BABI NA TAKWASS

389 47 0
                                    

*🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*

© by *😘Um Nass 🏇🏼

® NAGARTA WRI. ASSOCIATION

  Wanan shafin Sadaukarwa ne gareki  *_Real Mai Dambu ce_*

BABI NA TAKWAS (Page 8)

Tarar gabansa Malam Isubu yayi "Baka ce komiba zaka juya Alhaji Isah, idan babu halin ta baka rabin inaga ai gara kayi magana yafi kayi shuru?"

Kallonsa yayi sanan ya kalli Ruqayya da ɗiyarta wanda tun kallon farko da ya mata yaji tausayinta ya kamashi, duk da bai san mi yake damuntaba amma akallon farko idan ka musu xaka fahimci akwai wani al'amari mai girma atare da su. Murmushi yayi sanan ya fara magana "Banda abinka Malam Isubu aini da kai duk ɗaya ne, ko kyauta kace na sata ina mai tabbatar maka da cewar hakan za'ayi, balle kuma lamani akan bada rabi zuwa wani lokacin, wanan shi yafi komi sauƙi agareni, shi yasa ma banyi maganaba, ta bada abin da ya sauwaƙa kawai ba sai na bita bashiba, idan Allah ya kaimu wata shekarar da kwana sai ta bada kuɗin shekara gudan idan tana da wadatar hakan."

Ajiyar zuciya suka sauƙe akusan tare tsakanin Luyya da Malam Isubu suka kuma fara yi masa godiya cikin haɗuwar baki, musamman Ruqayya dataga abin kamar amafarki ko kaɗan batayi tsammanin zata samu rangwame awajan Alhajinba ayanda ta lura da shi, amma kuma saɓanin tunaninsu sai gashi ya musu fiye da abin da suka buqata, ƙullin kayanta ta kunce ta lalubo kuɗi nan ta qirgi dubu biyar ta miqa masa, acikin kuɗin ya zari dubu ɗaya ya bawa Malam Isubu kana ya zari wata dubu ɗayan ya damƙawa Ismaha Zainab "Gashi ki siyi biskit da alawa." mamakinsa ne ya kama Ruqayya hakan ma aɓangaran malam Isubu godiya suka ƙara masa har sai da yaji ba daɗi "Mutum ai rahma ne malam Isubu aduk inda yake baya rasa amfanin da zai maka da kuma ranar da zai ma, kamar kai gashi ina zaune ka kawo min ƙaruwa har gida, ni ya kamata na maka godiya." yana gama faɗar haka ya juya ya fice, bayansa Malam Isubu yabi shima yana ɗagama Ismaha Zainab hannu har suka fice.

  Ɗakin Ruqayya tabi da kallo tana kuma ganin ɗan qunshin kayanta, ga wata yunwa data mata dirar mikiya alokaci ɗaya, ko tantama batayi Ismaha Zainab najin fiye da wadda takeji "Allah gamu gareka, acikin sabuwar rayuwa da garin da bamu da wani da zamu kirashi da sunan danginmu, ka bamu mafita da sauqi acikin rayuwar da zamu fuskanta karka ɗora mana abin da bazamu iyaba."
Tana gama faɗar haka ta jiyo sautin kukan Ismaha Zainab sai faman cakwaikwayeta takeyi "Luyya Abinci" kukan take babu ƙaƙƙautawa kamar da ake mintsininta, to amma ita kanta taga dauriyar yarinyar, ba zata iya tuna yaushe ne taci abinciba, cikin sanyin murya ta fara mata magana "Kiyi haƙuri bari na bada asiyo miki abincin kinji." kai ta gyaɗa sai dai har xuwa wanan lokacin hawaye bai bar zuba acikin idanuwantaba, sai hannu da ta saka ta fara tsotsar bakinta.

  "Assalama alaikum" sautin muryar Malam Isubu ya doki kunnenta.
"Wa alaikumussalam maraba" ta faɗa tana ɗan ƙaƙalo murmushi.
  Shiga ɗakin yayi hannunsa ɗauke da tabarma sai kuma ɗaya hannun da yake riƙe da kwano babba, kallonsa take har ya ajiye kayan kana ya ɗago da kallonsa gareta yana murmushi "Naga baku da komi ne na shinfiɗa shine na kawo muku tabarma da bargo aciki, akwai kuma gidan sauro saboda muna da yawaitarsa anan, acikinsa akwai ƴar ƙaramar fitila saboda duhu sai kuyi maleji dashi kafin kuma garin ya warware muku,  wanan kuma abinci ne Mai ɗakina ta gama shine na karɓo muku sai kuci, ga ruwan leda (pure water) sai kuyi maleji da shi, sanan idan kuna buqatar wani abu ku min magana gidana shine na huɗu kafin nan, idan wani abu na amfani ko aike ya tashi kima mutanen da kuke gida ɗaya magana zakiji daɗin zama da su."

Risinawa tayi har ƙasa tana jin wani hawaye na zuba acikin idonta "Na gode sosai malam, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, tabbas ka gama mana duk wani taimakon da ko wani baqo yake buqata, Allah ya raya maka zuri'a ya rufa maka asiri duniya da lahira kamar yanda ka rufa mana namu asirin."

"Ameen ya Allah" ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa dan sosai yaji daɗin addu'ar tata, daga haka ya fice ya barsu yana musu sai da safe.

Tabarmar ta ware ta shimfiɗa musa afaffaɗan ɗakin tabarmar da girmanta qwarai gefe ta kawar da bargon da gidan sauran da ya kawo wanda ko wata igiyarsa yake maƙale da ƙusa, ɗan murmushi tayi aranta taji sanyi sosai,  ashe aduniya akwai mutane na gari har yanzu wanda sukeyi dan Allah? Ta faɗa tana zaunar da Ismaha Zainab akan tabarmar sanan ta janyo da kwanon abincin gabansu, tuwon laushi ne na hatsi wanda yasha tuqi da ganin yanda yake sheqi, ga kuma ya samu qarin armashi na miyar ɗanyan kuɓewa wanda tasha qananun kifi na ƙawara, ga man shanu daya daki hancinta, ganin tuwon da ƙamshin miyar su suka taimaka wajan ƙara hautsina cikinta ya ankarar da ita tarin yunwar data tara, Ismaha Zainab kuwa tuni ta fara dariya tana tafa hannayenta "Luyya Tuwo anci" ta faɗa tana qara washe haqoranta.
"Yanzu kuwa zaki ci Ismaha Zainab indai abinci ne." tana gama faɗar haka tayi Bismillah ta fara bata abaki haɗiya kawai take bata tauna, sai da ta cinye fiye da rabin abincin sanan tace "An ƙoshi, luwa" ruwa ta bata tana kallonta cike da tausayi, sanan itama ta fara cin abincin, sosai taji daɗinsa hakan ya sata cinyeshi tass bata ankareba sai jin kwanon tayi wayam babu komi. Hakan ya sata suɗe hannu ta gyara shimfiɗarta dan tuni Ismaha Zainab ta ɓingire tayi barci, aranta ta ƙara shima malam Isubu albarka saboda taimakon da ya musu, sai da ta kammala yin shimfiɗa ta kwantar da Ismaha Zainab kana ta fito tsakar gida, alokacin har almuru ta gabato ana kiraye-kirayen sallahr magrib, kallonta takai ga tarin matan da suke tsakar gidan sai kai da kawowa suke, wasu kuma suna zaune ana cin uwar hira ba tare da sun miƙe dan su gabatar da sallahr da ake kiraba, ƙarasawa tayi kusa da su ta musu sallama, amsawa sukayi suna ɗan murmushi atare, sai wadda ta hakimce agefe fuskarta babu yabo babu fallasa ta amsa, murmushin yaƙe Ruqayya tayi kana tace "Dan Allah ruwa zaku ɗan sanmin na ɗauro alwala." kallonta sukayi kamar sunga sabuwar mutum, kamar ba zasuyi mata maganaba, hakan yasa jikinta yayi sanyi ta fara qoqarin juyawa tabar wajan, saboda kallon da suke mata yasa ko wani karsashin dake atare da ita ya gudu.

🥀🥀🥀🥀🥀
*GIRMAMAWA*

#Um Nass
#NWA
#cmnt like nd share
#Da amana

ISMUHA ZAINAB CompletedWhere stories live. Discover now