BABI NA 13

358 44 1
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

©BY 😘Um Nass🏇

®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

BABI NA SHA UKU (page 13)

  Kallon ɗakin taci gaba dayi tana nazarin rayuwar da zasuyi da Alh. Isah bayan ada ta sakankance akan ta haƙura da sake sabuwar rayuwar Aure, duka maza abu guda ta ɗaukesu masu son kansu, marasa adalci da tausayi ga matansu.

Motsin shigowar Alh. Isah ne ya ankarar da ita daga dogon tunanin data shiga, lokacin da sukayi ido biyu saida gabanta ya faɗi da ƙarfin gaske, ba zata iya misalta abun da taji agame dashiba, sai dai ta hango tsantsar walwalar da take ɗawainiya da shi alokacin daya shigo bakinsa awashe, wanan ya bata nutsuwa kaɗan aƙasan zuciyarta amma bata kawo hakan mai ɗorewaba.

"Amarya kinsha ƙamshi." kalmar daya faɗa yana ƙarema ɗakin kallo kenan har ya diresu akanta, kai ta sunkuyar saboda sabuwar kunyarsa da ta sauƙa aƙasan ranta.
  "Ɗiyata tayi barci har haka" ya faɗa yana shafa kan Ismaha Zainab data bararraje tana sauƙe numfashi.
  Miƙewa yayi tsaye yana karkaɗe babbar rigarsa "Ki mata shimfiɗa sai kixo muje ɗakina, bari na zo." yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin.

Da ido tabishi aranta tana tunanin yadda zasu raba shimfiɗa da ɗiyarta, amma kuma idan ta tuna girman haƙƙin miji akan matarsa sai taga wanan ba komi bane, arayuwar da tayi awanan garin ta koyi abubuwa da yawa dangane da Addininta ko anan ta godewa Allah dayasa alkhairi acikin barinta garinsu.

Miƙewa tayi ta gyarama ismaha Zainab shimfiɗarta kana ta tofeta da Addu'ar kariya.

Cikin nutsuwa ta gyara zamanta aɗakin tana kallon yanda Ismaha Zainab take sauƙe numfashi hakan ya bata tabbacin tana jin daɗin barcin da takeyi.

"Yauwa kin gama komi?" Alh. Isah ya faɗa yana shigowa ɗakin.

"eh na gama"

"To taso muje gasu Salamatu can na tarasu."

Miƙewa tayi tabi bayansa ba tare da tayi maganaba har suka shiga ɗakinsa. Azaune tagansu dukkaninsu ɗibga-ɗibga dasu kamar da aka hura musu iskar taya, ido suka zubo mata wanda yasata faɗuwar gaba dan ba kyakkyawan kallo suke mataba, asalima kallo ne da yake nuna tsantsar tsanar da suka mata, zama tayi anesa dasu take fuskantar Alh. Isah.

Gyaran murya yayi cikin muryarsa mai Amo ya fara magana "Abin dayasa na taraku anan ba dogon abu zan faɗa mukuba, wanan da kuke gani itama matace kamar ku, sanan bana son tashin hankali acikin gidana, dan bazaku takura min ku shiga rayuwataba bayan na wadataku da duk wani abu najin daɗi." sanan ya juya ga Ruqayya ya nunata da hannunsa "Kece baƙuwa Ruqayya waɗan nan duk yayyanki ne, bana son wani abu na tashin hankali yabiyo baya, abu mafi muhimmanci bana haɗa soyayyar ƴaƴana data kowa, dan haka ki kula da kyau kada ki shiga abin da bai shafekiba, wanda ba zakiji daɗin sa ba." daga haka ya janyo leda mai zanen zabira ya miƙa musu "Gashi gasasshiyan nama ne akwai ƙaramin ɗauri da babba, ƙaramin shine naku babban kuma na yarana, bana son ku musauya musu." karɓa sukayi suka hura hanci da harare-harare, wanda bai san sunayiba, da ƙyar sukayi ɗaga luta-lutan jikinsu suka tashi.

Da ido Luyya ta bisu cikin mamaki daya daskarar da ita, yau kuma wata ƙaddarar ce ta wuntsulota wanan gidan, da alamu mijinsu bai san komi akan sha'anin aureba, bayan ci da sha da sutura sauran al'amuran ko oho.

Wata ledar ya janyo ya buɗeta namane shima gasasshe da ɗuminsa sai albasa da aka yayyanka, ɗaya ledar kuma lemon kwalba ne guda biyu, hannu ya fara murzawa yana washe baki "To Amarya matso muci kinji."

Kai ta girgiza ba tare datayi maganaba dan ta cika da mamakinsa sosai da sosai, bai jira taci ko karta ciba ya fara yagar naman yana korawa da ruwan lemo hankalinsa kwance, bai ƙara mata tayiba har saida ya cinye fiye da rabin naman kana ya saki gyatsa "gashi nan idan kina iya ci sai kici, nikam barci nakeji."

Daga haka ya ƙarasa shiga ɗakin, kanta ne ya kulle ta fara tunanin, mi yake faruwa ne da ita,, bata da wanan amsar kafin kuma ta lalimo abin da zatayi tunani akai ta tsinkayi kiransa daga cikin ɗakin, wanda ya sata miƙewa tabi bayansa cike da faɗuwar gaba.

******
Washe gari ta riga kowa dake gidan tashi ta shirya tsaff ta yima Ismaha Zainab shirin zuwa makaranta, sai faman tambayarta take "Luyya yau asabon gida muka kwana? dakinki yayi cau? Kullum agado zan kwana? Amma kuma ina yazakal ɗin?" Kai Luyya ta ɗafe tana kallon Ismaha da bata gajiya da magana.

  "Wacce kike so na Amsa miki aciki?"
"Duu" ta faɗa tana dariya, kai ta girgiza cikin murmushi kafin tayi magana aka hankaɗe labilen ɗakin ba tare da anyi sallamaba matashin saurayi ne ya wurga musu harara "Ki fito malama ki ɗora mana abinci muna jin yunwa kada ta hallakamu, kun cikama mutane gida da surutu sassafe ke da wanan jarababbiyar ƴar taki."
Cikin mamakin rashin tarbiyyarsa Luyya take kallonsa yanda yake magana baya ko jinkirtawa balle yasha numfashi, kafin tayi magana ta tsinkayi muryar Ismaha Zainab "Ai dai bani bace jalababba ba ce kai."

Afusace ya shigo ɗakin ya bige mata bakin nan take jini ya fito wani ihu tasa mai ƙarfi wanda yaja Luyya runtse idonta "Na ƙara ji kinyi magana saina karyaki." ya faɗa yana ficewa aɗakin "Anyi din mugu accaluma."
Tana kuka tana maganar bai juyoba sai waje da yayi abinsa, kallon LUyya tayi datake ƙoƙarin fita aɗakin.

"Luyya Ni bana con nan gidan, mu koma gun yazakal"

Bata sauraretaba ta fice ta barta ai nan ta fito tana ihu da birgima wanda saida ya tada mutanen gidan gaba ɗaya, dama yaransu sai sunga dama suke zuwa makaranta dan ba'a tsawatar musu.
"Kai yau mun haɗu da jaraba sassafe ahanamu barci, uban mi za'a mata ne?" taji Muryar Salamatu uwar gida cikin kaushin murya da alama ko sallah batayiba dan fuskarta alamun barci ne ajikinta, kallonta Ismaha Zainab tayi, sai kuma tabar kukan ta fara tuntsirewa da dariya tana nunata, hakan yasa salamatu kallon jikinta tana son ganin abin da takema dariya, amma bataga komiba,  sanye take da ɗaurin ƙirji sai gashinta daya miƙe atsaye kamar an mata shuka ahakan wai kalba aka mata.

"Uban mi kikema dariya ajikina?" ta faɗa cikin faɗa tana harararta..
Aifa nan ta ƙara tuntsirewa da dariya dai-dai fitowar matasan gidan da Alh. Isah "Luyya kallo tuleliya da ita babu liga, gashinta kamal na goluba, kiga ya'un balci abakinta ya buɗe." nan ta sake fashewa da dariya,  nan kuma mutanen wajan suka fara kallonta suma suka tuntsire da dariya harda Alh. Isah da yake ƙoƙarin fitowa, yi suke suna duƙawa, hakan ya fusata Salamatu ta iyo kan Ismaha Zainab gadan-gadan zata daketa.....

🥀🥀🥀🥀
😂😂😂caiii..

#Um Nass
#NWA
#CMNTS, LIƘE ND SHARE
#DA AMANA

ISMUHA ZAINAB CompletedWhere stories live. Discover now