GARAƁASA

218 5 0
                                    

[6/23, 12:58 PM] Oum-Nass: INUWAR GAJIMARE⛅
 
Nagarta Writer's Association

  Oum-Nass 🏇

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI

   ƊAYA

Gudu yake iya ƙarfin sa, idanuwan sa na fidda ambaliyar ruwa, bai damu da ƙayoyin da yake takawa a ƙafafuwan sa ba, balle mutanen da suke binsa da kallo, suna masa kallon mahaukaci sabon kamu.

   Sai da ya kusa fita a cikin garin kana ya hango wani kangon ginin da  ya ke kewaye da ciyayi a cikin sa. Kutsa kai ya yi, yana zagawa, yana wara idanuwansa, da har zuwa lokacin basu daina zubar da hawaye ba.

  Can ya hango wata yarinya da ba zata wuce shekara goma sha uku ba, kwance ko motsi bata yi, ƙarasawa wajanta ya yi da mugun sauri yana girgizata da dukkanin ƙarfinsa.

   Amma ko gezau bata yi ba, ƙara ya saki mai ƙarfi, wanda amonsa ya cika kangon da ya ke "KHADIJATU!" Ya faɗa yana ƙara girgizata cikin tashin hankali.

    Ɗagata ya yi da niyar ɗaukanta, nan yaji damshi ya mamaye hannunsa, saurin janye hannunsa ya yi, yana mai fuskantar hannun nasa "JINI!" Ya faɗa, yana ƙara wara idanuwansa a fili wanda suka cika da hawaye.

  Ƙirjinsa ne ya ci gaba da bugawa da tsananin ƙarfi, saitin zuciyarsa na fat-fat kamar zata yi tsalle ta fito.
   A hankali ya sulale a wajen ya zauna, yana riƙe da zuciyarsa da yake ji tana barazanar fasa ƙirjinsa ta fito. Cike da tsoro yake ƙara kallon yarinyar.

    _'Mutum baya tara sani akan gaibu da kuma hasashen rayuwar da zata gifto masa anan gaba. Amma ni ina da yaƙini akanka ISHAQ! Ko da ace duniya da mutane cikinta za su sauya, ina da tabbacin kai ba zaka sauya ba._
  _A tare da kai Uba nake gani jigo kuma INUWAR GAJIMAREN da ke samar da iska ko bai bada ruwa ba. Bana so KHADIJATU ta tashi a matsayin marainiya! Bana son jin sautin kukanta! Bana son damuwarta! Ka min alƙawalin zaka kula da ita fiye da rayuwarka!"'_

   Kansa ya dafe da yake ji kamar zai ɓalle daga maɗaukarsa, magan-ganun mahaifiyarsu na masa amsa kuwwa a ciki kunnuwansa, kamar a yanzu ne ta ke faɗa masa.
  Kamar wanda aka fizga haka ya sake tashi ya ɗagata, ba tare da lura da yanda jinin ke zuba yana ɓata shi ba, hawayen fuskarsa na ƙara ambaliyar  sauƙa a kan fuskarsa.

   "Kada ki tafi ki barni Khadijatu! Na yima Ummi Alƙawarin zan kula da ke fiye da rayuwata, zanyi dariya a lokacin da kike taki dariyar, zan shimfiɗa rayuwata na baki kariya da dukka nin ƙarfina!
  Amma me yasa kika tafi ke ɗaya baki jira ni? Me yasa baki tsaya ni ba? Bayan nace ki jira bazan daɗe ba?"

  Shi kaɗai yake sambatu, yana gudu da ita a jikinsa, ƙayoyi duk sun huda masa ƙafafuwansa.

  Kai tsaye asibitin ƙauyen nasu ya nufa "Likita! Likita!!" Yake faɗa cikin ruɗewa da neman agajin likitan. Wanda muryarsa ta riga data dusashe.
 
   A hanzarce likitocin suka nufeshi, ganin yana ɗauke da yarinya ba numfashi, ga kuma jini duk ya ɓata su , suka ɗorata akan gadon marasa lafiya.
   "Me ya faru da ita?" Likitan ya watsa masa tambaya.

   Kai ya girgiza yana riƙe da ƙirjinsa da har lokacin bai daina zafi da bugawa ba.
  "Ban sani ba likita! Nima a haka na sameta cikin jini. Dan Allah karka bari ta mutu likita, ka ceto rayuwar 'yar uwata."

   Kai likitan ya girgiza cikin tausaya masa, ya shige ɗakin da aka kaita. Tashin hankali ne sosai ya ziyarce shi, kafin ya shiga sharce gumi akai-akai, "Nurse" Ya kira su, nan suka dafa masa, suna ƙoƙarin tsayar da jinin da ke zuba ta ƙasanta.
  "Ya Allah! Wani rashin imani ne haka?" Ya faɗa cikin tsoron ganin halin da yarinyar ta ke ciki.

   Fitowa ya yi bayan sunyi nasar tsayar mata da jinin da ke zuba a jikinta, ya kuma basu umarni da suyi mata ɗinki a jikinta.

   A hautsine ya miƙe yana tunkararsa "Likita ƙanwata tana raye? Me ya sameta?"
Numfashi likitan ya ja, a hankali ya zare gilashin da ke idonsa "Ta zubar da jini mai yawa jikinta, akwai yiyuwar sai an ƙara mata jinin."

ISMUHA ZAINAB CompletedWhere stories live. Discover now