*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©BY *😘Um Nass 🏇*
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN (PAGE 20)
Tafiyar awa guda ce ta kai su makarantar ƴan mata dake Kaugama, Tun a bakin get jikin Ismaha Zainab yayi sanyi, ganin makarantar kewaye da wayoyi "Anya za'a samu abin arziƙi a nan?" tambayar da ta yima kanta kenan, sai dai kafin ta lalimo amsar da ya kamata ta ƙarfafa zuciyarta an wangale musu get suna shiga, tsitt kake ji babu motsin ɗalibai kasancewar safiyar Litinin ce kowa na aji yana ɗaukan darasi.
"Fito Ɗiyata" Alh. Isah ya faɗa yana ƙoƙarin fitowa, fitowar itama tayi cikin unifoarm ɗinta farin hijab farar riga sai zani mai gida-gida launin kore da fari da ɗan kwalinsa.
Kallon ko ina take a makarantar babu wani na sabunta da zai tabbatar mata da ƙawar da aka bata a cikin labarin.
Wani office suka nufa itama tana bin bayansu, sai a lokacin ta fahimce ashe mai ɗaukan sunan ɗalibai ne. Bayan ƴar taƙaitacciyar gaisuwa suka danƙa musu amanar Ismaha Zainab, lokacin yace su jira a kira musu wanda suka sani dan ta kai ta Ajinsu.
Da murna Sa'adatu tazo tana washe baki ta gaida Alh. Isah da Usama da fara'arsu suka amsa sai a lokacin ta kai dubanta ga Ismaha Zainab cikin nuna jin daɗin ganinta ta rungume ta tana mata Maraba da zuwa, ƙamewa tayi tana binta da kallo sai baza ido take tana ƙiftasu.
Anan dai suka juya suka tafi suka barta kamar tace ta fasa amma ɗoki da murna ya hana tabi ta kansu, Usama kuma sai washe haƙori yake ya ɗauko kuɗi ya ƙara mata a kan wanda Alh. Isah ya bata sannan suka juya suka bar ta.
Hannunta Sa'adatu ta riƙe ta kai ta Ajin da a kace ta kai ta J.s.s 1A, lokacin malami yana cikin ajin. Gabatar da ita tayi a matsayin ta na sabuwar ɗaliba sannan ta juya ta barta da zummar idan an tashi zata zo su ɗauko kayanta su nufi Hostel (Ɗakin ɗalibai).
Malamin ne ya nuna mata bancin gaba wanda yara biyu suke kai, zama tayi suka cike uku, daga nan ya cigaba da koyar dasu darasin Nahau Wadiy.
Bayan an kaɗa ƙararrawa ya fita a lokacin hankalin ƴan bancin ya dawo kanta. Da murna suke mata barka da zuwa, suka fara gabatar mata da sunayensu Maryam Wada sai kuma Hauwa Tanimu, duka ba zasu wuce sa'anninta ba "ISMAHA ZAINAB IDRIS" ta faɗa cikin murmushi. Nan suka fara dariya "Sunanta zainab" itama dariyar tayi suka shiga fira har suna ce mata makonsu ɗaya da zuwa suma basu daɗe ba. A haka wani malamin Adab da Insha'i ya shigo hirar tasu ta katse.
Bayan ya ƙare aka kaɗa musu zuwa karɓan abinci, a lokacin kusan 11:30am mamaki ne ya kamata da taji cewar sai a lokacin za'a karɓi abincin safe.
"To mi kuke ci da safe? Dan yanzu kam ai an kusa zuwa lokacin rana, taɓ wannan ai sai hanjin mutum ya tsittsinke."
Dariya suka mata sosai sannan Maryam Wada tace "Dama ai sai dai kayi kwaɗon ƙanzo ko kwaki idan kuma akayi sa'a ka karɓo tuwon dare sai kayi kwaɗonsa ya mafi daɗi."
Ido ta ƙwalalo waje cikin tashin hankali ta fara magana "Wani kwaɗon tuwo kuma bayan ance har shinkafar kaza ana rabawa? Allah ya sauwaƙe ma haƙorana tauna kwanannan tuwo"
Dariya sosai suka sa, cikin dariyar Hauwa Tanimu ta fara nuna Ismaha Zainab "Ashe fa shinkafar Kaza, to garama ki ware yarinya, anan sau ɗaya ake raba nama a sati a haka ma tsoka ɗaya kawai za'a baki, yo kika samu tuwo ai kin kere sa'a, dan shi kansa tuwon samunsa sai mai rabo, balle har ya waye miki."
Kai ta girgiza cikin son ƙin ƴarda da hirar tasu "Ko da wasa bazan taɓa yarda da wannan maganar taku ba. Haba sai kace wasu akuyoyin ɗaure."
Shuru sukayi basu ƙara tanka mata ba har suka ƙarasa wajan karɓan Abincin, ido ta ƙwalalo waje ganin dogon layi wanda a lissafinta kusan mutum ɗari uku ne, sai faman ture-ture a ke da kokawa, gefe ɗaya kuma masu mulki ne sai faman gyara layin suke suna dukan mutane.
"Na shiga uku ni Ismaha Zainab wannan uban layin na miye kuma?"
"Na karɓan abinci ne mana" suka amsa mata a tare suna ƙoƙarin bin layin.
'Taɓɗijam! Gaskiya ni bazan iya bin wannan dogon layin ba, haba sai kace da a ke dafa raƙumi kuga inda ake dukan mutane kamar wasu jakkai."
Ta ƙarasa faɗar haka tana ƙetare mutane tana kallonsu, kafin su Hauwa Tanimu su mata magana tuni tayi gaba abinta da ido suka bita suna mata fatan Allah kare jikinta.
YOU ARE READING
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...
