*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
*😘Um Nass 🏇*
Page 37
Ƙarasowa kusa da ita yayi yana murmushi, duka mutanen wajan kallonsa suke cikin rashin fahimtar waye, idan aka ɗauke Idirisu da yake jin ya ƙasƙanta agabansu, wataƙila da babu haƙƙinsu akansa da shine yake da matsayi da ɗaukaka irin tasu.
Risinawa yayi har ƙasa ya gaidasu, da murmushi akan fuskarsu duka suka amsa cikin haɗuwar baki.
"Muntari kaine ka zama haka?" Luyya ta faɗa tana murmushi, kai ya sosa cikin sigar jin kunyarsu.
"Na samu labarin zuwanku ne ai awajan Bura, shine na taho ina ta Allah-Allah na sameku, ashe da banzo akan lokaciba da kun tafi.""Allah sarki, ai ni ina nan har kwana biyu, Mai gidana ne zai koma yau." ta ƙarasa maganar tana nuna shi da hannunta, juyawa yayi ya kalli Alh. Isah ya sake gaidashi cikin girmamawa.
Sosai Alh. Isah ya yaba da hankalin yaron "Mukhtar ya Iyalin?"Kai ya sosa yana murmushi "Har yanzu babu Iyali Alhaji, ku tayamu da Addu'a dai."
Kai ya gyaɗa yana murmushi "To Allah ya kawo nagari, amma dai kayi ƙoƙari kada ka mai-maita shekara kana gwauro" dariya suka saka masa ganin yanda yake ƙara sunkuyar da kansa yana sosa ƙeya.
Agogo Alh. Isah ya kalla sanan ya sake yi musu sallama akan zasu tafi, fatan Alkhairi da sauƙa lafiya suka musu, Babuji da Innarmu na ƙara miƙa musu godiya.Sai da sukaga ɓacewarsu sanan suka koma cikin gida. Anan suka bar su Idirisu suma suka kama hanyar nasu gidan, cikin jin kunya da dana-sani mai yawa.
Shigarsu gida aka zubama Muntari abinci, sai da yaci yasha ruwa, ya rage daga shi sai Luyya aka sake sabuwar gaisawa kana Luyya ta kalli Muntari "Bani labarinka Muntari bayan rabuwarmu, dan naga sauyi sosai ayanayin ka.
Murmushi yayi sanan ya girgiza kansa "Abun da ya faru aranar nan ya zame min mafari na ƙunci da zubar hawaye agareni, musamman dana zama Sila na wargaza miki dukkanin farin cikin ki, da duk wata alfarmar da kike da ita agarin nan. Lokacin dana samu labarin korarki da Babuji yayi, nayi kuka, kuka na sosai. Ƙarshe nima zaman garin nan gagarata yayi, saboda kallon da mutanen garin nan suke min, lokuta da dama sukan aibatani da tsiniwa agareni, hakan yasa na tattara kayana nabar garin nan, bayan mun siyar da gonarmu ta gado Innata ta haɗa min da kuɗin dake hannunta, muna kuka muka rabu. Ban tsaya ako inaba sai a Zakirai anan na yada Zango, kinsan lamari na Allah da nayi kwana biyu agarin, naga yanda mutanen garin suke tafiyar da mu'amularsu cikin amana da gaskiya kawai sai naji garama na Zauna agarin yafi min kwanciyar hankali, da ɗan kuɗin da yake hannuna na kama hayar shago akasuwar garin, na shiga cikin Kano na fara sarar kayayyakin sawa daga yadika na maza zuwa atamfa mai sauƙin kuɗi. Cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya sanya albarka akasuwancin nawa, ƙarshe shagon da nake haya na siyeshi ya zama nawa, ganin damar dana samu sai na koma karatun boko har na samu matsayin digri afannin kasuwanci, Alhamdulillah hakan da nayi sai ya ƙara taimaka min awajan sana'ata yanzu kaf garin Zakirai zance babu mai shaguna kamar ni. Acikin shekarun nakan zo garin nan cikin dare dan ganin Innata da tambayar ko ansamu labari akanki, amsa ɗaya nake samu akan har yanzu babu labarinki. Ko kwana bana ƙarayi nake tattarawa na koma, saboda jin tsoron abin da zai-je-ya-zo idan mutanen garin nan suka ganni, ƙarshe na samu labari gaskiya ta fito, har baban Ismaha Zainab yaje gidanmu neman yafiyata, hakan yasa na fara sakin jiki nake shigowa akai-akai ganin mahaifiyata."
Numfashi Luyya ta sauƙe bayan gama sauraron maganar da Muntari "Masha Allah, amma duk da irin wanan cigaba da nasarar da ka samu ka gagara ajiye iyali?"
Kai ya gyaɗa cikin yanayin alhini da takaici ya fara magana "Ina naga wanan lokacin da nutsuwar, kullum ina cikin bada cikiya da bin gari-gari wajan nemanki, gani nake kamar ni nake da duk wani alhaki na tarwatsuwar farin cikinki da barin gidan auranki. Hakan yasa bani da lokacin ɓatawa wajan sauraran ƴan mata. Sannan kuma.... Ummm.. Ummm" ya kasa faɗar maganar tasa yana faman sosa ƙeyarsa alamun nauyi da jin kunya da maganar tasa ta masa.
Murmushi Luyya tayi tana jinjina lamarin Muntari da kuma kawaici irin nasa "Sanan kuma mi? Wanan ba hujja bace da zata hanaka yin aure Muntari, ko ka manta lamari na Allah da yakan sauya al'amuransa ta hanyar aiko da ƙaddara ga bayinsa mai kyau ko marar kyau dan ya gwada imaninsu, ka cire cewar kai ne kake da alhaki akan rabuwar aurenmu da Idris, dama can iya wa'adin zaman da aka ɗibar mana kenan muyi arayuwa, abu na gaba naji daɗin yanda ka samu sauyi da ci gaba acikin rayuwarka, amma kuma banji daɗin jinkirin da kayiba wajan ƙin ajiye iyali ba, ƙila da yanzu ka samar min da takwara." ta ƙarasa maganar cikin salon tsokana wanda ya sashi dariya shima.
"Ai kin min alƙawalin aura min Ismaha Zainab ne. Wanan dalilin yasani jiran tsammanin ganinku, na kuma ƙudurce araina muddum ban gankuba babuni babu aure."
Ido Luyya ta fiddo waje cikin mamakin maganar tasa, kafin kuma ta ƙaƙalo murmushi "Wasa kake Muntari, bayan lokacin duka batafi shekara uku aduniya ba."
Kai ya gyaɗa fuskarsa babu alamun wasa "Ta iyu alokacin ke wasa kika ɗauka, amma ni har azuciyata da gaske na riƙe alƙawarin, ina kuma Addu'a da roƙon Allah ya bayyana min ku idan ina da rabon yin aure aduniya, dan nasan muddum ban sameku ba, babu ni babu aure har abada. Sai gashi Allah ya amsa min Addu'ata jin labarin zuwanku."Tunda ya fara maganar gumi yake zuba akan fuskar Luyya, tsoro gami da Al'ajabi suka cikata. Kallon Muntari take tana so taga wata alamar da zata nuna cewar da wasa yake, amma kuma babu alamun hakan, sai gaskiyar da take gani atsakiyar idonsa da kuma fuskarsa.
Kai ta dafe tana ƙara jin zubar gumi akan ko wata gaɓa ta jikinta "Ya Allah!" ta faɗa cikin rarrauniyar Muryarta.....🥀🥀🥀🥀🥀🥀
_Tofa alƙawali dai ance kaya ne, ban saniba ko wanan tsohon alƙawalin zai cika, ammafa da alama mai guri ne yazo zai kore mai tabarmar da ya bararraje akai._ 😁😁😂
Kuyi malejin shafin *GIRAMAMAWA*
#IsmahaZainab
#UmNass
#NWA
#Cmnt,Like,share
#DaAmana
YOU ARE READING
ISMUHA ZAINAB Completed
AdventureAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...