*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©BY *😘Um Nass
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA SHA SHIDA (Page 16)
A zaune suke a tsakar gida jifa-jifa suke hira wadda a cikinta maganar Luyya da Salamatu tafi yawa, Rabi kuma na gefe tana gyatsina baki.
ƙarshe ta tashi ta ɗora sanwar tuwo ta barsu a zaune "Ni kam mi yasa kuke barin su Usama suke zaune haka kara zube ba tare da suna zuwa makaranta ba? Gashi ƙannansu ma sun bi sahun su suma basa zuwa."
Gwaɓe baki Salamatu tayi cikin nuna halin ko in kula ta fara magana "Wato Ruƙayya ko kaɗan Alhaji baya son a yima yarannan faɗa da tsawa, domin a baya idan na matsa musu ƙarshe sai dai rigima ta kai ni ga barin gidan nan, shi yasa yanzu ba ruwa na kowa ya gyara ya sani."
Ido Luyya ta fiddo waje cikin tsantsar mamaki "Amma kuwa wannan ba gata yake musu ba, a nawa zaman da nayi a garin nan na ƙaru da abubuwa masu yawa na ci gaban rayuwa. Zan iya cewa ilimi shine babban gatan da iyaye suke bawa yaransu, musamman saboda halin rayuwa."
"Hmm kar ki tona zuciyata kiji ƙunan da ke cikinta, Allah ya sani ni kam ina son karatu, duk da cewar ni ban samu damar yinsa ba."
"Hirar mi kuke yi ne naji kun shiga yanayin Alhini?" Rabi ta tambaya tana zama kusa da Luyyah.
"Akan maganar karatun yarannan ne, take cewa muna tilastasu zuwa"
Ido ta ƙwalalo waje cikin tsoro da alhini "Bar batun nan kin ji, waya isah ya takurama yaran Alhaji ya tsinkayi tafiyarsa na jiran sa."
Dariya suka saka gaba ɗaya, sai dai a zuciyar Luyya ta qudurta sauya ma mutanen gidan nan rayuwa, tun daga kan mai gidan har zuwa su kansu mata da yaran gida, tabbas akwai rashin wayewa da ƙarantar ilimi a tare da su, dama ana samun haka har a cikin garin da za'a ƙira shi da maraya? Abin ya mutuƙar bata mamaki da tsoro, ta kuma gode wa Allah da nata zaman yasha bam-bam da nasu.
Kallon gefen da yaran gidan suke wasa tayi, taga Ismaha ZAINAB a tsakiya tana faman yi musu manyance, idonta ne ya kai kan Asshe ƴar gidan Rabi wanda Walidi ya kwatsama duka dan ta ɗora ƙafarta a kansa, kafin tayi kuka Ismaha ta toshe mata baki "Kiyi haƙuli zan lama miki."
Juyawa tayi da kallonta ga Walidi ɗan gidan Salamatu, harara ta buga masa "Mun daina wacan da kai tunda kai mugu ne ka balmana wasan mu."
Hararar ta yayi cikin jin haushin ta dan dama ya fisu girma a wajan, aƙalla zai yi shekara bakwai "Babu inda zani. Ke awa za kice nabar wasan?".
Bata masa magana ba ta tashi taja hannun Asshe da sauran yaran Khadija da Bilki yaran Salamatu suka biyo bayanta, sabon wasan ta kafa ba tare da ta sake kallonsa ba.Labari take basu suna dariya wanda yawanci akan makarantar da take zuwa ne, tana ƙara ƙawata musu daɗin da ke cikin makarantar "Kunga ko a makalantar har lilo muke hawa, mu hau kan banci, wata Aunty ɗin mu mai gashi bucucu ta linga kalanto Ingilishi, bafa a magana ilin wanda muke yi."
Tagumi suka buga cikin jin daɗi ina ma suke zuwa makarantar da take zuwa "Ya zakal yace ina da kokali, yana ta siya min alawa da kuɗinsa. Haka ma Aunty ɗin mu tace ni akwai kwalwa." ta ƙarasa tana buga kanta da hannu gami da yin dariya.
Suma dariyar suka sa, Khadija mai wayon cikin su ta ce "Ni kam idan Alhaji yazo zance ya kai ni irin makarantar ku."
Suma sauran yaran suka fara kiran "Muma muna so sai muna tafiya abunmu mu huɗu ko?" kai Ismaha Zainab ta ɗaga cikin jin daɗi "Wallahi kuwa."
Walidi ne ya matso ya zauna kusa da Ismaha Zainab yana dariya "Ai dai nace na bar dukan kowa, kina hirar dani kinji."
Baki ta turo gami da shan kunu bata yi magana ba "Allah na daina dukan ta"
ESTÁS LEYENDO
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...