*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©BY *😘Um Nass 🏇*
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN DA HUƊU (PAGE 24)
MISRAH
"Ni wallahi har mamakin ka nake Musaddiƙ kana ɓata ma kanka lokaci da yawa a kan wanan ƴar yarinyar. Ga Khairat babbar yarinya ƴar gidan jakadan Nigeria ta mace a kanka kana wulaƙanta ta, ya kamata ka sauya hali da tunani fa."
Kallonsa yayi yana lumshe ido fuskarsa ƙunshe da murmushi, cigaba yayi da daddana na'ura mai ƙwaƙwalwar da ke gabansa ba tare daya tanka masa ba.
Tsaki Ma'aruf yayi kana ya miƙe yana bibbiga litattafansa "Kanada ɗaga kai da wulaƙanci Musaddiƙ. Wata ƙila saboda Allah ya fifita matsayinka fiye da namu, ya kuma albarka ce ka da tarin ilimi da kyau gami da farin jini a wajan mutane shiyasa kake nuna halin ko in kula a kan duk wanda ke raɓar ka. Babu komi kayi haƙuri da shiga rayuwarka da nake yi."Juyawa yayi da zummar barin wajan, wanda Musaddiƙ ya bishi da rakiyar ido kamar ba zai masa magana ba, amma kuma yasan rigimar Ma'aruf wannan ba shine karo na farko da suka saba sa-in-sa akan maganar Khairat ba, bai kuma san dalilin da yasa yake adawa da soyayyar da yake nunawa Ismuha Zainab ba duk da ƙarancin shekarun ta.
"Ma'arufff!" Ya kira shi cikin sassanyar muryarsa mai fita da nutsuwa da amo mai daɗin ji. Cak ya tsaya amma bai juyo ba dan yana cike da jin haushin share shin da yake yi. Murmushi Musaddiƙ yayi sannan ya miƙe ya nufi kusa da shi, gabansa ya sha yana kallon sa gami da Murmushi wanda ya zama ɗabi'a a gare shi "Na ɗauka kai ne mutum na farko da zaka bada labarin kyawawan ɗabi'u na, ka kuma kare ni a duk inda kaji za'ayi suka a gare ni ko kuma a ɓata min suna ta hanyar jingina ni da Mummunar sifa kwatankwacin yanda kayi."
Murmushi yayi mai sauti yana naɗe hannayensa a ƙirjinsa, idonsa fess akan na Ma'aruf da shi ma yake kallonsa "Kimanin shekara uku muna tare da kai amma kuma har zuwa yanzu ka gagara yi min uzuri da adalci a kan ɗabi'ar da bani na siya ma kaina ba. Matsalar ka kullum akan maganar Khairat ni kuma ga wanda zuciyata ke so take ta dakon jira akan lokaci ya aranta min kasancewa tare da ita."
Kai ya girgiza yana ƙara yawaita murmushi, a cikin idonsa yake hango kamanninta da komi nata "Ina sonta duk da ƙarantar ta, tabbacin da na samu akan zan iya samun ta shine ya baro ni da ƙasata bayan na cire hakan a raina. Kai abokina ne na kusa ina son ka dunga min adalci akan ko wata kalma da zaka jinginata a gare ni. Bana son hayaniya bana son magana wanda bazan anfana da alkhairi a cikin taba."Yana gama faɗar haka ya koma mazaunin sa ba tare daya ƙara bi ta kan Ma'aruf ba.
Kunya ce ta kama shi sosai jin kalaman da suke fita a bakin Mussadiƙ, tabbas yau ya kai shi maƙura tunda ya fallasa abin da ke ransa, duk da a tsawan shekaru ukun da suka yi yasan abu da yawa a kan Musaddiƙ ɗin, haka kuma ya daɗe da sanin matsayin da yarinyar ta taka a zuciyarsa, amma kuma ya kasa fahimtar mi yasa shi baya taya shi son ta? Bai kuma san mi yasa yake adawa a duk wani abun da zai zamo na tsaginta.Juyawa yayi yana kallon Musaddiƙ wanda ya cigaba da daddana wayarsa kamar babu wani abun dake damunsa, yana da zunzurutun wahala kaga damuwa akan fuskarsa koda kuwa kai ka baƙanta masa rai, haka kuma ba zai taɓa nuna maka ransa ya ɓaci ba a cikin ruwan sanyi yake hukunta ka da shurunsa, shi yasa yake mamaki da yanda har ya kamu da soyayyar yarinya ƙarama.
"Kayi haƙuri kaji abokina, ina jin haushi na ma magana ka ƙyale ni. Har yanzu na kasa yin sabo da shurunka."Murmushi yayi sannan ya rufe laptop ɗin nasa ya miƙe tsaye "Lokacin lacture ya gabato kada mu makara."
"Amma ai bamu gama maganar da muke ba, ba kuma ka bani amsa akan abin dana faɗa ba."
Kai ya girgiza yana ɗaukan litattafansa ya fara fita, da baya ya bisa yana ƙara masa mita akan ƙin bashi amsar da yayi.
"Ma'aruf mana! Ba ko wata tambaya bace take samun amsa, shi kuma shuru a duk inda yake yana zuwa a muhallin amincewa ne, ka koyi zama da kurma koda na rana ɗaya ne zaka amfana da baiwar da Allah ya bashi."
Baki ya kwaɓe cikin ƙara jin takaicin sa "To ma miye maraba tsakanin kai da kurame, wani lokacin garama a bar ni da kurma nasan baya ji na."Shi dai murmushi yayi ya ƙara ɗaga ƙafafuwansa dan ganin idan ya biya Ma'aruf zai kwana yana mita shi har mamaki yake wani lokacin kamar mace haka yake da mita.
*****
KAUGAMAYau ranar juma'a hakan yasa duk ɗalibai suke nufar wajan taro a cikin hostel, gaban wata ƙatuwar bushiyar maina, wanda duk itace mafi yawa a cikin makarantar, amma wannan ta fi sauran girma har kwanciya tayi, gata kuma a tsakiyar hostel ɗin, shiyasa ma jiniyas suke ma wajan kirari da dandalin sharri, dan ko wata ƙura aka kwaso a nan a ke dire musu.
Gashi kuma duk ranar juma'a sai an tarasu an ƙirƙirar musu laifi na gaira babu dalili. To yau ma dai hakan ce dan duk malamai sun tafi hutun mako.
Kamar ko wani taron da ba na alkhairi ba siniyo jummai ke buɗe shi da ashariya da ƙirarin da take ma kanta akan na wadda tafi kowa "Yau babu sallama da buƙatar gabatar da kaina a gare ku. Sai dan zan yi muku albishir da cewar wannan satin nacin dunduniyar takalmin uwarku ne da kuma ɗankunnin da ke kunnenta, musamman ƴan aji biyar. Jiya nayi sanarwa akan a kai min ruwa kitchen da ƙyar mutane talatin suka kai, dan haka zan kira suna."
Nan kuma aka shiga kallon-kallo tsakanin ƴan aji biyar da sauran jiniyas ɗin, tsawa ta buga cikin muryarta mai tsoratarwa "ƴan aji biyar ku ware gefe, sauran jiniyas kuma ƴan aji ɗaya zuwa uku su tafi ɗaki."
Nan aka rage daga ƴwn aji biyar sai na huɗu, gefe ɗaya kuma Ismaha Zainab ce ta tsaya tana muzurai, ko shakkah bata yi wannan mai ƙirar masu shan jinin ba alkhairi zata shuka ba.Komawa tayi kusa da Sa'adatu wanda dan tsoro da fargaba har ta fara kuka, sanin bata kai ruwa jiya ba "Anty Sa'adatu ai dukan ku za tayi? Kuma ai kun fita yawa kuje ku tarar mata mana. Shine kuke kuka tun yanzu?"
A tsorace ta juya ta kai kallonta ga Ismaha Zainab sam bata yi tsammanin zata tsaya ba balle ta zo har inda suke "Ke Ismaha ki tafi ɗaki kada ta dake ki."
Kafaɗa ta maƙale cikin jin tausayin sa'adatun sannan ta zauna a wajan itama.
Rarrashinta ta fara yi akan ta tafi amma kuma taƙi tafiya, a haka aka kawo bulallai tari guda, tun a nan idonsu ya raina fata idan aka ɗauke Ismaha Zainab da ta fiddo ido waje cikin mamaki "Tabɗijam kamar za'a bugi jakkai."🥀🥀🥀🥀🥀
_Yau bana jin typing akai na sai da na daure nayi saboda faranta muku rai kawai._
*Ba ra'ayina bane saka zagi cikin labari amma ga duk wanda yayi bodyn skull yasan wannan ƙarami ne daga cikin ɗabi'ar makarant, akan haka nake neman fahimta daga gare ku.*
*GIMAMAWA*#Um Naass
#cmnts, like nd share
#Da Amana
VOCÊ ESTÁ LENDO
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...