BABI NA 15

449 52 0
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

©BY *😘UM NASS🏇*

 
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

_Lokuta da dama ɗan Adam yakan kasance cikin bulayi da rashin madafa akan anya ba shi kaɗai ke kiɗansa da rawarsa ba ba tare da mataya a tare da shi ba? Sai gashi daga baya idan yayi haƙuri da tsaikon da ake samu, yakan samu cincirindon dafafi na dubban masoya, a raina naji tasirin dake cikin Alƙalami ya zarce na dubban takkuba, na kuma haƙiƙance akan jinginar da nawa muradin dan girmama naku fatan. Gare ku masoya masu bibbiyata a duk inda kuke wannan labarin gaba ɗaya sadaukarwa ne gare ku nagode sosai._

BABI NA SHA BIYAR (page 15)

  Hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa ya cigaba da kallon su suna dariya, can yaga abin nasu bana ƙarewa bane yayi gyaran murya. Take suka shiga taitayinsu suna wurga ido, musamman zakar da yaga fuskar mutumin kamar babu alamun rahma a tare da shi, cikin ƙoƙarin son zamewa ya fara matsawa da baya da baya, amma kafin ya kai ga matsaya ya tsinkayi muryarsa.

  "Kada ka tafi ka barta." cakk ya ja ya tsaya yana kallonsa, murmushi akan fuskarsa ya zare wani ƙaramin akwati a cikin Aljihunsa, hannun Zakar ya kama ya ɗora masa wannan abin "Nasan kana a matsayin yayan ta ne a yanzu, kana kuma da wayo a kanta, ka ajiye mata wannan kada ka nunawa kowa, idan har Allah ya aranta mana tsawon rayuwa nan da shekaru goma ka bata shi, na tabbata a duk inda nake zan neme ta adai-dai wannan lokacin."
Karɓa yayi yana jujjuya ɗan akwatin da aka kewaye shi da leda mai ƙyalƙyali, ya masa kyau sosai amma ganin yanda aka tantankeshi yana nuni da cewar koma miye a cikinsa yana da muhimmanci.

  Hannu ya miƙa ma Ismaha Zainab cikin murmushi da saurinta ta miƙa masa tana dariya, suka gaisa "Musaddiƙ sunana ba ƙato mai mulyal yara ba." ya ƙarasa magana yana kwaikwayon muryarta, hakan ya sata dariya ita da Zakar kafin itama ta ɗaga idonta tana jujjuyawa alamar son magana, kai ya gyaɗa mata cikin nuni da ta faɗi abin da yake ranta. 

"Icmaha Dainab, nima ba baby ba", hakan da ta faɗa yasa su dariya sosai, cikin rashin fahimtar kalmar Icmaha ɗin ya kalli Zakar.

"Mi take nufi da Icmaha?".

"Ismaha Zainab zata ce haka ake faɗa mata."

Murmushi yayi sosai har haƙoransa suka bayyana "ISMUHA ZAINAB ko dai? Sunanki Zainab?" ya faɗa cikin sigar tsokana wanda ya sata yin murmushi kafin ta zame hannunta daga nasa.

  "Ya zakal mu tafi kal amin bulalal makala."

Kai ya gyaɗa cikin dariya sannan ya kalli Musaddiƙ "Makaranta zan rakata kada ta makara."

Hannu ya saka a cikin Aljihunsa ya ɗauko rafar 50 ya danƙama zakar, saurin buɗe ido yayi yana girgiza kai gami da matsawa baya alamun kuɗin sun bashi tsoro "Luyya ta hana mu karɓan kuɗi ko kaɗan ne, balle wannan mai yawa gasu sababbi."

Kallon yaron yayi yana tuna ranar daya fara haɗuwa da Ismuha Zainab idan bai manta ba itama haka ta sanar da shi a lokacin da yayi mata kyautar kuɗi "Wacece Luyyah?" Ya samu kansa da yi musu tambaya, da zai yi wuya ace mamansu ce.

  "Ummanmu ce ni da ya Zakal" yaji sautin Muryar Ismaha Zainab na sanar da shi matsayinta.

"Ok. Kuzo na ɗauke ku a hoto saboda ina tunawa daku." da sauri Ismaha Zainab sarkin son hoto ta matsa kusa dashi ta fara lanƙwasa da kareraya, tun yana ɗaukan ta har dariya taci ƙarfinsa ya kasa dan abin da take ya wuce bashi mamaki sai dariya. Maƙalo wuyansa tayi tana cunno baki  "Oya Mai mulyal yala ka mana tare." kallonta yayi yana murmushi kafin yayi wani yunƙuri ta danna ta ɗauke su, ƙara maƙalƙale shi tayi tana dariya a haka ta ɗauke su sannan ta sake shi ta ja hannun zakar da yake ta musu murmushi.

ISMUHA ZAINAB CompletedWhere stories live. Discover now