BABI NA 32

575 68 3
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

©by *😘Um Nass 🏇🏼*

_Follow me on wattpad @UmNass_

Page 32

  kallon-kallo suka ci gaba da yi tsakanin su ba tare  da wani ya ƙara tankawa ɗan uwan sa ba.
  "Bakya amsa Sallama ne ƴan mata?" sautin muryar sa ta sake ankarar da ita, da kuma haƙiƙan cewa akan sanin mamallakin muryar.
Kallon sa ta sake yi sai kuma ta samu kanta da jin shakkar sa "Wa alaikumussalam" ta amsa masa sallamar sa, sanan ta fara ƙoƙarin juyawa dan ta shige gida.
  Duk wani motsin da take yana ƙara tuno wasu abubuwa acan baya, duk da sauyawa da shekarun da aka ɗauka amma kuma dole akwai wani abu da yake kyautata zato akan itace.
"Baby Ismuha Zainab" ya faɗa cikin muryar sa mai sanyi, cak ta ja ta tsaya, sai yanzu ta tuna ko waye, duk duniya mutum guda ne ya fara kiranta da haka, bayan shi kuma babu wanda ya sake kiranta da wanan sunan.
Juyowa tayi gaban ta yana luguden faɗuwa, mamaki gami da tsoro duk sun sauƙar mata alokaci ɗaya, bayan tsawon shekarun da aka ɗiba bata sake ganin sa ba, balle labarin sa sai atsakanin kwana biyu da Ya zakar ya kawo mata saƙo daga gareshi, amma kuma abun mamaki gashi yazo yana kiran ta ya ganeta.
  "Wanene kai? Ya akayi ka san suna nah?"

Hannayen sa ya harɗe akan ƙirjin sa yana murmushi, azuciyar sa yana hamdala da tasbihi ga Allah, wanda ya sauƙaƙa masa tarin wahalar neman ta.
"Ai kya bari mu gaisa kafin ki fara jero min tambayoyin ki."
Haushi ne ya kama ta sosai, ji take kamar ta maka masa mari, duk da ta gane shi daga yanda yake magana zuwa kamanninsa da ta sani abaya, sai dai haske da tsayin daya ƙara, muryar sa ta ƙara ƙanƙancewa fiye da abaya, ita har mamaki take ana samun maza da buɗaɗɗiyar murya amma shi tasa ta fiya sanyi da yawa.
  Hannun ta ta harɗe itama akan ƙirjinta tana aika masa da harara "To gaida ni mai muryar yara."

Ido ya waro waje cikin mamaki, kafin kuma ya samu kansa da murmushi, yana nuna kansa yana nuna ta "Ni zan gaida ki ma? Bayan kirana da kikayi da mai muryar yara."
Kai ta gyaɗa masa cikin gundura da magana da shi "Naga kamar kafi son yin gaisuwar ne fiye da abin da ya kawo ka, muryar ka ma tafi ta yara ƙanƙanta saboda su idan sukayi magana akwai ƙarfafawa acikin ta, kai kuma kamar wanda kullum yake rayuwa cikin barci." ta ƙarasa maganar tana cuno baki.

  Tunda ta fara maganar yake kallon ta yana kallo kansa, gashi ta ko ina yafita tsayi, dan tsaf zai ci abinci akan ta yana tsaye nan, amma kuma ko tsoro babu atare da ita take faaɗar magana.
Kai ya girgiza yana ƙara kallon ta "Baki sauya ba har yanzu? Na ɗauka surutun ki da tsokanar ki ya ragu, ashe dai suna nan" murmushi yayi mai sauti ya ƙara matsowa kusa da ita anan ta ɗan matsa baya cikin mamaki da fargabar abin da zai yi, risinawa yayi kusa da ita ta yanda tsayin su ya dai-daita "Jiran da nayi bai wadata ba har yanzu, daga ɗaƙiƙa na fara lissafi har zuwa shekara ina cike da zumuɗi da ɗokin dawowa ganin ki, gashi ina ganin ki na samu tabbacin ke ce, sai dai banbanci kaɗan da aka samu Waccan Ismuha Zainab ɗin tafi ki murmushi mai kyau, ta fiki iya magana mai daɗi, ki tambaye ta saƙona ya risketa awajan yayan ta? Idan ta ce miki eh, ki mata albishir ɗin dawowa ta gare ta, ki kuma bata tabbacin zunzurutun soyayyar da nake mata tun kafin ta san wacece ita, zan kuma dakace ta akan alƙalanci tsakanin mai kyau da marar kyau."
Yana gama faɗar haka ya juya da zummar barin wajan, da sauri ta sha gaban sa tana kallon sa, cikin jin haushin kalaman sa da maganar sa, tsayawa yayi yana kallon ta shima.
"Tabbas saƙon ka ya riske ta akwana biyun da suka wuce, amma daga lokacin da tayi tozali da shi ta tsaneka tun kafin ta tuno kamanin ka."
Da sauri ya dafe ƙirjin sa inda saitin zuciyar sa take buga da ƙarfi jin maganar ta, kallon idon ta yayi yaga tsantsar gaskiyar da take cikin maganar ta.
Murmushi tayi mai sauti wanda da ganin sa najin haushi ne "Ka na mamaki ne?" ta aika masa da tambayar "Ina zuwa." tana ƙarasa maganar ta shiga gidan da ɗan saurin ta, bin ta yayi da kallo har awanan lokacin yana mamakin abin da kunnuwan sa suka jiye masa, bai gama tsinkewa da mamaki ba ya ganta ta sake dawowa hannun sa ta kama ta saka masa ɗan akwatin da ya bawa Zakar ya bata "Wanan shine saƙonka da ya riske ni akwana biyu, na dawo maka da shi saboda bana Son ka, bana son ko wani abu da zai gifta tsakani na da kai wanda zai alaƙanta ni da So! Bana so a soni! Na tsani ko wani namiji da zai ce yana so nah! Na tsani masu ɓata lokuta sun akan kalmar yaudara ta So! Dan Allah ka fita acikin rayuwa tah! Ina girmama ka karka bari na ma tsana ta sosai."
Tun da take maganar ya ke bin idonta da bakin ta da kallo, tsoro da mamaki ne yake kama shi, zuciyar sa kuma sai bugawa take da ƙarfi-ƙarfi, _"mi yake shirin faruwa da ni ne?"_
  Tambayar da yake yima kansa kenan ba tare da ya samu amsar ta ba, ɗago da idonsa yayi yana kallon ta wanda itama kallon sa take bai fahimci irin kallon da take masa ba har ta juya zata koma "Ɗan tsaya dan Allah." tsayawa tayi ba tare da ta juya ta sake kallon sa ba, aranta tana jin ƙunci da ganin halin da yake ciki, sai dai kuma wani sashi na zuciyar ta na jin haushin sa da duk wani namiji musamman wanda zai zo mata da saƙon ina sonki.
"Duk abin da kika faɗa min da gaske ne? Da gaske kike bakya so nah?" muryar sa ta ƙara sanyi sosai.
Juyowa tayi ta kalle shi sanan ta aika masa da harara "Ya wuce wai tunda ga tabbaci nan ahannunka na dawo ma da abin da ka bani tsawon shekaru goma."

Murmushi yayi mai ciwo kana ya ƙara sa kusa da ita, hannun ta ya kama ya ɗora mata sarƙar "Ki riƙeta amatsayin kyauta ba amatsayin abin da saurayi yake bawa budurwar sa ba, shekaru goman da tayi ba atare da ni ba ta sa min sa rai akan samun ki, amma kuma ƙaddara bata bani damar hakan ba, amma har yanzu ban fidda rai akan zan same ki ba, har yanzu zuciya  bata rage wani abu daga soyayyar da nake miki ba, asalima duk abin da kika faɗa ya ƙara min ƙwarfin gwuiwa akan na ci gaba da son ki. Addu'ar da na daɗe inayi na tabbata ba zata faɗi ƙasa ban za ba, har yanzu baki gama sanin wacece ke ba, amma kuma ni nasan komi akanki ciki harda abin da ya hana ki so ni, xanyi yaƙi da shi har sai na tabbatar da zamana Mai Nasara akan sa."
Yana ƙarasa maganar ya juyo da sauri-sauri ya shige motar sa, da matsanancin gudu ya fige ta kamar yanda ransa yake masa zafi da zugi.
 
  Da kallo ta bishi har ya ɓace ma ganinta, hannun ta ta kalla tana bin akwatin da ta bar mata, haka kuma ko wata kalma ta maganar ta na dawo mata sabuwa "Har yanzu ban san wacece Ni ba?" mi hakan ke nufi? Kai ta girgiza ta shige gida.

Ɗaki ta nufa anan ta tadda Luyya tana duba littafin Addu'o'i ahannun ta zama tayi agaban ta kafin wani lokaci hawaye ya zuba ƙasa, wanda ya sauƙa akan ƙafafuwan Luyya, da sauri ta kalli inda hawayen ke xuba Ismaha Zainab taga tana faman zubar hawaye.
  "Subhanallah! Lafiya kike kuka Ismaha?"
Kai ta girgiza mata "Da gaske ne har yanzu ban gama sanin kai na ba Luyya? Har yanzu ban san ko ni Wacece ba?"
  Tun da ta fara maganar gaban ta yake faɗuwa, har ta zo ƙarshe sanan jikin ta ya fara karkarwa "Wa ya faɗa miki haka?"

  Ɗan akwatin ta ɗauko ta fara nuna mata "Wanda ya bani wanan kyautar yanzu muka rabu da shi aƙofar gida, na sanar da shi bana son sa da duk wani abun da zai fito daga gareshi, sai dai hakan bai dame shi ba, asalima ya sanar dani yasan komi dake tare dani wanda ya zama silar ƙiyayyar da nake masa."
Hawayen idon ta ta share ta goge "Da gaske ne akwai wani abun da ban sani ba na rayuwa ta? Wane ne Baba nah da ya haife ni? Ina iyayen ki da ƴan uwanki da duka sauran dangin da zan kira ahali nah?"
  Mutuwar zaune Luyya tayi tun da ta fara maganar take kallon ta, cike da mamaki da tsoro gami da fargabar wata tambayar da zata fito daga bakinta.
Jijjigata Ismuha Zainab take sautin kukan ta na ƙara ƙaruwa "Kinyi shuru Luyyah,  Mi yasa kika gudo kika bar su? Mi yasa tun da kika zo ko bayanki bakya waiwayawa balle ki koma? Ina son sanin wacece ni Luyyah, bakya ga lokaci yayi da ya kamata nasan hakan?"

  Tana gama faɗar maganar ta kwanta tana kuka, hawaye ne ya shiga zuba daga idon Luyyah itama, tabbas ko waye wanan ya ɓallo mata ruwa, lokaci kuma yayi da ya kamata ta waiwayi baya, ta koma gida ta nemi yafiyar iyayenta duk da cewar su suka koreta, amma atsawon shekarun nan komi zai faru ya kamata ta koma ta gan su, ta sauƙe fargaba da nauyin da yake ɗawainiya da ita aƙasan ruhinta.
  Wanan fargabar, wanan damuwar, wannan ruɗaɗɗan al'amarin da ke ɗawainiya da ƴarta ya kamata ya tsaya haka nan.
Nauyi taji Ismaha Zainab ta mata, kafin ta farga ta zube agaban ta, idanuwan ta sun kafe sunyi sama, numfashin ta kuma ya ɗauke.

Ƙara Luyya ta saki da ƙarfin gaske wanda ya janyo hankalin ɗaukacin mutanen gidan suka shigo ɗakin suma, dan ganin mi yake faruwa.

🥀🥀🥀🥀🥀🥀

_Kuyi maleji da wanan, kuyi haƙuri akan jina da kukayi shuru, wasu al'amura ne suka sha kaina, yanzun ma bani da tabbacin ci gaba da kawo muku labarin akai-akai, sai yanda hali yayi dai, ngd_

*GIRMAMAWA*

#ISMUHA ZAINAB
#NWA
#UM NASS
#CMNT, LIKE ND SHARE
#DA AMANA

ISMUHA ZAINAB CompletedWhere stories live. Discover now