BABI NA ƊAYA

978 59 2
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

©by *😘Um Nass 🏇🏼*

® *NAGARTA WRI.ASSOCIATION*

بسم الله الرحمن الرحيم

*_Alhmdulillah, Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.A) mai kowa mai komi wanda ya yarde mana cikin ikon sa da rahmar sa muka sake kasantuwa a tare, ina roƙon Allah ya bani ikon  kammala wannan labarin cikin sa'a da nasara mai yawa._*

_Haƙiƙa godiya ta tana da yawa ga dubun masoya na a yayin da na ga kuna farin ciki da murna a lokacin da kuka yi karo da SHINFIƊAR labarin nan, sosai nake farin ciki kuma nake yinku Allah ya bar ƙauna Son So FISABILILLAH_

  TSOKACI:
*DUK abin da za ku gani  a cikin wannan labarin mai daɗi ko aƙasin sa tofa ƙirƙira ne ba wai da gaske bane, idan kuma a kayi katari da samun wani abu da yayi kamancecciniya da rayuwar wani to yayi haƙuri ba da sani na hakan ta kasance ba, idan kuma kuka yi karo da wani kuskure a cikinsa, ina roƙonku da ku ankarar dani a kan lokaci cikin Kamala ba da cin Fuska ba 👏🏻*

BABI NA ƊAYA

*Ƙauyen Kwalam*

Ƙaramin gari ne, ɗaya daga cikin ƙauyukan Ringim, wanda idan aka cureshi a wani garin ba zai wuce girman unguwa guda ɗaya ba, mutanen garin sun kasance abu guda, ma'ana kusan ahali guda ne da suka fara rayuwarsu a cikin ƙauyen, ƙalilan ne a cikin su baƙi wanda suka zo dan su zauna, abu guda mai muhimmanci idan ka kalle su zaka ga tsago guda akan kumatunsu, kamar na mahauta amma ko kaɗan basu da alaƙa da su, sai dan hakan ya zama al'ada a gare su ne yin tsago a fuskarsu, wanan kenan.

Ƙofar gidan cike yake taf da mutane, wasu suna tsaye a yayinda wasun su suke zaune. Daga cikin gidan kuma wata mata ce a zaune da lilliɓin mayafi a kanta, tana zaune a kan kujerar tsugunno, gabanta kuma bahuna ne da fanteka na taliya da ɗan wake, tana zubawa wasu, tana karɓan kuɗin wasu, da alama sana'arta ce hakan, duk da aƙallah ba zata wuce shekaru ashirin da ɗaya ba, amma yanayin rayuwa da wahalar aikin da take zai nuna ta kai shekaru talatin a duniya, tana da kazarniya da fara'a wajan bawa ko wani mutum Haƙƙin sa.
Cikin abun da bai wuce awa guda ba abincin ya ƙare sai aka samu sauƙin mutanen, duk da wasu suna zuwa ana ce musu ya ƙare, haka suke komawa gida cike da jimami da takaici, dan duk garin abincin ta ne mai rahma da kuma daɗi, matsala ɗaya idan baka yi sammako ba baka samun sa, kasancewar su mutanen ƙauye ne da yawan su ɗumame ke jiran su a gida dama kuma abincin nata ya kasance na matasa ne masu karkaɗe jiki da nuna su sun wuce cin tuwo (Lolx).

Tashi tayi ta tattara kwanukan da aka ɓata ta fara haɗa su waje ɗaya tana wanke su, kafin ƙarfe goma gidan na ta yayi tsaf kamar ba a ɓata shiba, ɗaki ta shiga ta tadda ƙaramar yarinyar ta wanda ba zata wuce shekara uku ba tana barci hannunta a bakinta tana tsotsa, shafa kanta tayi tana murmushi gami da sauƙe ajiyar zuciya, kamar mai jira ta buɗe idanuwanta tarai a kan Mahaifiyar ta, baki ta wangale sannan ta mirgino jikinta ta ɗora kanta a kan cinyar mahaifiyar tata "Luyyah", ta faɗa tana shafo Fuskar mahaifiyar tata, itama murmushi tayi ta shafa Fuskarta "Kin tashi?", kai ta ɗaga mata tana dariya, miƙewa tayi da ita ta fito waje ta surka ruwan sanyi dana ɗumi ta mata wanka sannan ta goyota suka koma ɗakin ta shirya ta tsaf cikin doguwar rigar atamfa da ɗankwalin ta, masha Allah yarinyar tayi kyau mutuƙa, duk da kasancewar ta baƙa ce amma ba baƙin wuluk ɗin nan b, sai magana dara-dara da gashin saman ido wanda yake da yawaita musamman idan ta rufe idon, sai hancinta wanda bashi da yawaitar tsayi amma ya taimaka wajan dai-daituwa a kan fuskar tata mai ɗan faɗi, bakinta ɗan mutsugul kamar loma ba zata shige ta ba, gefen fuskarta kuma akwai kwantattun gashi wanda yake nuna cewar tana da gashi, kanta a kitse yake da kitson shuku wanda saida aka tufkesu  aka duƙunƙune saboda yawan su, akan Fuskarta akwai ɗan siririyin tsage a kumatunta na dama hakan ya ƙara fito da kyanta.
"Masha Allah, Yarinya ta kin yi kyau", ta faɗa tana murmushi itama baki ta wangale tana dariya sai juyawa take, can kuma ta ɗano bakinta ta fara shafa cikinta "Luyyah Abinci", ta ƙarasa faɗa kamar mai shirin yin kuka.
"zo muje kici abincin kar kiyi kuka." da murnarta ta fice wajen da gudu bin ta tayi tana murmushi "Oh Ismaha Zainab sarkin ci", kai tsaye kitchen ta shiga ta taddata tana kalle-kalle kwano ta ɗauko ta ruƙo Hannunta suka fito barandar da ke tsakar gidan, tabarma ta shimfiɗa musu suka zauna kana ta buɗe abincin Taliya ce da tumatur yayyanke a kanta sai gefe kuma yaji ne a ɗan ƙaramin kwano, dariya Ismaha Zainab ta fara yi tana tafa hannunta "Taliya", hakan yasa Luyyah yin dariya sanan ta ce "Oya kice Bismillahi sai ki fara ci."
"Bicmillah", tace tana kaɗe hannunta duk da ba wai ci gareta mai yawa ba amma idan kaga yanda ta dage tana walwala da ɗai sai kace duka zata ci, bata kai ga kammala ciba ta tsinkayi sallama, sai da gabanta ya faɗi gane muryar mai sallamar, ba kowa bace face Tani Matar yayan mijinta.
"Wa alaikumussalam, maraba da Yaya Tani",  ta faɗa tana taro ta da dariyar da take ta yaƙe, kallon sama da ƙasa ta mata sannan ta kwaɓe baki "Ahh lallai ba shakka, Hajiya Ruƙayya baki da matsala ke kam kin tada kai da sulalla ga gardawa suna shawagi a kowata safiya ta duniya, bawan Allah Idrisu ana can neman halaliya bai kuma san wainar da a ke toya masa a gida ba."
Ɗago kanta ta yi tana kallon Tani ɗin, wannan ba shine karo na farko da ta saba mata haka ba, bata san mi ta tsone mata a rayuwa ba gashi har ta kai matakin da ko uwar mijin su yanzu ta tsane ta bayan kuma a baya itace take sonta kamar ranta ƙarshe ita ta zama sila na ƙulluwar auren ta da Idris ɗin. Kafin ta farga ta sake wata magana Tani ta janye kwanon Taliyar da yake gaban Ismaha Zainab ta fara kai loma bakinta "Tunda ba'a mana tayi ba mukam ai zamuci ko ran mutum baya so, iyaka dai a mana Allah ya isa ita kuma yanzu ta zama riga a jikin kowa."
"Haba dai yaya Tani ai kin girmi na miki Allah ya isa, inama abin yake?", ta faɗa tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi, baki ta ƙara taɓewa "Ke kika sani da kinibibin ki." Tass ta gama cinyewa ta suɗe hannunta sannan ta ɗauko leda ta juyo yajin "Wanan yajin zan tafi dashi gida dama yau wara da Mai zanyi." daga haka ta kakkaɗe jikinta, "Innarsu Kamalu ce ta aiko na kira ki idan kina da lokacin ta, dan gama yanzu baki da lokacin mata sai ƙatti masu cin riba biyu."

"Zanje Yaya, jira ni mu tafi tare." ta faɗa da idanuwanta da suke shirin zubar da hawaye gabanta naci gaba da luguden faɗuwa, tasan ƙila wani faɗan ne yake jiran ta a gaba, kiran surukar ta babu alkhairi ko kaɗan a cikinsa, dan ma ta auna arziƙi da bata tako da kanta tazo ta same taba.
Ɗaki ta shiga ta ɗauko Hijabi sannan ta ruƙo Hannun Ismaha Zainab suka nufi waje bayan ta kulle ɗakin ta da ƙofar gidan, sannan ta cewa Tani da take faman doka mata harara "muje Yaya". Bai wuce gidaje shida bane tsakanin su ko ina ta gifta sai kaji yara da matasa na kiranta suna gaida ta cikin walwala, wasu kuma su kira Ismaha Zainab dan yarinyar akwai shiga rai da dariya, hakan ya ƙara ƙular da Tani sosai gashi dai su biyu suke tafe amma dan wulaƙanci babu mai kiran ta sai dai su kira wata Ruƙayya, ƙwafa tayi ta ƙara jijjiga kai, ƙarshe ta ƙara sauri ta tafi ta bar Ruƙayya da take gaisawa da wani "Innar Ismaha yau na makara ban samu abinci ba."
"Ai kuwa Muntari yau kam kayi barci da yawa, ka ci ɗumame ai." ta faɗa tana dariya dan tasan ba abinda ya tsana kamar tuwo, kai ya girgiza yana ɓata fuska "Allah ya tsare ni da cin ɗumame yana sabon sama ban ci ba balle kuma da ya kwana."
Dariya tayi "To ai ɗumamen yafi daɗi."
Kai ya girgiza yace' "Allah ya tsare ni dai da cin sa, ina zaku je ne haka naga kamar kuna sauri?" Yayi saurin sauya hirar.

"Wallahi nan zamu je gidan su Baban Zainab Innar sa ta aiko kirana."
Kai ya gyaɗa yana tambayarta "Lafiya dai ko?", kai ta girgiza "Ban dai sani ba sai naje, kaga abokiyar tafiyar tawa ma ta wuce ta barni", ta faɗa lokacin da ta ankare da ɓacewar Tani.
Alawa ya ɗauko a cikin Aljihun sa ya miƙawa Ismaha Zainab, "gashi amaryass wannan na toshi ne, duk da baki ajiye min abincin kari na ba, ku isa lafiya", ya faɗa yana yin murmushi gami da juyawa da muryarta da bata fita tace' "na gode kuma na cinye yanzu duka", dariya suka yi dukan su har da Muntari yayi gaba abinsa yana ɗaga musu hannu, matashi ne ɗan shekara sha bakwai, haka yake tsokanar Ismaha Zainab da sunan amaryar sa wai yana sonta.

Sai a lokacin hankalinta ya dawo kanta samu tayi gabanta na ci gaba da faɗuwa tuna tsawon lokacin da ta ɓata, hakan ya sata ƙara sauri, cikin sanyin Murya ta yi sallama sai dai ga mamakin ta babu wanda ya kulata a cikin mutane huɗun da suke zaune. Jikinta ne ya yi sanyi kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki, haka ta ƙarasa ta samu waje ta tsugunna "Innah ina kwana", kai ta juyar gefe ba tare data amsa mata ba, sake gaida ta ta sake yi, cikin hargowa ta juyo tana kwatsa mata tsawa "an faɗa miki ban jiki bane, ko kuma kin ɗauka ni kurma ce kamar mahaifin ki wanda baya ji sai an ƙwala masa murya?". Da sauri ta ɗago tana kallon ta kai ta gyaɗa mata cikin ƙara murtuke fuska "duk abin da kike yana dawowa yana samu na, kin maida gidan ɗana dabdalar tara ƙartai da zuwan kina siyar da abinci, sam ba zan lamunci wanan abin ba, idan shi Idirisun kun shanye shi to fa ni a tsaye nake, dan haka cikin biyu dole ayi ɗaya ko ki haƙura da sana'ar ki ko kuma ki haƙura da aurenki." ido ta ɗago wanda tuni hawaye ya cika su "amma Innah shi ma Idris ɗin ai yasan ina sai da abincin, asali ma da shawarar sa na fara siyarwa, kuma duk wanda yace maza na cika min gida to maƙaryaci ne dan babu masu shiga gida na sai yara ƙanana."
Hannu Tani ta tafa tana salati "wato mu ne maƙarya tan naki kenan? Idan gardawa basa shiga gidan ki taya suka san kamanninki? Tunda muka doso layin nan ake faman kiran sunan ki kuma duk cikin su babu yaran, ƙarshe ina tahowa nayi na bar ki?", ta ƙarasa maganar tana hararar ta, ƙarfin hali Ruƙayya tayi saboda yanzu kam an kawo ta gejin inda ba zata jure ba "Tunda haifa ta a kayi a garin ba taka haye bace ai dole su san suna na, kuma dole idan an gaida ni na amsa saboda an girmama ni."
Azabure Tani ta miƙe tana nuna ta da hannu "akul ɗin ki Ruƙayya, kada ki faɗa min babu daɗi, kinsan koda nake ba ƴar gari ba ai ina da dangi anan ɗin, balle ki faɗa min magana."
"Ni dai ban ce ke ba, idan ma kinji haushi to ke kika so kiji."
"Da kyau Ruƙayya ashe rashin kunyar da ake faɗa min taki ta wuce yanda nake tunani, a gabana yau kike musayar magana dani, zan ɗauki mataki idan shi Idrisu ɗin ne yace kina min rashin kunya zan kawo ƙarshen abun, kuma dole ki taƙaita tara gardawa a ƙofar gidan ki idan ba haka ba to sai dai ki san inda dare ya miki, wama ya sani ko kina rage dare da su ɗinne?".
Kai ta sunne ƙasa tana riƙe hannun Ismaha Zainab wanda ta lafe a jikinta, ji tayi an finciki yarinyar "zo nan uwar ƙiwa baki san ki gaida mutane ba, to nice dolen ki da ko kallo ban ishe kiba ja'irar yarinya." Innar su Kamalu ta faɗa, kuka Ismaha Zainab ta ƙwala wanda yasa su toshe kunnuwansu, bakinta ta yi saurin bugewa hakan yasa jini zuba saboda haɗuwar da yayi da haƙoranta, wani rikitaccen ihu ta ƙara callarawa saboda zafin da taji, sosai kukan ke taɓa Ruƙayya amma bata da damar yin magana, hakan ya sa ta miƙewa tsaye "Innah ni zan koma gida."
"Saboda an taɓa ƴar ki tana kuka shine zaki ce zaki tafi? To ki gayas amma yau a nan zata wuni, dan ko taƙi bata da kamar ni." kai ta girgiza bata ƙara magana ba ta musu sallama tana jin Ismaha Zainab na callara kuka tana kiran sunanta "Luyyah", amma bata tsaya ba sai sauri data ƙara ta fuce ta bar gidan..

🥀🥀🥀🥀
#UM NASS
#NWA
#Cmnts nd vote
#DA AMANA

ISMUHA ZAINAB CompletedWhere stories live. Discover now