*🏌🏻♀ISMAHA ZAINAB💍*
©By *😘Um Nass🏇*
*® NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA(Page 26)
Farin ciki ne sosai ya kama Siniyo Jummai, lokacin da taga duka firifawan na bin bayanta, hakan ya sa ta fara ɗana tarkon muguntar da zatayi ma jiniyas ɗinta, sai dai azuwa lokacin tana fargabar kada labari ya isa ga Ismaha Zainab.
"Tunda an gama miki ɗinki sai ki tashi mu tafi ai." Siniyo Shamsiyya ta faɗa tana kafe Jummai da ido.
Tashi tayi ba tare data tankaba, fatanta kada abin data shirya ya wargaje. "Muje to." bayan dai-daituwarta akan ƙafafuwanta, wanda ɗayar bata kaita ƙasa sosai ba. A zuciyarta tana aiyana irin kalar ramuwar gayyan da zatayi.
Murmushi Lateepha tayi, lokacin da idonta ya sauƙa akan na Siniyo Shamsiyya. "Mun gode Dear."
Ɗan harararta Siniyo Shamsiyya tayi ba tare da tace komiba ta fice ta barsu anan, suna mata rakiyar dariya, dan su da kansu sun-san rinjayarta sukayi, har ta amince da bukatar dukan ɗaliban.****
Har yanzu a bangaren Sa'adatu hankalinta yaƙi kwanciya, jikinta yayi matuƙar sanyin dan tasan halin Siniyo Jummai, ba zata taɓa hakura ba, sai ta rama abinda aka mata.
Fargabar rashin sanin abin da zata iya musu, shine yake ƙara faɗar mata da gaba, gashi Hauwa Ahmad itama ko ajikin ta itama. Abar batun Ismaha Zainab agefe, ita akwai ƙura akanta da zun-zurutun yarinta atare da ita, dan farin ciki take hankalinta kwance.Zuwan Hauwa Ahmad ya katsewa Sa'adatu tunaninta, zama kusa da ita Hauwa tayi cike da farin ciki, dan har yanzun bata bar dariyan abinda Ismaha tayi ba, idanunta nakan ismaha yanda take ta faman rubutu alittafinta, kamar ba wani abun da ta aikata yake damunta, sannan ta sake kallon Sa'adatu bakinta ɗauke da magana.
"Ya dai Yar uwa? Naga kin rafka uban tagumi hannu bibbiyu, kamar wanda labarin mutuwa ya isketa."Harara ta aika mata tana sauƙe ajiyar zuciya "Kinfi kowa sanin dalilin tagumina ai."
Ƴar dariya Hauwa Ahmad tayi, ganin yanda Sa'adatu ke son ɗora mata laifi akanta "Matsala ta ɗaya da ke, shine baƙin tsoron da har yanzu yake ɗawainiya dake. Nifa wallahi naji daɗin abinda Ismaha Zainab tayi ma Siniyo Jummai, badan ita ba da wallahi mun kaɗe har buzunmu. Qila da har yanzu bamu gama kukan tanadin muguntar da take shirin yi mana ba." ta kai ƙarshen maganar fuskar ta ɗauke da fara'a."Hmm! nikuwa bana farin ciki, dan nasan sarai Siniyo Jummai ba kyalemu zatayi ba, sai tarama abinda aka mata, tsorona ɗaya karsu hucce akan waɗanda basu-ji-ba-basu-gani-ba, dan nasan ta sarai da tanadin mugunta." Yanda Sa'adatu tayi maganar kaɗai, zaka kafahimci tarin damuwa da tashin hankali a tare da ita.
Sai alokacin Hauwa Ahmad ta farga da shukar da sukayi a idon makarwa "kin faɗi gaskiya Ƴar Uwata, wallahi sam na manta da wanan ɗabi'ar ta Siniyo Jummai. Allah dai ya jisshe mu alkhairinsa."
"Ameen" Sa'adatu ta faɗa tana rafka uban tagumi, ga wankin da ta ɗebo tasashi agaba, ta kasa yinsa.
*****
"Wallahi yau sai munci kan dunduniyar malafar takalmin uwar yaran nan, ga baki ɗaya tundaga kan aji ɗaya har zuwa aji biyar, sai sun san sun taɓo mu, babu tausayi balle sassauci." Laure mataimakiyar Siniyo Jummai ta yanko wannan maganar, tana zuge ganyen bulalin da aka zargo musu. tana cin alwashin akan genaral dukan da zasuyi, dan ta bama Siniyo Jummai ƙwarin gwuiwa akan yaufa tana tare da ita.Lateepha ta amshi maganar daga bakinta, cike da zakewa da abinda zasuyi yau "Allah ya kaimu dare dai."
Maganar da sukayi taja hankalin da yawa daga cikim ɗaliɓai, nan tsoro da dirar musu acikin zuciyarsu, da fargaba akan dare yayi.
Kafin wani lokaci maganar ta gama zagaye tsakanin sauran Jiniyas ɗin.Lokacin da labari ya isa ga su Sa'adatu sai da cikinta ya ɗuri ruwa. Kasancewar suna tare da Hauwa awanan lokacin "Ni dama nasan hakan sai ta faru, dole ba za suyi shuru su ƙyalemuba. Mun shiga uku!" Sa'adatu ta faɗa tana ɗora hannu akanta.
Kallonta Hauwa Ahmad tayi, zuciyarta fal tsoro kamar zata faɗo.
ESTÁS LEYENDO
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...