*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
*😘Um_Nass* 🏇
Page 39
Har ta shiga gida tana faman dariyar maganar Muntari, wanda hakan yaja hankalin Luyya take tambayarta har ta dawo? Eh kawai tace mata sanan ta shige ɗakin Innarmu.
Tunani ne ya shiga kai-kawo acikin kwanyarta tana auna ƙiyasin rayuwarsu ita da Luyya komi ganinsa take kamar acikin barcin da kan ɗauke mutum ya farka, gefe ɗaya kuma na zuciyarta na cike da kewa da kaɗaicin mutum ɗaya "Ko ina ya shiga?" dan tun ranar data ce bata sonsa bata ƙara ganin gilmawar sa ba.
Da tarin tunane-tunane barci yayi awun gaba da ita.******
Tun da gari ya waye ya shirya tsab cikin farar shadda wanda hakan ya zama ɗabi'arsa sanya fararen kaya. Kusan duka kayansa kalar fari ne, ɗan banbancin da ake samu bai wuce na zaren da ake yima kayan nasa ado dashiba.
Sai dai yau komi da ya sa ajikinsa fari ne tun daga kan takalmi da agogon azurfar dake hannunsa har hularsa da take ɗauke da adon fari da sirkin ruwan zuma kamar yanda aikin da ke jikin shaddar tasa ya zama kalar ruwan zuma da sirkin farin zare.
Jikinsa ya feshe da nau'ikan turaren da suka zama mahaɗin kwalliyarsa.
Wayoyinsa guda biyu ya ɗauka wanda suma sukayi shige da yanayin shigar jikinsa.
Cikin nutsuwa ya fito daga ɗakinsa ya nufi ɓangaran iyayen nasa, asaman daining ya samesu suna karyawa, hakan ya sashi ƙarasawa yana murmushi.
Sai da ya tsugunna har ƙasa ya gaida su suka amsa cikin jeruwar haɗuwar bakinsu, fuskarsu ƙunshe da fara'a. Sanan jidda ta gaidashi itama tana satar kallonsa.
"Har ka fito kenan?" Umma ta aika da tambayarsa tana murmushi.
Kai ya shafa kana ya murza goshinsa "Eh Umma."
"Ka karya ga abinci nan"
Kujera yaja ya zauna saitin Jidda yana kallon Abbansa da yake cin abinci bai sake magana ba "Umma amma dai jiya anma Abbana horon yunwa agidan nan? Dan naga yau ko kwalliyar tawa bai yaba ba."
Dariya suka saka masa sanan suka juyo da kallonsu ga Abba wanda ya ɗan taɓe bakinsa "Ni ina zan gane kayi kyau, bayan kace bazan maka rakiya ba."
Dariya Musaddiƙ yayi sanan ya murza goshinsa "Jidda nah nayi kyau ai ko?"Kai ta gyaɗa tana murmushi "Sosai ma, nasan tana ganinka sai ta sume saboda kyan da kayi."
Dariya yayi sanan ya dunƙule hannunsa yana murmushi "Nagode ƙanwata."
Dariya Umma ta saka "Yau dai naji kan Aboki da abokinsa tun kan aje ko ina."
"Waya faɗa miki kinji kanmu? Kawai ban son yin magana mai tsayi ne yau."
Abba ya faɗa dai-dai lokacin da yake goge bakinsa da tishu "Kayi kyau sosai Abokina." ya faɗa yana laliben aljihunsa rafar 1k ya ɗauko guda uku ya dire masa agabansa "Ga wanan kayi mata tsaraba dashi, na biya kuɗin kwalliyar nima."
Mamaki da jin daɗi suka cika Musaddiƙ ba shiri ya sauƙa akujerarsa yaje ta bayan Abba ya rungume shi "Na gode sosai Abba nah. Allah ya ƙara girma da Arziƙi."
"Ameen ya Allah." ya faɗa yana bibbiga kafaɗarsa.
"Amma wanan kuɗin bakaga yayi masa yawa?" Umma ta faɗa tana kallon kuɗin tana mamaki.
"Ni inaga kamar yayi kaɗan ma, amma kina batun yayi yawa. Na tura takaddunsa wajan mataimakin govnor idan Allah ya shige mana gaba za'a ɗaukeshi aiki amatsayin lakcara idan kuma sunga matsayinsa yafi hakan zai iya samun fiye da wanan, kinga alokacin zai ɗauki wata jigila da hidimar kansa."
Kai ta gyaɗa tana murmushi "Allah ya taimaka to."
"Ameen ya faɗa yana riƙo hannun Musaddiƙ wanda mamaki ya hanashi yin magana "Muje naga tafiyarka lokaci na ƙara tafiya."
Suma su Umma miƙewa sukayi suka takashi har wajan motar suna masa fatan sauƙa lafiya da saƙon gaisuwa ga surukarsu.
Har ya fice yana ɗaga musu hannu, gefe ɗaya kuma hawaye ke zuba a idonsa, zuciyarsa cike da ƙaunar iyayensa da jin kewarsu atare da shi, kamar da zai bar garin gaba ɗaya.
Tafiyar awa ɗaya da rabi ce ta kawo shi Ƙauyan Kwalam, wanda sai alokacin yake jin fargaba da tsoron abin da zai faru a haɗuwarsu da Ismaha Zainab.
Da tambayar kwatancan da Alh. Isah ya masa ya samu gidan ba tare da ya sha wuya ba.
Fitowa yayi acikin motar tasa, zuciyarsa cike da fargabar abinyi. Da ƙyar yayi ta ƴan maza ya tura wani yaro akan ya kira masa Ismuha Zainab.
Da gudu yaron ya shiga cikin gidan tun azauren farko ya fara ƙwala mata kira.
"Ya Allah!" ta faɗa tana dafe da kanta saboda jin kiran yaron take har tsakiyar kanta.
"Ya akayi ne?" ta aika masa da tambayar cikin ɓacin rai da ganin zallar rashin tarbiyyar yaron.
"Wai ana kiran Ismaha Zainab inji wani aƙatuwar mota awaje." yaron ya ƙarasa maganar yana buɗa hannunsa da son kwatancan girman motar.
Harara ta aika masa sanan tace "Kaje kace bata nan."
"Kai tsaya" Luyya tayi saurin dakatar da yaron "Je kace tana zuwa."
ESTÁS LEYENDO
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...