38

687 63 6
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

*😘UmNass🏇*

_Acikin ko wani shafi da suke wanzuwa da gifta tsakanikanin ku, nasan akwai mutane da yawa da sukan aro dauriya agareni dan su bani ƙarfin gwuiwa wajan ci gaba, na ku na musamman ne hakan yasa na baku shafin kyauta cike da *GIRMAMAWA* agareku:
  ANTY MAIJIDDA MUSA
MRS USMAN
Ummu Rahma

  Page 38

   Ta ɗauki tsawon lokaci tana riƙe da kanta, ko wata kalma ta maganar da Muntari yayi dawo mata sabuwa take acikin kunnuwanta. _"Toma ta ina zata fara? Ta wata hanya zata gamsar da shi akan matsalar Ismaha Zainab? Taya zai fahimci har yanzu akwai ban-banci tsakaninta da sauran mutanen da suke rayuwa su kaɗai? Duk da cewa an samu sauƙi da sauyi atare da ita amma har yanzu bata da tabbacin ta warke sarai musamman idan tayi la'akari da taurin kai na Aljannin da yake tare da ita. Amsar da ya kamata ta bawa Muntari ta ɓacema kwanyarta, idan ta sanar dashi zaiga kamar son bashi Ismaha Zainab ɗinne bata yi."_ saƙe-saƙen da take aƙasan ranta ne ya sha kanta.
  Ɗagowa tayi taga ita yake kallo da alamun sauraron amsar da zata bashi, murmushi tayi sanan ta gyara zamanta "Har yanzu cike nake da mamakinka Muntari, amma kuma da naga tabbaci atare da kai sai mamakin ya ɗauke daga kaina."
Murmushi tayi tana gyaɗa kanta, tana son ƙarfafawa kanta gwuiwa akan maganar da zata faɗa "Zan turoma Ismaha Zainab ka nemi soyayya daga gareta, muddum ta amince zan tsaya maka har ka aure ta."

Murmushin sa ne ya ƙara yawaita akan kyakkyawar fuskar sa "Nagode Luyya ɗinmu." kai ta gyaɗa tana yalwata nata murmushin ta shige cikin gida zuciyarta cike da fargabar abin da zaije ya zo, da ko wani taku na ƙafarta tana jin-jina girman al'amarin da zai wanzu tsakanin Muntari da Ismaha Zainab.

******
  Lokacin da Alh. Isah suka dawo gida tuni gari ya kaure da kiraye-kirayen sallahr magrib, hakan yasasu wucewa masallacin unguwar kai tsaye, suka bi jam'in sallah.
Bayan fitowarsu ne sukayi karo da Musaddiƙ wanda shima amasallacin yayi sallah.
  Risinawa yayi ya gaida Alh. Isah fuskarsa ƙunshe da fara'a ya amsa.
"Taho mu ƙarasa gida malam musaddiƙ, dan yanzu dawowarmu daga tafiya agajiye nake."

  "Ayya bari to na wuce gida, gobe sai na dawo in sha Allah."

Juyawa yayi da zummar tafiya wanda yasa Alh. Isah ya riƙo hannunsa  yanayin fuskarsa ya sauya zuwa damuwa "Nifa amatsayin ɗana na ɗauke malam musaddiƙ, hakan yasa nake ta gayyatarka dan kasancewa ɗaya daga cikin iyalina, ko wata rana na gayyaceka zuwa shiga sai ka kawo min uzurin da zai hana hakan faruwa. Ban san ko aranka akwai wata manufa daban akanmu ba, duk tsawon lokacin da muka ɗauka atare kaƙi bani dama guda ɗaya da zan kyautata maka."

Saurin ɗago kansa yayi ya kalli Alh. Isah wanda duhu ya ɗan farayi, sai dai hasken farin lantarkin daya cika kan titin ya taimaka wajan samarwa wajan da haske mai kyau, shi yasa yaga yanayin fuskarsa da kuma gaskiyar maganarsa.
_Toma taya zai shiga gidan mutanen da yake jin kunyarsu sosai? Bai shirya fuskantar Ismaha Zainab awanan lokacin ba, shi yasa yake gocewa duk wata hanyar da yake da tabbacin zata sadashi da ita. Amma da alamun hakan bashi da amfani, tunda gashi mahaifinta na ƙoƙarin yi masa bahaguwar fahimta._
  "Ba haka bane Abba, kawai inajin nauyi da kunyar shiga gidan ne."
  "Ni na gayyace ka ai malam Musaddiƙ, kaga wancan ƙaton abokin naka shi korarsa muke amma ya maƙale mana duk da yana da nasa iyalin, hakan bai hanashi zuwa ya cinye mana tuwo ba."
Dariya yasa ganin yanda Usama ya fara turo baki kamar ƙaramin yaro "Baba kaima ka biya ta yarinyar nan Ismaha Zainab ko?"

"A'a kawai gaskiyar data faɗa nake nanatawa, kada kazama irinsa kaji ɗana Musaddiƙ. Wuce mu tafi maza na fara jin yunwa." dariya yake yana magana wanda yasa shima musaddiƙ ɗin yin dariyar.

"Allah Baba har na fara jin kewarta, barin ma da babu wanda zan tsokana yanzu." ya faɗa yana yamitsa fuska.

Dariya Alh. Isah yayi dai-dai lokacin da suka ƙaraso gidan "Ai itama ta huta yau, dan zatayi barci babu ciwon kai."

ISMUHA ZAINAB CompletedWhere stories live. Discover now