*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©by *😘Um Nass🏇🏼*
_FOLLOW ME ON WATTPAD @UmNass_
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA BAKWAI (Page 7)
Kallon gidan ta cigaba da yi, hannunta saƙale a jikin na Ismaha Zainab wanda sai faman dariya take da tsalle-tsalle, bata da damuwa ko kaɗan.
"Ina zan dosa a wannan garin?" tambayar da take ma kanta kenan, duk da cewa tana da ƴan uwa da yayya a garin amma bata jin sha'awar isa gare su, hasashe take a kan suma zasu iya korarta kamar yanda mahaifin ta ya kore ta duk da soyayyar da take tsakanin su na Uba da Ƴa, kallonta ta kai ga mutanen da suke zaune a gindin bishiyar da take tsallake da gidan su, tsarguwa tayi da kallon da suke jifan ta da shi, fuskarsa na nuna alhini da tirr da halinta.
"Ai dama rana dubu Allah ke arama ɓarawo yayi ta sharholiyar sa a duniya, amma idan Allah yaso bayyanar da gaskiya cikin rana ɗaya tak asirin mutum yake tonuwa, ko kaɗan ban taɓa tsammanin kamilalliya kamar Ruƙayya wanda ta samu kyakkyawar tarbiyya da nagarta tsatso kamilallai zata aikata kwatan-kwacin abin da tayi a yau"
"Banda abinka NA-TA'ALA ai shi mutum mugun ice ne, sanin abin da ke cikin baɗininsa kuwa sai Ubangijin sa, kai dai kawai kaga mutum amma karka tona baƙin halin dake a tare da shi."
"Haka ne Kallamu, Allah ya shiryar mana da zuri'a"
"Ameen-Ameen sai dai hakan."Hirar mutanen ta soki dodon kunnuwanta wanda hakan yasa zuciyarta ƙara samun zafi da rauni "Tabbas Idris ya cuce ta, ya kuma zalince ta, ta hanyar yaɗa ta a duniya a kan abinda bashi da tabbaci a kan gaskiyar sa, amma kuma ta bar shi da Allah shi zai fidda gaskiya a tsakanin su, babu abin da yayi mata saura na ƙima a cikin wannan garin wanda zata yi tunƙaho da alfahari a gare shi, zaman garin ya fice mata a rai tana jin tsanar komi da ya fito a garin, amma tafi tausayawa rayuwar Muntari sanin yana hannun matar uba, ko wani hannu zai kama kuma? Tambayar da bata da amsar ta kenan hakan yasa ya ja hannun Ruƙayya suka nufi tasha.
Motar Ringim ta nufa dan itace ta cika ana jiran mutum ɗaya hakan ya kawo mata sauƙin tafiya, dan dama ji take kamar tayi fuka-fukai ta tashi tabar garin, zuciyarta ta bushe ta ƙeƙashe daga zubar hawaye.
Kuɗin motar ta biya mutane na kallon ta mafiya yawan ƴan tashan sun san fuskarta dalilin abincin ta musamman matasa, kondostan motan ne ya fara washe baki "Innar Isma kice zaki maraita mu da cin taliya gobe?" kallonsa tayi kana ta ƙirƙiro murmushi ba tare data ce masa komi ba, jikinsa ne yayi sanyi duk da yasan ba haka ya saba ganin taba amma yana da tabbacin akwai damuwa a tattare da ita, hakan yasa yaja bakinsa ya tsuke har suka isa cikin garin Ringim.
A nan fasinjoji suka fara sauƙowa kowa yana kama gabansa, tashar ta kalla tana ganin mutane da suke ta hada-hadar su ba tare da sun damu da kowa ba.
"Ina ya kamata na nufa?" tambayar da ta jefawa kanta kenan, dan ko kaɗan bata jin sha'awar zama a cikin Ringim dan yayi kusa da garin su, hakan yana nuna cewar bata bar matsala ba, dan ko yaushe zasu iya haɗuwa da mutanen garin su musamman da ya zama Ringim gida ce a wajen su, kullum cikin zuwan ta suke, koda ta samu wata ƙima a garin za'a samu wanda zai mata dirar mikiya ya faɗi abin da yaji a kanta na gaskiya da ƙarya, ya goge ƙimar da zata samu a idon mutanen."HAƊEJIA JIGAWA" muryar wani kondostan mota ta bugi kunnenta yana faman ɗaga hannu "Haɗejia Jigawa saura mutum ɗaya" maganar da ya sake yi kenan, ji tayi zuciyarta na ingiza ta a kan ta tafi ta shiga motar, hakan yasa ta ƙarasawa kusa da kondostan motar "Ina son zuwa Haɗejia" ta faɗa ba tare data haƙiƙance a kan tana son zuwa garin ba, ba kuma dan ta san garin ba, asali ma sunan sa kawai take ji a bakunan wasu, sai dai a yanda take jin zuciyarta na azalzalar ta babu abin da zai dakatar da ita daga zuwa garin.
Baki kwandostan motar ya washe nan ya ɗauki ɗan ƙullin kayanta yana faɗin "Taho muje Hajiya" bayan sa tabi suka nufi wajan mota babba (Bos) nuni ya mata da kujerar data rage a nan ta hau tana karanto "Bismillahi" a kan laɓɓanta kana ta zaunar da Ismaha Zainab a kan cinyarta, bata ƙara ma kowa magana ba ganin babu wanda ta sani, mafiya yawa maza ne sai matan da ba zasu wuce uku ba a cikin motar, damuwar da take tattare a cikin zuciyarta ba zata bata damar da zata musu magana ba hakan yasa ta kwantar da Ismaha Zainab a kan ƙirjinta ta jingine kanta a kan kujera tana lumshe ido, sosai hayaniyar mutanen wajan ta takura mata ji take har tsakiyar kanta, ƙaran rufe motar da taji an yi shi ya sata buɗe ido, kwandostan motar ne ya shigo shi da Direba nan ya fara karɓan kuɗin motar mutane ɗari biyar babu ragi babu ƙari, kuɗin ta zaro ta miƙa masa kana ta sake rufe idonta, ba dan tana jin barci ba sai dan tana so tabar jin raɗaɗin da take ji a cikin idanuwan nata.
KAMU SEDANG MEMBACA
ISMUHA ZAINAB Completed
PertualanganAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...