*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©BY *😘Um Nass 🏇*
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN DA BIYU (PAGE 22)
Hannu takai da zummar ta daketa sai kuma taga rashin kyautawuwar hakan, nan ta shiga surfa masifa har dai Ismaha Zainab ta tashi take mitsittsika ido, wanda yayi dai-dai da tashin ɗaukacin mutanen ɗakin.
"Sauƙo min akan gado munafuka! Ashe ko gama futsarin kwance bakiyiba aka kawo min ke?" tana magana numfashinta nayin sama saboda ɓacin rai, babban takaicinta fitsarin yarinyar data haɗiya har cikin ta.Sauƙowa Ismaha Zainab tayi, jikinta jagaf da futsari abin da bata taɓa yiba kenan tun ƙuruciyar ta, amma yau itace akema tijara haka wata kunya ne taji ta dirar mata wanda bata taɓa jin irin taba, hawaye kuwa kamar an ɓalla famfo haka yake zuba akan fuskar ta.
Watso mata katifar ta tayi a santar da sauran yara marasa galihu suke kwana, sanan ta ci gaba da wurgo mata sauran komatsanta "Tun farko da nasan haka kike da babu dalilin da zaisa na gayyato ki kwana ta. Ga tsiyar kayan ki nan kije can ki ƙaraci futsarin ki."
"Yau naji tujara ke Marwanatu mi yasa baki da haƙuri ne? Da wanan tsohon daren kika cikama mutane kunne da masifa, gashi kin hana kowa yin barci." Wata dattijuwar tsohuwa ta faɗa tana fitowa daga wani ɗaki da alama mallakin ta ne, haka kuma itake da alhakin kula da ɗaliban da suke cikin ɗakin.
Baki ta murguɗa duk da duhu ne amma kasan bata da kunya ko kaɗan "Futsarin kwance fa tamin ya shiga har bakina, da taci sa'a ma ban daketa ba iya faɗan ne ai ta ji daɗi."
"Wacece ne ta miki Futsarin?" ta sake faɗa dai-dai lokacin da take dallara fitilar hannu.
Da hannunta ta mata nuni ga Ismaha Zainab wanda take raɓe tsamo-tsamo.cikin futsari. Tausayin ta ne ya kamata "Wanan da ɗaukan alhaki ma kike. Yarinyar nan duka nawa take? Awanan bam-bamin faɗan naki sai na ɗauka da sa'arki kike Mtss" ta ƙarasa maganar tana buga tsuka.
Sanan ta koma ɗakin ta ba tare da tayi magana ba, sauran mutane ɗakin suma suka kwanta da yawa suna jan Allah ya Isa akan hanasu barcin da Marwa tayi.
Hannuta Sa'adatu ta riƙe cikin tausayi, asaninta bata taɓa ganin Ismaha Zainab hakaba. Da wuyama kaga abu ya ɓata mata rai balle tayi kuka harda jan zuciya. Rungumeta tayi tana sauƙe ajiyar zuciya akai-akai tanaga wanan tozarcin ya isa haka."Shikenan yi haƙuri, zo muje mu kwanta ashimfiɗa ta." daga haka taja hannun ta bayan ta cire mata kayan jikinta ta sauya mata wani, suka kwanta akatifar ta duk da ƙan-ƙantar ta, amma ta ishesu. Rungume Sa'adatu tayi tana sauƙe ajiyar zuciya mai yawa, har ga Allah nadama ce da kuma tarin dana sani suke sauƙar mata na zuwa wanan makarantar, dama ace zata dawo da jiya yau, to da babu makawa zatayi fatan ace ta soke ko wani zirƙilli da zaƙewar da tayi akan zuwa wanan garin.
*****
HAƊEJIATun bayan tafiyar su Ismaha Zainab hankalin Luyya ya tashi ƙwarai, fargaba da tsoron abin da zai iya zuwa ya dawo ya cika mata zuciya.
Allah ya sani tana mutuƙar jin tausayin ɗiyarta, kwatan-kwacin yanda take sonta, akwai matsalar da ke ɗawainiya da rayuwar Ismaha Zainab wanda babu wanda ya sani sai ita, amma kuma itama ta gaza nema mata maganin da zai zama kariya agareta. Daɗin daɗawa ƙiriniyar ta da take ƙara ninkuwa acikin ko wata rana, gashi yanzu ta tafi garin da babu uwa babu uba ba kuma gwaɓa, sai dai jiki magayi, Allah dai ya kareta kawai.Dai-dai dawowar su Usama da Alh. Ali suke sanar da mutanen gidan sun bar Ismaha Zainab acan sai rawar kai take "Gaskiya makarantar jeji ce sosai, gata kuma alungu akwai tazara mai yawa kafin ka isa cikin gari." Usama ya faɗa yana kwaɓe baki, duk da ba shiri suke da Ismaha Zainab ba yaji kewar barin ta agarin nan.
YOU ARE READING
ISMUHA ZAINAB Completed
AdventureAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...