40

995 52 4
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

*😘UmNass* 🏇

Last page 40

Hidimar biki sosai ake aduka ɓangarorin guda uku. Kaya na gani na faɗa Musaddiƙ ya haɗama Ismaha Zainab ɗinsa wanda Abbansa ne ya tada matar ƙaninsa suka je suka haɗo masa, sanin cewar Umma bazata ba.
Ahidimar Auren jidda kawai  take sa ran zata baje kolin ta amatsayinta na ɗiya kuma ƙawa agareta.

Tun ana saura mako uku biki Salamatu ta gayyato ƙawarta Asma'u mai gyaran jiki ƴar sokoto tun data zo take faman dirzarsu tun suna mita da maƙalewa har suka saki jiki ganin duk abin da suke abanza.
Tuni fatarsu tayi santsi da sheƙi musamman Ismaha Zainab data bam-bamta da su, kyanta ya ƙara fitowa sosai da sosai. Duk wanda ya kalleta sai ya ƙara juyowa ya kaleta. Atsakanin kuma basa haɗuwa da Musaddiƙ sai waya da suke kusan ƙarar da yini suna yinta, da musayar saƙonni atsakaninsu.

Ahaka har makon bikin ya zo tun daga ranar Juma'a aka fara gudanar da hidimar bikin wanda ta zo amatsayin ranar sakin lallai da kamun hannu ga angwaye, ko wani gefe babanninsu ke hidima awanan ranar.
Ɓangaran Amare ƙawayansu kan ɓoyesu har sai an basu kuɗi sanan su bada asaka musu lallai. Su kuma Angwaye zasu zauna aƙofar gida da abokanansu akan fararen kujeru anan mata zasu samesu afesa ma ango turare wanan shine sakin lallansu.

  Ranar Asabat da misalin ƙarfe 11:30 dubbanin mutane suka sheda ɗaurin Auren Musaddiƙ Adam da amaryarsa Ismaha Zainab Idris sai Zakar Abdullahi da Bilkisu Isah, Mukhtar Bello da Hafsat Isah. Ƙofar gidan Alh. Isah cike yake gam da mutane.

Ranar Musaddiƙ yayi dariya mai tafe da hawayen farin ciki, ashe da gaske kuka yakanzo asigar farin ciki? Tambayar da yakema kansa kenan lokacin da yaji kunnuwansu sun bashi tabbacin Ismaha Zainab ta zama mallakinsa na har Abada.
Rungumar Ma'aruf yayi yana sauƙe ajiyar zuciya akai-akai "Majnun Ismaha zainab" Ma'aruf ya faɗa yana murmushi da bibbiga bayansa.
"Ina tayaka murna abokina Allah ya baku zaman lafiya."
"Ameen" ya faɗa yana goge hawayen da yake zuba akan fuskarsa, sanan sauran abokanansa suka fara zuwa suna masa murna.

  Duk wata hidima da liyafa ta bidi'a ya soketa ya hana, to dama itama ba ra'ayin abin da zai zame mata hayaniya da ciwon kai takeba, ganin haka da yayi sai yasa duka sauran angwayen haɗe kansu suma suka ce ayi walima da wa'azi.
 
Acikin gida kuwa tun lokacin da sukaji an ɗaura aure gaban amaren ya fara faɗuwa, komi na jikinsu ya zama cikin sanyi wani nauyi suke ji sosai yana sauka akansu. Kallon-kallo aka shigayi tsakaninsu.
Ƙara wayar Ismaha Zainab tayi alamun shigowar saƙo acikinta, saurin buɗewa tayi ganin sunan mamallakin saƙon. Murmushi tayi tun kafin ta buɗe wanda hakan yaja hankalin su Hafsat ya dawo kanta.
 
  _"A Yau duniya ta sheda zamanki mallaki nah! Inajin kaina fiye da sarkin dake kan karagar mulkinsa."_
Wani saƙon ne ya sake shigowa tayi saurin buɗewa _"Mutane sukance abin daka samu yana da banbanci da wanda zaka samu agaba, sai dai ni na miƙe ƙafa da sa ran akan kyawawan ranakun da zasu zo min idan ina tare dake."_
  Hannunta tasa tafara ciza yatsanta tana murmushi, zuciyarta na ƙara buɗewa da so da ƙaunar Musaddiƙ ɗinta.
   Dariyar da taji an saka mata yasata ɗagowa, ganin su Hafsat tayi suna nuna ta "Wallahi kin kusa zarewa Ismaha Zainab, gaba ɗaya Musaddiƙ ya maidaki wata kalar Ismaha Zainab daban." Bilkisu ta faɗa tana ƙara dariya.
  Ido kawai ta wara sanan tayi murmushi ba tare data ce komi ba "Miskilancinki akanmu kaɗai yake zuwa, amma idan kina tare da Musaddiƙ sai ki koma kamar aku dan surutu." Hafsat ta faɗa tana aika mata da hararar wasa

  Kai ta gyaɗa tana shimfiɗa murmushi akan fuskarta "To ya ranku yake? Kuma kuyima mazajanku mana, baba muntari da yaZakal."
Duka suka aiko mata cikin haɗuwar hannu da gudunta ta tashi ta fice tabar musu ɗakin tana gwalonsu.
Gidan cike yake da ƴan uwa da abokan arziƙi su Innarmu da Innar su kamalu duk suna nan, harda Tani da Haule matar Idirisu ta yanzu.
Tani kam tuni ta ƙara sanyi ganin daula da arziƙin da Luyya take ciki "Lallai ta ƙara yarda Hassada ga mai rabo taki ce babba. Yau gashi   Ruƙayyar data tsana take cin arziƙinta da kuma alfarmarta, haka kuma aɓangaran Innar kamalu tayi kuka da tayi danasani da neman yafiya daga bakin idrisu da Luyya yafi aƙirga, har sun gaji da yafe mata.
  Ko ina Ismaha Zainab ta gifta mutanen Kwalam suna janta da wasa da tsokana, ta zama tamkar wata tauraruwa acikin su. Ko ina ta gifta takan tafi tabarsu da ƙamshin turaren daya zauna mata ajikinta, haka fulawar da aka zizirama hannunta ta ƙara fito mata da sirrin kyan yatsun hanunta.

ISMUHA ZAINAB CompletedWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu