*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB💍*
©BY *😘UM NASS🏇🏼*
BABI NA UKU (Page 3)
Washe gari:
Ƙofar gidan a cike take taff da mutane kamar yanda ya zama sabo, wasu suna tsugunne suna cin abincin yayin da wasu suke gefe ɗaya a tsaye da alamun jira suke a zubo musu nasu.
Wani ɗan Almajiri ne wanda bazai wuce shekara 7 ba yake zirga-zirga tsakanin masu gidan da wajen da alama shine mai karɓan kuɗi da kuma kai musu abincin da suke siya.
Buguzun-buguzun take tafiya kamar zata tashi sama fuskarta babu walwala ko kaɗan a cikinta gefe ɗaya kuma Tani ce da kululu ƴan koranta suke take mata baya har cikin gidan, dai-dai lokacin da Ruƙayya take zuba abinci gidan ta tsaf-tsaf babu hayaniya da tarkace a ko ina ɗin nan na kwanika, dan tana siyarwa tana wankewa, duk wanda ya ci a kwanon ta sai ta wanke kana ta zubawa wani a cikin kwanon, batayi aune ba taji an tankwaɓe kwanon da take zuba abincin, zubewa abincin yayi a ƙasa kwanon ya kife, cikin ɓacin rai ta ɗago dan taga waya mata wannan aika-aikar, ganin Fuskokinsu da tayi yasa gabanta faɗuwa ga kuma Innar su Kamalu sai huci take kamar baƙin maciji, "Ni zaki maida ƙaramar yarinya sa'ar ki, na kafa doka a cikin gidan ɗana amma kisa ƙafa ki shure, saboda kin shahara kin gawurta da bin maza da maida ƙofar gidan ɗa na sansanin bariki, wannan ya shiga wannan ya fita." ta faɗa tana huci kana ta janyo fantekar taliyar tayi jifa da ita, nan ta komaɗe sauran taliyar ciki ta zube, ido Ruƙayya ta runtse hawaye na zuba a cikinsa, wannan tozarci wannan cin kashin yayi yawa, kafin ta buɗe idonta tarr akan Innar su Kamalun wanda taci gaba da tijarar ta "Tunda baki da mutunci baki san girma naba, a yanzu na janye ko wani zaɓi dana baki dole ne kibar gidan nan a yanzu-yanzu na baki ƙwararan saki uku Cirr a madadin Idirisu." hannu su tani suka ɗaga suna tafawa ita da kululu "Shikenan magana ta ƙare."Kallon su take baki a buɗe cikin mamakin maganar su, da ƙyar ta aro dauriya tayi murmushin da bai wuce na saman laɓɓa ba "Inna ai baki da ikon da zaki sake ni kice na saku, domin igiyar saki na tana hannun Idris, sai dai idan ya dawo kina da iko da duk wata dama a matsayin ki na mahaifiyar sa da zaki tirsasashi kice ya sake ni, sannan ina baki haƙuri akan gidan ɗanki da kika ce ina sana'a amma kuma ke kika janyo hannuna kika shigo dani gida na a matsayin matar da zata zauna a gidan, sannan abu na gaba da shawarar ki ne na fara sana'a ta dan haka yanzu babu wanda ya isah yace bazan yi taba, dan baku da abin da zaku bani."
Baki buɗe Innar su Kamalu take kallon ta cikin mamakin maganar ta, a sanin ta ko musayar magana bata taɓa haɗasu da Ruƙayya ba amma kuma yau sai gashi ita ke faɗa mata magana mai zafi haka, mamaki da tsoro ya sandarar da ita ta gaza magana, hakan yasa Tani ta ɗauki salati "Lallai Ruƙayya wuyanki ya isa yanka, yanzu Innar su kamalun kike faɗawa haka? Mahaifiyar data halallaƙo mijin ki kike cewa bata da ikon sakin ki, amma kuwa in baki manta ba duk duniya babu wanda ya kai ta a wajan kamalu, haka idan ta saka masa kara baya tsallakawa, ko a wannan gaɓar nasan iyaka yace to amma ba wai yace hukuncin ta bai iyuba, sai gashi ke kin maida mata magana son ranki, lallai idan da ranka zaka ga abubuwan mamaki." ta ƙarasa maganar tana matsar hawayen munafurci.
"Ni ai ban san abin faɗa ba ko kaɗan, lamarin Ruƙayya yau ya wuce na masu hankali, Innar kamalu yau kam an nuna miki iyakar ki, fatana da roƙona ɗaya Allah yasa basu asirce miki ɗan kiba, inada naga tana magana da ƙarfin gwuiwar ta kamar ta shiryawa hakan." Kululu ta faɗa tana gyara tsayuwar ta da riƙe haɓa wanda yake nuna tsantsar jimami da tausayin Innar kamalu.Jin maganar su yasa innar kamalu ƙara haukacewa nan ta shaƙe wuyan Ruƙayya ta haɗa ta da bango, cikin tsantsar masifa da hargagi ta fara magana "Aradun Allah jinina yafi ƙarfin ki ɗiyar kurma, ni zaki maidawa magana Ruƙayya? Duk gatan da na miki, sai yanzu na ƙara samun dalilin da yasa yanzu na tsane ki, saboda kin koma bin bokaye da kuma neman maza kamar karya." kakari take idanuwanta sunyi ja sun furfito waje saboda azabar shaƙar da Innar su kamalu ta mata, ba wai ba zata iya ƙwatar kanta a wajen ta bane yasa ta ƙyale ta, a'a so take ta bata damar da za tayi abun da zai sa zuciyarta ta huce a kan jin haushin ta da take, idan akwai wani dalili da zai sa Innar kamalu ta shaƙeta haka ba zai wuce na zugar maƙiyan da suka kewaye ta bane.
_"Kiyi haƙuri da duk abin da zaki gani ko ji a nan gaba Ruƙayya, Allah ya sani ina son ki sosai, hankalinki nutsuwarki da kuma tarbiyyar da iyayen ki suka baki sune suka yi rinjaye a cikin zuciyata na yarda na janyo ki cikin ahali na, a duk cikin ƴaƴa na nafi yarda da nutsuwar Idrisu shi yasa na je na nema masa auren ki, saboda zai yi iya ƙoƙarin sa wajan kula da ke da sauƙe duk wani nauyi da yake kansa, ina roƙon ki da kiyi haƙuri ki toshe kunnuwanki daga sauraran maƙiyan ku."_ kalaman Innar su kamalu a lokacin da aka bada auren ta ga Idris, akwai kusanci mai yawa tsakanin su da ita da soyayyar da take mata kamar ɗiyar cikinta, tabbas komi yana da iyaka amma a wancan lokacin idan akace mata Innar su Kamalu zata mata ƙiyayya kwatan-kwacin wannan to zata ƙaryata hakan, amma sai gashi yau rayuwarta take nema da ɗaukewar numfashi a tare da ita, idanuwanta ne ya fara yin sama alamar zai ɗauke saboda ƙofar numfashin data toshe babu hanyar futa, hannayenta ta saki suka sauƙa ƙasa, ji tayi an fincike Innar Kamalu daga riƙon da ta mata an wullata can gefe ɗaya, ita kuma ta sulale ta durƙusa a wajen tana faman maida numfashi akai-akai, idanuwanta jajir da su saboda azaba.
Ihu ta fara ji yana kaure gidan hakan ya sata ɗago da rinannun idanuwanta cikin mamaki da tsoro taga su tani suna nufar hanyar waje wanda take a garƙame kamar an rufe, ƙara kallon wajan tayi amma bata ga abin da suke yiwa Ihu ba, can ta murtsuka idanuwanta da suka sauya kala zuwa jajaye nan ta fara gani da kyau, ƙara mirtsike idonta tayi dan gaskata abin da take gani *ISMAHA ZAINAB* ce riƙe da sharɓeɓiyar bulala wanda ta ninkata tsayi da girma sai binsu take tana tsula musu hatta Innar su kamalu da take a zaune ta kasa miƙewa daga jifan da aka mata bata tsira ba saida ta shauɗa mata bulalar sau uku, gantsarewa tayi tana ci gaba da ihu.
Tsoro da fargaba ya hana Ruƙayya miƙewa balle tayi magana, dan ji tayi kamar an ɗaure ta a wajan, hatta bakinta yaƙi buɗuwa balle tayi magana, bata ƙara tsorata ba sai da taga ta yi tsalle ta buɗe ƙofar gidan, da hannu ta musu nuni da ƙofa nan suka ruga da gudun tsiya takalman su a hannunsu, dariya ta sa mai ƙarfi tana ɗaga kanta sama, can kuma tayi shuru ta sulale ƙasa ta kwanta.
Da ido Ruƙayya ta bita har yanzu ta kasa tsinana komi sai bugawa da ƙirjinta yake yi da ƙarfi, "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un!, mi hakan yake nufi ?? Mi ya faru da Ismaha Zainab?? Ya Allah kada ka jarrabe ni da abin da yafi ƙarfi na." ta faɗa hawaye na tsere akan fuskarta..🥀🥀🥀🥀🥀
Wayyo da Alama Ismaha Zainab tayi gamo. kuyi haƙuri da ganin yawaitar rubutu na, zan iya baku Read more ɗaya zuwa biyu amma idan yafi haka yawa ana samun gajiyawa wajan gundurar karanta labarin, cmnts naku na ƙaranci, Anty Jidda hop yau ba zaki yi tsallaken pgs ba.#Um Nass
#NWA
#CMNT, LIKE, SHARE
#DA AMANA🤝
![](https://img.wattpad.com/cover/166166065-288-k414201.jpg)
YOU ARE READING
ISMUHA ZAINAB Completed
AdventureAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...