*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©BY *😘Um Nass 🏇*
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
BABI NA SHA BIYU (page 12)
Kallonta taci gaba da yi har taji sauqar numfashinta ahankali, wanda yake bata tabbacin da cewar barci ya ɗauketa, ajiyar zuciya ta sauƙe mai ƙarfi kana ta gyara mata kwanciyarta akan ƙatuwar katifar da take yashe atsakar ɗakin, acikin shekaru biyun da sukayi ta samu alkhairi da yawa wajan sana'arta, hakan yasa ta gyara muhallin da suke ciki ta siya ƙatuwar katifa da kuma ma'adanar ajiye kayansu.
Acikin waɗan nan shekarun da suka wuce ba zata ce bata da manema masu sontaba, asalima ita ke gudunsu, saboda komi zatayi tana duba makoma da rayuwar da ƴarta tilo zata faɗa agidan da xa'a kirata agola, wanda bata shirya jin wanan kalmarba, amma kuma ako ina tayi aure dole akira ɗiyarta da wanan sunan, sai kuma dalili mai girma na daƙusar da sana'arta da zata iya faruwa, wanda itace silar barinta garinsu, aranta tana jin bata shirya zaman kashe wando ba, amma kuma babu dalilin da zai hana aharamta mata neman halaliyarta.Miƙewa tsaye tayi ta fara kai kawo atsakar ɗakin, ganin hakan bazai mataba ya sata miƙewa ta zari Hijabinta, awanan lokacin tasan zata samu Malam Isubu agida, tana buqatar abokin shawara, fitowa tayi ta yima Maman Zakar sallama akan zata leƙa gidan Malam Isubu amma ga Ismaha Zainab na barci ta kular mata da ita, to tace mata tana binta da kallon tuhuma ganin yanda idanuwanta suka kumbura, sai dai ganin tana sauri yasa bata dakatar da itaba balle ta tambayeta, har ta fice tana mamakin abin da yasata kuka.
Bata da shamaki da shiga gidansa hakan yasata yin sallama ta kutsa kai "Maraba da Luyya innar Ismaa Abu" Faɗar matar Malam Isubu cikin tsokana da barkwanci, kamar yanda ta saba yimata ako yaushe, murmushi tayi ta samu kujerar tsugunno datayi karo da ita atsakar gidan ta zauna.
"Gidan shuru haka, ina yaran suke? Ai da na turo miki Ismaha Zainab ta tayaki hira"
Haɓa tayi saurin riƙewa "A'a na yafe wanan tayin nata, dan idan tazo sai ta gauraya min gida ta kuma saka min ciwon kai da tsinanniyar tambayarta marar amfani."Dariya Luyya tayi mai sauti har tana riƙe ciki ganin yanda Iya Kaltum take magana cike da tsoro da sarƙewar murya "Kaii Yaya Kaltum har haka kike tsoron ƙawar taki, ai yanzuma sa'a kikayi tana barci da tare zamu taho, amma nasan tana tashi zata taho."
"Ai gara, na gode Allah da tayi barci ai."
"Wajan Yaya Isubu nazo, Allah yasa yana nan?""Eh yana nan, kin taki sa'a dan yanzu ya qare cin abinci ya shiga ɗaki ya ɗan rintsa, amma nasan yaji maganarki."
"A'a barshi ya kwanta anjima sai na dawo."
"Ina kuma zaki bayan kin zo, barci ai baya samu ga talaka awanan ranar"
Murmushi tayi tana jinjina kai "Duk da haka dai ni na katse maka jin daɗin naka. Ina yini Yaya Isubu?" ta ƙarasa faɗa tana murmushi, shima dariyar yake yana kallon fuskarta wanda har yanzu akumbure take ga kuma shatin hawayen da aka goge ya bushe, Zama yayi akan tabarmar da Iya Kaltum take kai kana ya fuskanceta."Lafiya lau Ruqayya, mi yake faruwa naga Fuskarki da damuwa."
Kai ta sunkuyar ƙasa ahankali ta fara magana, wanda hakan yasa Iya Kaltum miqewa zata bar musu wajan "Ki zauna yaya kema ba xaki rasa abin da zaki faɗaba" Luyya ta faɗa wanda hakan yasa Iya Kaltum zama tana kallonta.
"Muna sauraronki Ruqayya, Allah yasa matsalar da take tafe dake ba babba bace?"
"Awajena babba ce yaya Isubu sai dai awani ɓangaran kallon ƙarama za'a mata, yau Ismaha Zainab tazo min da tashin hankali mai girma, ina kuma jin tsoro kada matsalar nan gaba tafi haka muni."
Kallonta sukayi cikin mamaki kana suka fara magana "Wata kalar matsala ce haka Ruqayya?" Nan ta zauna ta faɗa musu rigimar da Ismaha Zainab ta mata akan nemo mata Babanta.
Numfashi taja ta fuzgar da iska mai ƙarfi "Ba ƙin kaita gida nayiba Yaya kun riga da kun san matsalar data baroni da garinmu, ina jin tsoron na maidata har yanxu ƙurar bata lafa ba, araina nafi son duk lokacin da zan koma gida na koma da kimata, na koma da ɗumbin girmamawa daga wajan mutanen garinmu."
ŞİMDİ OKUDUĞUN
ISMUHA ZAINAB Completed
MaceraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...