BABI NA 31

512 62 1
                                    

*🏌♀ISMAHA ZAINAB 💍*

  ©by *😘Um Nass 🏇🏼*

® *NWA*

  _Ayayin da duniyar ka ta cika da kyautata wa sai ka samu masu karramawa agefe suna jiranka, wasu mutanen sukan bada lokacin su dan su giramamawa wanda yake tare da su, koda basu da alaƙa da su, ayau ina bada Kalmar Giramamawa ta gareki *FATIMA MOROKI* na gode sosai da tarin kulawa_

PAGE 31

  Tafiyar awa biyu ce ta kawo su garin Haɗejia, tun daga  ƙofar shiga garin Musaddiq ke wara ido, komi ya sauya an samu sauyi sosai da ci gaba agarin, ga dandazon mutanen da suke ta zirga-zirga kamar aranar kasuwar garin ke ci.

"Masha Allahu." kalmar da yake faɗa kenan akan laɓɓan bakin sa.
  Har suka shiga unguwar su ta G.R.A nan ma wani sabon kallon ne, saboda kyawawan gine-gine na kece raini da suka fara masa mara ba da shigowa, hata gidan su an ƙara faɗaɗa shi da sabbin abubuwa na zamani ataƙaice tsarin gidan gaba ɗaya ya dawo wani kala daban.
Murmushi yayi yana girgiza kansa ba tare da ya ce komi ba har suka shiga gidan.

  Yayi mamakin ganin ƴan uwa turum agidan suna jiran sa, kwarya-kwaryar liyafar dawowar sa aka  fara yi, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya masa ba.
Tabbas kowa yabar gida gida ya barshi, ya yarda da wanan kalmar ta hausawa, ayau ya jishi daban, ya kuma dawo sabon mutum.

Bai samu kansa ba sai wajan la'asar liss, shima saboda mafiya yawa sun tafi gida jansu, agurguje ya shiga ɓangaran sa, yayi wanka ya shirya cikin farin yadi wanda aka masa aiki da baƙin zare, ya sa baƙar hula da baƙin takalmi, sai agoga baƙi da ya sa, sanan ya feffesa turare ajikinsa.
Agurguje ya kalli agogon dake hannun sa, ƙarfe 5:30 na yamma, ɗan tsaki yayi ahankali, yana fatan Allah yasa ya kada dare ya masa.

  Fitowa yayi ya nufi sashin Umman sa, suna zaune a palo ita da Jidda da Abban sa wanda shima yau bai fita ko ina ba,  da sallama abakin sa ya shiga palon, wanda turaren sa ya rigashi isah.

Atare suka juyo suna kallon sa cikin mamaki Umma ta fara magana "Ina zuwa kuma haka da yamma sakaliyya?"

Kai ya ɗan sosai yana murmushi cikin muryar sa mai sanyi "Zan ɗan zaga garin ne Umma."

  "Amma ai ka bari ka huta kafin ka tafi ko? Duka awarka nawa da zuwa ko barci ba ka samu kayi ba fa."

Murmushi yayi sanan ya kalli Abban sa da sauri yayi Murmushi "Ki barshi yaje ya dawo, tun da kikaga  har yayi kwalliya haka, fitar tasa na da muhimmanci ai."
Kai Umma ta gyaɗa tana murmushi "Ko dai ya samo maka suruka ne ba'a so naji?" Baki ta ɗan taɓe "Idan tayi wari maji ai."

Kunya ce ta kama Musaddiq ya kalli Abba ba tare da yayi magana ba, mukulli mota ya miƙa masa "Rabu da ita ɗan Abba, su bari idan tayi warin sa ji amma ba yanzu ba."

Fita yayi cikin hanzarin sa, mamakin gano shin da Umma tayi yake.
Dariya Jidda tasa masa tana kiran "Yaya nah nazo na maka rakiya?" ko juyowa baiyi ba balle tasa ran zai amsa mata, hakan yasa su yi mata dariya, "Maganin ki ai" Ummah ta faɗa tana dariya.

"Nima tsokanar sa nake Umma, yaushe xan bi Yaya nayi zaman kurame ahanya." ta ƙarasa maganar tana dariya, wanda suma suka tayata, daga nan suka kangara wata hirar wanda mafiya yawa akan halayyar Musaddiƙ ɗin ne.

*****

  Karo na uku kenan yana zagaya unguwar yana kara dawowa, komi ya sauya acikin unguwar, babu kuma wata sheda da ko alama da xai iya ganeta atsawon shekarun da suka wace.

Birki ya take yaja ya tsaya, yana fuzgar da iska abakin sa, wani zafi yake ji acikin ƙirjin sa yana kuma ɗora laifin da wauta irin tasa, mi yasa tun farko bai karɓi Adireshin su ba? Babu wata shedar da ya taɓa karɓa wanda zai gane su awanan lokacin.

Wayar sa ya zaro ya kunna bidiyon da ya ɗauke ta lokacin haɗuwar su ta farko maganar ta yaji tana kiran "Wayyo Luyyah na rabu da ganin ki na mutu."

Ido ya fiddo waje cikin jin daɗi da farin ciki, saboda sunan Luyya da yaji yana ganin kamar ya samu gidan ne, haka kuma kamar matsalar sa tazo ƙarshe.

Wajen da ya kaɗeta ya janyo yana ƙura masa ido, neman wata alama yake da zai gane wajan ko Allah zai sa ya tambayi Luyya ɗin, dan ayanda yaji sunan ta wani kala da ban yasan bazai yi wuyar samu ba.
 
Waiwaye ya shiga yi yana fara duddubawa can ya hango mashigar lungun, sai dai ƙarin shagunan da aka samu da sabon titin da akayi alayin ya taimaka wajan ruɗar da shi. Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi "Alhamdulillah" ya faɗa yana tada motar sa, ƙarasawa yayi wajan shagon da samarin da yaga kamar mazaunin samari ne, tun ƙarasowar motar samarin suke binta da kallo, da yawa numfashin su har tsayawa yake, dan ko ba'a faɗa musu ba sun san ta ciyu Naira kuma ta koka, cikin nutsuwa ya fitowa a motar hakan yasa hankalin samarin ya ƙara iyowa  kansa, da yawa suna kiran "Masha Allah, ko basu sani ba sun san balarabe ne dama xai shigi motar nan."
Ƙarasawa yayi kusa da su yayi musu sallama cikin muryar sa mai sanyi, da sauri suka amsa suna rige-rige.
"Dan Allah tambaya nake?"
Da sauri suka shiga kallon-kallo tsakanin su, jin hausa na fita abakin sa "Allah ya sa mun sani."

  "Gidan Luyyerh nake tambaya."

Kai suka girgiza "Gaskiya babu mai irin wanan sunan na Luyyerh anan unguwar." wani matashi ya bashi amsa cikin bashi tabbacin tambayar da yayi.

"Ya Rabbi!" Musaddiƙ ya faɗa cikin jimami da alhini.
"Baka san sunan mijin ta ko wani daga cikin yaran gidan ba?"

Kai ya riƙe yana shafa goshin sa kamar mai son tuno wani abu, can kuma yayi saurin yin magana "Tana da yarinya inaga sunan ta Ismuha Zainab."

Da sauri wani ya tashi "ohh ce mana zakayi Luyya ai, yanda ka faɗa ne sai yayi kala da sunan ƴan gayu, gidan Alh. Isah gashi can abakin titi." ya ƙarasa maganar yana nuna masa gidan.

Da kallo ya bishi yana sauƙe murmushi "Na gode sosai." hannu yasa a aljihun sa ya zaro kuɗi ya miƙa musu, da sauri suka karɓa suna ta rabtaga musu godiya.
  Har ya shige motar sa "Ina son baƙi irin wanan masu ƙamshin nera, ba wai ƙamas na ƙamure mai warin dauɗa ba." wanda yayi masa kwatancan gidan ya faɗa yana dariya, suma sauran matasan suka tayashi da dariya, anan aka shiga raba kuɗi, suna jinjina ƙarfin kirki da kuɗin mutumin, wasu kuma suna son sanin alaƙar da ke tsakanin sa da Luyya duk da sun san tana da jama'a amma wanan na Musamman ne.

  Lokacin da ya isa ƙofar gidan ya daɗe acikin mota gaban sa na ta faman bugawa, tunani yake akan ta ina zai fara, mi kuma ya kamata yayi awanan lokacin.
Dafe zuciyar sa yayi da yaji bugun ta na ƙaruwa, kamar ance ya kalli ƙofar gidan ya hango wata matashiyar budurwa na fitowa, ido ya ƙwalalo waje cikin mamaki abin da zuciyar sa ke hasaso masa akan ita ce Ismuha Zainab ɗin sa, kai ya girgiza "Bana jin zata kai wanan girma."
Saurin fitowa yayi acikin motar ya ƙarasa wajan ta, har zuwa lokacin ƙirjin sa na harbawa da qarfi da qarfi.
"Assalama alaikum wa rahmatullah" ya faɗa yana kallon ta, da sauri ta juyo kallon ta ga mai sallamar, ƙuri ta masa da ido tana tunanin ina ta san mai irin muryar nan? Mai kuma kamar nan?
Kallon-kallo aka shiga yi ita bata amsa masa ba shi kuma bai ƙara yin wata magana ba.

🥀🥀🥀🥀🥀

#Ismuha Zainab
#NWA
#Cmnts, like nd share
#GIRMAMAWA

   ©Um Nass

ISMUHA ZAINAB CompletedWhere stories live. Discover now