ta ɓata cike da jin haushin zagin da Siniyo Jummai ta mata, ta juya ta fara tafiya, kallonta takai ga Sa'adatu wanda ta haɗa kai da gwuiwa tana rafka kuka ita haushintama takeji, tafi kowa ragonta da saurin kuka.

Ji tayi ta ƙara musu tsawa, saida taga akwai tazara mai yawa tsakaninsu sanan ta kirata "Ke Tuleliya mai Mulyal ƴan kashi kinga." da sauri Siniyo Jummai ta kai kallonta gareta, gani tayi ta haɗa hannunta ta ɗora asaman kanta alamun ƙaho sanan taja kunnenta ta buɗe hancin ta, sanan ta ɓaye baki tayi wani ihu "Jaki-Jaki ai dai a Aji ance ke kike zuwa ta lamba ta kashi. Kuma mugu azzaluma ce kika ce ina kama da Aljannu, ai dai bani ba, tunda bana shan jinin mutane."  tana gama faɗar haka ta fara tsalle gami da juya ido, dariya sosai ƴan Aji biyar suka kwashe da ita, sauran masu kukanma suke neme shi suka rasa sai dariyar da suke.

Ina rami na Afka, haka siniyo Jummai taji, kunya da tsananin ɓacin rai suka dirar mata alokaci ɗaya, yarinyar nan ta rainata sosai, shaƙiyancin ta ya wuce na sauran ɗalibai sabin zuwa, sai rashin kunya.

ISMUHA ZAINAB CompletedOnde histórias criam vida. Descubra agora