*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB💍*
©BY *😘UM NASS🏇*
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
BABI NA GOMA (PAGE 10)
Sosai taji daɗin shawarar da malam Isubun ya bata, dan dama tana son fara yin sana'a gudun kada ƴan kuɗin da take da shi ya ƙare akan hidimar yau da gobe, sai dai batun zuwa Islamiyya ne ta jingineshi gefe ɗaya har saita ƙar-ƙare Iddarta kamar yanda Addinin musulunci ya shara'anta.
Kasuwa taje da kanta ta siyo injin murza taliya ta kuma siyo kayan amfanin da zatayi aiki da su, acikin kwana biyu dayin maganarta da Malam Isubu ta fara yin sana'ar taliya da ɗan-wake duk da kaɗan tayi aranar farko gudun kada tayi jangwaɓo Amma cikin ikon Allah data fita bakin titi tass ta ƙare, haka matan gidan da suke zaune da yawansu sun siya saboda sha'awarta da sukayi, da kuma kashe yunwarsu ta farko kafin su ɗora nasu.
Amma ta zakar daban ta bashi nasa dan ƙin karɓan kuɗin da mamansa ta bashi tayi, idan akwai wanda take jin daɗin zama da ita fiye da kowa agidan to babu shakka Maman Zakar ne da ɗanta, sune wanda suke jure ko wani fitsara ta Ismaha Zainab da rashin kunyarta, haka suke nuna soyayyarsu akanta koda abayan idonta ne.Ahankali kasuwar ta fara buɗe mata tuni sunanta ya sauya daga Ruqayya ya koma Luyyah mai saida Taliya da ɗan-wake saboda jin sunan abakin yaran gidan da suke haya tare, wanda ya samo asali ne daga bakin Ismaha Zainab da suke jin tana kiranta da shi, suma kansu matan gidan bakin yaran suke bi tun suna tsokanarta da maida abin wasa sai gashi ya zauna abakinsu raɗau.
Masu suna Ruqayya dama su biyu ne agidan sai gashi an samu bam-banci da nata, ita kam bata ko damuwa asali tana jin daɗin sunan kasancewar ƴarta ɗaya tilo da take kiranta da shi.*****
Bayan Watanni Shida:Awaɗan nan watanni guda shidan da suka faru an samu sauyi mai yawa acikin Rayuwar Luyya ta yanda ta fara zuwa Islamiyya, kanta ya ƙara waye ta fahimci duk abin da yake faruwa da ita abaya tana da nata sakacin, haka ta duƙufa da karanta Addu'o'i daga Hisnul-muslim (garkuwar ko wani musulmi) haka take fakar Ismaha Zainab ta tofa mata acikin ruwan shanta, tun tana amayarwa ko bakinta ya gimtse yaƙi shiga, har ta yakice ko wani tsoron da yake tare da ita, take mata ɗura, ahankali sai aka samu ɗan sauƙi kaɗan rashin kunyarta ta ragu, amma kuma sai ta samu azababben surutu da tambaya mai gundurarwa ga mutane.
*****
Gudu yake faman shararawa ababban titin dake Matsaro, kasancewar safiya ce hakan ya ƙara masa bawa motar wuta, akai-akai yake buga tsaki yana kallon agogon Azurfar dake saƙale atsintsiyar hannunsa, wanda suke farare tass da su da gargasa ajikinsu, Yarinyar daya hango tana tsalle akan titin ba tare data kula da shiba, yasa yin hon da ƙarfi amma kuma abin haushin ko ajikinta asalima ci gaba tayi da tsallenta tana gwalon wani gefe, wani wawan birki yaja ya tsaya wanda saura ƙiriss motar ta buge yarinyar, tsoro ne ya kamata ta durqushe awajan tana jero ihu "Wayyo ya kashe ni, shikenan la mutu la bar ganin Luyya aa Ya Zakal ɗina" abin da take ta nanatawa kenan tayi kwanciya warwas akan titin, ta runtse ido gam, ita ala dole ta mutu.Takaici ne ya kama na cikin motar hakan ya tilasta masa fitowa acikin motar, tasbihi na fara jerowa axuciyata ganin tsantsar kyan da yake da shi, fari ne tas da shi yana da wadatar magana afuskarsa, wanda ko kaɗan bata buɗewa akai-akai take lumshewa da ƙawatuwar gashin idon da suka taimaka mata wajan futar da kyanta, hancinsa bashi da tsayi sosai amma bazaka kirasu da daƙusassuba asalima sun dace da kewayayyiyar fuskarsa wanda saje ya fara fitowa ajikinta, bakinsa yana da ɗan faɗi kaɗan acikinsa akwai jerarrun fararen haƙora ƙananu dasu sai ushiryar data ƙara musu kyau duk da gajartarsu, bashi da tsayi na sosai amma bazaka ajiyeshi acikin gajerun mutaneba, ta ko ina ya haɗu duk da shekarunsa bazasu haura 18 ba amma tun yanzu kyansa ya fara fitowa, masha Allah itace kalmar dana nanata kenan.
Tunkararta yayi cikin takunsa mai nutsuwa duk da yana cike da haushinta amma hakan bai hanashi tafiya cikin nutsuwaba, tsugunnawa yayi yana kallon yanda take ihu idanuwata arufe tana kiran ta mutu, sanye take cikin kayan makaranta ja mai gidan dara-dara hakan ya fahimtar da shi makarantar dake kusa take zuwa, yarinyace da bazata haura shekara biyarba, amma ganin ihu da birgimar da take ya bashi dariya ainun, ya ɗauko wayansa ƙirar kamfanin LG mai madannai ya fara mata vedio record, sai da ya gaji kana ya maida wayar aljihunsa, ɗaukanta yayi ciɗak ya maidata bakin titi kana ya ɗauko dunƙulalliyar ɗari biyar ya haɗa ajikin hannunta, da sauri ta buɗe idonta tana kallonsa, ganinsa sanye cikin fararen kaya da kuma hasken fatarsa ya ƙara ruɗar da ita ta fara wani kukan "Wayyo sarkin mutuwa agabana" nan ta ƙara runtse idonta tana sabon kukan.
Murmushi yayi mai ɗan sauti yana kallon jikinsa ahankali ya fara magana da muryarsa mai sanyi, wanda idan baka kasa kunne da kyauba ba zaka ji mi yake faɗaba "Ke Baby ban kaɗekiba, nima mutum ne kamarki." Ido ɗaya ta buɗe jin muryarsa kamar ta yara, nan ta tuntsure da dariya kuma har tana riƙe ciki, kana ta nunashi da hannu, nan shima ya fara dudduba jikinsa, ai nan ta ƙara masa dariya, abin sai ya ƙumar da shi ya juya zai tafi, da gudu tasha gabansa tana haki tana nuna shi, tana ƙara yin dariya, haushine ya ƙara kamashi aransa yace "Wanan yarinyar ba mutum bace" ya ƙara raɓawa ta gefenta ya wuce.
"Kai ƙato mai mulyar yara" yaji sautin maganarta nan ya tsaya cak, sai alokacin ya fahimci abin da ya sata dariya, juyawa yayi ya nuna kansa "Ni?" Ya tambaya.
Kai ta gyaɗa masa kana ta matso kusa da shi, ta miƙa masa kuɗin da ya saka mata ahannunta "Luyya tace kal ina kalɓan abu ahannun ƙato, zai yanke min kai" bata jira abin da zaice ba ta buɗe hannunsa ta saka masa, kana ta juya da gudunta "Sai anjima mai mulyar yara" da ido yabita yana murmushi sai da yaga ta shige wani lungu sanan ya faɗa motarsa yajata, shi kaɗai yake tafiya yake murmushi, duk yanda yake sauri saida ya ɓata lokaci gashi har mutane sun fara buɗe shaguna akasuwa.Ahaka ya ƙara yawaita gudun motarsa har sai da ya shiga unguwar G.R.A Acikin wani tamfatsetsan gida ya tsaya yana ƙara yima motarsa hon, da gudu mai gadi ya wangale masa ƙofar ya shiga, hannu ya ɗaga masa yana masa barka da zuwa mai gida, shima kai ya ɗaga gami da miqo masa hannu ta jikin window motar, wajan adana motoci yakai motar tasa wanda ko kaɗan bata kama sauran motocin da suke gidan kyau da tsaruwaba, ajiyeta yayi kana ya fito ya nufi ɓangaran da zai sadashi da palon gidan, kamar yanda yayi tsammani mutanen gidan basu tashiba sai masu aiki da suke kai-kawo apalon.
"Barka da safiya Yallaɓai" sautin mai aikinsu ya daki kunnensa, ɗago da limsassun idanuwansa yayi ya kalleta kana ya gƴaɗa mata kai, anan ya fara daddana wayarsa ba tare da yayi maganaba.
Agogon dake hannunsa ya sake dubawa ganin har 8:30am yasashi miƙewa ya nufi kitchen ɗin dake palon, wata er dattijuwa ce take kai kawo anan tana faman juye kayan karin data shirya.
Gyaran murya yayi wanda ya ankarar da ita da zuwansa kitchen ɗin, baki ta washe tana ɗan risinawa "Uban ɗakina har ka fito ashe?"
Kai ya gyaɗa mata kawai yana dube-dube, da sauri ta ɗako kofi ta haɗa masa tea ta miƙa masa "Nasan wanan kake buqata, ko ahaɗa maka da soyayyan dankali?"Kai ya girgiza "Nagode Baba" abin daya faɗa kenan ya koma palon ya zauna, da ido tabishi tana murmushi "Uban ɗakina kenan. Shi dai abinci bai dameshiba ko kaɗan" sanan taci gaba da aikinta, ta fito ta jere akan daining table ɗin dake gefen palon, har lokacin yana zaune yana kurɓan shayin.
"A'a Musaddiq ka dawo dama? Shine baka shiga ka sanar daniba kake zaune apalo" Muryar wani dattijo ta ratso kunnensa, ahankali ya ɗago ya kai kallon ga mahaifin nasa, sanan ya risina ya fara gaida shi "Barka da safiya Abba, Mun tashi lafiya?"
Zama yayi akan kujerar yana fuskantar ɗan nasa cike da soyayya "Alhmdlh lafiya lau Musaddiq, ban san ka dawoba ina ta jiranka ashe kai kana nan palo azaune?"
Kai ya gyaɗa "Eh ban jima da dawowaba ai?"
"To ya batun tafiyar taka?"
Kai ya juyar da gani baya son tafiyar ahankali yayi magana "Mako mai zuwa In sha Allah komi xai kammala."
Dafa kafaɗarsa yayi cikin sigar lallashi "Allah ya kaimu, ka kwantar da hankalinka kaji, in sha Allah lafiya zaka je ka dawo ka samemu, fatanmu dai ka samu ci gaba akan komi."
"Amma Abba ni bana son barin ƙasata, bana son yin nisa daku, ananma zan iya yin karatuna ba sai nabar jahata da ƙasataba."Murmushi yayi kafin yayi magana ya tsinkayi muryar Mahaifiyarsa "Kabar Rarrashinsa Alhaji koda baya so dole ya rabu damu, ana nuna masa gata da soyayya amma shi yana dojewa, muma ai muna son iyayenmu muka rabu da su."
Atare suka juya suka kai kallonsa gareta fuskarta murtuk babu fara'a.
🥀🥀🥀🥀
#Um Nass
#NWA
#CMNT, LIKE AND SHARE.
#DA AMANA
VOCÊ ESTÁ LENDO
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...