*🏌♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©BY *😘Um Nass *
🔥®Nagarta WRITERS ASSOCIATION
Babi na Ashirin da ɗaya (Page 21)
Ganin tana qara ɓatawa kanta lokaci yasa ta ɗaga qafa ta nufi wajan siniyo Jummai da kunya ta hanata tashi. Tausayinta ne ya kama Ismaha Zainab ganin yanda halittun Fuskarta ya qara hau-hawa qunshe bakinta tayi tana sunkuyawa dai-dai kanta "Kiyi Haƙuri Anty Jummai" kafin ta qarasa ta kifeta da mari wanda ya sata wuntsulawa tayi baya, sanan ta bita ta ci gaba da dukanta tana boll da ita kamar Allah ne ya aikota, kuka ya gagara fitowa ajikin Ismaha Zainab asalima duk dukan da take mata dunqulewa tayi awaje ɗaya ta cusa kanta ajikin cinyoyinta.
Da sauri siniyon data tura Ismaha Zainab ta shiga tsakaninsu ganin yanda Jummai ke dukanta kamar Allah ne ya aikota."Haba mana Jummai wanan dukan da kike mata ai sai ki kasheta, bakiga sabuwar zuwa bace. Mima ta sani akan rayuwar makarantar idan kin dunqule shekarunta duka nawama yarinyar take?"
Harara Jummai ta aika mata kamar idanuwanta zasu zubo "Ni da za'a barni babu hisabi wallahi kashenta zanyi, ban taɓa jin na tsani mutumba kamar wanan, kigafa irin abin da ta min?" ta faɗa tana duba jikinta da yayi futu-futu, haka fuskarta duk ta ɗaure da zafi.
Dariya ce ta kama Siniyo Shamsiyya ganin yanda Fuskar Jummai ta koma "Uhmm koma dai mi ta miki ke kika janyoma kanki, lokuta da yawa ke kike fara shiga lamarin sabbin zuwa, gashi kin daɗe da sanin cewar yara ne sai da lallami." tana gama faɗar haka ta ɗaga Ismaha Zainab da take dunqule waje ɗaya, abin mamaki da ruɗarwa furr ta kasa ɗagata.
Jijjigata ta farayi amma ko motsawa batayiba balle ta iya ɓam-ɓareta daga haɗa kai da gwuiwar da tayi. A tsorace ta kai kallonta ga Jummai "Na shiga Uku wanan yarinyar kamar dutsefa, taqi motsawa balle ta jinjiga.""Ƴar rainin hankali ce ai" ta qarasa faɗa tana qoqarin hankaɗa Ismaha Zainab, kamar wutar lantarki ta jaka da qarfi hakan ne ya faru ga Jummai lokacin data kai hannuta jikin Ismaha Zainab, kafin tayi wani yunƙuri tayi baya da ƙarfin gaske aka gwarata ajikin bishiyar Mainar da ke wajan "Wayyo Allahna" kalmar data sauqa akan bakinta saboda azabar data sauqar mata alokaci ɗaya.
Kallonta Siniyo Shamsiyya tayi cikin kaɗuwa da al'ajabi kafin tayi magana ta tsinkayi Muryar Ismaha Zainab "Anty mai kyau ki kaini na karɓi shinkafar kazar tunda ta haqura." Furgigi tayi takai kallonta ga Ismaha Zainab wanda take murmushi tana tsotsar hannu abinta, babu wani alamu ajikinta da yake nuna an daketa ko kuma shatin rauni. Kanta ne ya ƙara ɗaurewa tayi hanzarin kai kallonta ga Siniyo Jummai wanda take runtse ido hawaye na zuba cikin jin zugu da azabar da bayanta yake mata.
Bakin magana ta rasa gashi wani tsoro da shakkar Ismaha Zainab ɗin ya dirar mata alokacin, cikin rashin kuzari ta riqe hannunta suka tafi wajan karɓan Abincin. Kwano ta miqa aka bata duk da akwai layi mai yawa amma kasancewarta mai muqamin Shugabar ɗalibai amakarantar yasa bata ɓata lokaciba ta karɓa mata.
Ido Ismaha Zainab ta buɗe waje lokacin da idonta ya sauqa akan Faten masar da ke cikin kwanon. Ruwa ne aciki sosai ita kuma masar ta dawo kamar kwaɓaɓɓan kwaki, sai yakuwa bushasshiya da ganyen Albasa da yake yawo acikinta, hannu ta kai ta lakuta taji hannunta ya nutse ciki.
"Minene wanan ɗin?" ta faɗa cikin furgici da tsoron kaishi cikin bakinta.
Dariya Siniyo Hafsa tayi cikin son ƙular da Yarinyar tace "Wanan shine muke kira da Mandula acikin yarenki kuma Shinkafar kaza" ta qarasa maganar tana tuntsurewa da dariya."Na shiga uku! Yanzu da gaske wanan cinsa akeyi? Nikam idan naci mutuwa zanyi" ta qarasa maganar cikin yanayin tausayi da alhini ashimfiɗe akan Fuskarta, awani sashi kuma na zuciyarta yanaga tsagwaran wautar ɗaliban da suke qoqarin kashe kansu da kokawar bin layi.
YOU ARE READING
ISMUHA ZAINAB Completed
AdventureAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...