*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©BY *😘Um Nass 🏇*
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
BABI NA SHA ƊAYA (Page 11)
Kallonta suka ci gaba da yi har ta qaraso palon kana ta zauka akan kujerar da take fuskantarsu "Musaddiq karatunka yana da muhimmanci agaremu, bama mu kaɗaiba hatta kai zaka fi samun nutsuwa idan akace acan kakeyinsa, ka dai san ƙasar nan tamu da yanayin da take ciki baka buƙatar wani tuni akan abin da ya kamata kayima kanka."
Murmushi yayi mai sauti wanda da ganinsa na takaici ne, duk da kasancewarsa ba mai musu da jayayya ga maganar mahaifan nasaba amma awanan gaɓar yanaga kyautuwar tanka musu ita "Amma kuma duk da raunin ƙasar nan Umma tana da karatu, mutane da yawa sun amfana da moruwar karatun da ke cikinta, ba lallai ne sai agarin nanba ko wani gari zan iya zuwa nayi karatuna, ni dai kawai naji araina cewar ina tare da ku, banyi nisa da gida ba."
Kai ta girgiza kana ta miƙe tsaye "Bizarka ta riga data fito haka kuma an ɗaukeka amatsayinka na ɗalibi, kaga wata magana kuma yanzu ɓata lokaci ne." tana gama faɗar haka ta ƙarasa daining dan karin kumallo.
Magana yake sonyi amma kuma yasan ko kaɗan bazai iyaba, dafa kafaɗarsa Abbansa yayi, yana aika masa da murmushi mai nuna kulawa agareshi "Ko ina gidane ga musulmi Musaddiq, musamman da ya kasance ƙasar musulmi zaka je, Addu'ata agareka da fatana ako yaushe shine Allah ya sanya albarka akaratun da zakayi, Annabi s.a.w yace "Mu nemi ilimi koda zuwa birnin Sin ne" dan haka Misra batayi nisaba asalima gida ce, duk lokacin da kayi marmarin jinmu akwai waya zaka dawo ka taddamu lafiya, shekara kwana ce. Tashi muje muci Abinci." ya qarasa maganar yana riƙe da hannunsa, wanda yake jin hankalinsa ya kwanta ya kuma samu nutsuwa da tausasa kalamansa da mahaifin nasa ya masa, Abbansa ya iya bi da mutum, cikin soyayya yake yin magana da yaransa, saɓanin Ummansa da ta fiya tsawa da hancini ga yara, uwa uba bata zama dan taji matsalolin yaranta, jiki asanyaye ya miƙe ya bi bayansa suka nufi daining ɗin wanda har Ummansa ta fara cin nata abincin ba tare data kulasuba, sai da ya zo ne ta miƙe ta zubama Abbansa kana ta zuba masa ta tura gabansa "Ka tabbatar ka cinye." ta faɗa tana aika masa da harara, shi abinma dariya ya bashi kamar wani yaro ƙarami, haka ya fara cin abincin, can kumar daya tuna wani abu ya tsaya "Umma Jidda fa? Banji motsintaba"
Murmushi tayi gami da gyaɗa kai tana haɗiye lomar dake bakinta "Yau da wuri ta tafi makaranta tace suna da text ne, kuma yanzu so take tana ɗaukan kyautar mai zuwa da wuri makaranta, last time ɗin daya wuce ƙawarta aka bawa." ta qarasa maganar tana dariya wanda suma suka tayata da dariyar sai Abba da ya ƙara da cewa "Oh Jiddah rigima, shi yasa yau ba'a tasheniba ashe?"
"Aikuwa nima agurguje aka min sallama wai na fiya rashin sauri" nan suka ƙara saka dariya gaba ɗaya."Kema kenan Umma yau anga rashin hanzarinki?" Musaddiq ya faɗa yana murmushi, wanda shine yafi yawa akan dariyarsa.
"Zata zo ta sameni ai" ta faɗa tana jinjina kai, wanda hakan ya ƙara bawa Abba dariya.
"Lallai yau naji ku keda ƴar fadarki." sai alokacin ta ankare ta rufe bakinta."Na manta ashefa ku ƴan jam'iyyar adawa ne na faɗa muku."
Tashi sukayi suna dariya Abba ya kalli agogo "Nikam zan Wuce Umman Jiddah sai kuma na dawo?"
"To Allah ya kiyaye ya tsare hanya, ya dawo da kai lafiya Abban Musaddiq" ta faɗa tana murmushi wanda yasashi dariya shima.Idan har akwai abin da yafi komi yima Musaddiq daɗi bai wuce daddaɗan zaman da iyayensa sukeba, cike da soyayya da kulawa, shi yasa ko kaɗan baya son yayi nisa da su, amma kuma ƙaddararsa tasa ya fara karantar Islamic edication gashi kuma abaya yayima kansa katoɓarar shifa jami'atul Azhar zashi ta misra, wanda yasa mahaifinsa nema masa karatu acan.
Ahaka ta rakosu har harabar Adana motocin musaddiq ya shiga mazaunin Direba Abbansa ya shiga baya, nan take mai gadi ya wangale musu ƙofa suka jaa yana musu fatan sauqa lafiya.
Asalin Musaddiq:
Mahaifinsa Alh. Adam mai katako hafaffan garin Haɗejia ne dake jahar jigawa su huɗu iyayensu suka haifa shine ɗa na uku agidansu akwai yayyansa Ibrahim da Abdullahi sai Qanwarsu Autarsu Khareematu, sun taso da tsantsar kulawa daga mahaifinsu malam Habu da iya Hauwa, dai-dai gwargwado sun samu ilimin Addini dana zamani wanda alokacinsu ana kama yara ne akaisu makaranta da qarfi to aciki akayi dace aka tisa ƙeyar Adam da yayyansa guda biyu, aranar iyayensu sunyi kuka dan abin ya zame musu abin nuni ana dariya duba da kowa yana ɓoye yaransa idan ana kamen, sai dai cikin ikon Allah hakan ya zame musu alkhairi domin karatun ya musu amfani, sai gashi Ibrahim ya samu aiki malamin makaranta shi kuma Abdullahi ya zama lauya acikin koti hakan ya ƙara ɗaukaka darajar gidan nasu, tuni iyayensu suka fara alfahari da shima gobnati albarka, alokacin da aka yaye su Adamu sai aka ɗaukeshi aiki amatsayin malamin jinya, duk da alokacin mutane kansu na duhu sunfi ganewa da maganin gargajiya, ba ƙaramin wahla yashaba wajan wayar musu da kai, yakan kuma yi ƙoƙarin kula da iyayensu, ahankali samunsa sai ya ninka na yayyansa saboda shagon daya buɗe na siyar da magani, tafi-tafi sai gashi Allah ya albarkaceshi ya buɗe shagon saida kayan gine-gine sai dai yafi qarfi afagen saida falanki, nan sunansa ya sauya akafi kiransa da Alh. Adamu mai katako saboda sauƙin da yakewa mutane, acewarsa kowa agarin danginsa ne, aɗan tsakan-kanin nan suka biyama iyayensu zuwa ƙasa mai tsarki suka sauƙe farali, bayan dawowarsu akayi bikinsu duka harda Karimatu wanda ta Auri abokin yayanta Hussaini shima lauya ne mai.
Sai ya zama ana yima gidansu inkiya da gidan masu doka.
Auren zumunci Alh. Habu yayima Adamu da er ƙanwarsa da take hannun matan uba suna gana mata azaba, tun rasuwarta yaso karɓanta amma ubanta ya hana ganin abin yaƙi ƙarewa ya sameshi daya Aurama ɗansa Adamu ita, dan alokacin yayinsa suna da mata da yara uku, uku sanin matsayinsa yanzu aguje ya bada auren aka ɗaura ba tare daya sanar da mataanba, dan tsaf zasu iya hana auren, Maryama nutsattsiyar yarinya mai haƙuri amma takurawar da ta samu yasa ta dawo shuru-shuru da kuma masifa, abu kaɗan sai ya hassalata, sai dai kyakkyawa ce ƙwarai.Bayan shekara biyu Allah ya albarkacesu da samun ɗa namiji da kanta tace yasa sunan Mahaifinsa Abubakar suke masa alkunya da musaddiq, saida yafi shekara goma sanan aka haifa masa qanwa Anan suka saka mata Hauwa'u taci sunan Mahaifiyar Maryama da ta Adamu dan suna ɗaya garesu.
Daga nan haihuwar ta tsaya musu cak, sai suka ɗauki son duniya suka ɗora akan yaran baya kakaninsu kamar su cinyesu musamman Musaddiq da yake da nutsuwa uwa uba haquri matsalarsa ɗaya miskilanci.
Zumunci tsakanin Ahalinsu kuma sai sam barka, Musaddiq ya qare makarantar gaba da prmmry inda ya karanta ɓangaran arabiya domin shi atsarinsa yafi son Ilimin Addini fiye dana zamani, duk da ana musu turanci amma bai kai Arabic yawaba, tun alokacin yacema Abbansa shifa Misra zaije yayi karatu dan nan ne maƙurar karanta Arabic yana son Addinisa yana kuma son ya iya yaren da yafi ko wani yare daraja, sai gashi yanzu kuma yana jin babu daɗi da tafiya ta zo Wanan kenan.
*****
Kuka take tana birgima tana jifa da duk abin da yake jikinta "Wallahi ban yaldaba Allah, Allah kuwa ni sai kin ciyo min babana, kulum kulum inaga jiddo babanta ke kaita makalanta, da yayanta amma ni cai dai ya xakal ya kaini, Allah ban yaddaba."
Kukan taci gaba da yi, ganin taƙi kulata yasa ta matsa kusa da ita ta fara jan kanta tana goga mata hawayen fuskanta "Luyya ko kulma ce" sai alokacin ta leƙa fuskanta abin daya bata tsoro bai wuce ganin hawaye na zuba akan Fuskar Luyya ba.
Kuka take na tausayin rayuwar da suke ita da Ismaha ɗin acikin shekara biyun da suke fama da gidan haya, duk da sun samu alƙibla mai kyau da rayuwa mai ƴanci, zama cikin wayayyun mutane masu sanin hakkin ɗan Adam, amma ko kaɗan hakan ya kasa mantar da ita gida da abin daya barota dashi, kukan da Ismaha Zainab take ya tada mata da mikin da ta binne acikin zuciyarta acikin shekara biyu, iyayenta da kuma Idriss acikin wata rayuwa suke? Baqin fantin da aka mata take fatan ace ta warwareshi, amma kuma yayi kusa ayazu ta koma, yayi sauri da yawa tabar garin da akaƙi karɓan uzurinta aka kuma wofintar da ita.Gashi abin da takaici tace tana zaman kanta agidan haya mai tarin mutane, tasan tambaya ɗaya ce zata zo bakin mutane shine ta koma Karuwanci ta samu Lasisin yinsa. Wanan tunanin daya zo kanta shi ya ƙara tada mata hankali nan sautin kukanta ya qaru.
Hawaye taji ana goge mata cikin sanyin murya tace "Yi hakuli Luyya nabal kuka, bana con babal nawa, tunda baya xuwa ganina." daga haka ta ɗora kanta akan cinyarta tana sauqe ajiyar xuciya, hannunta ta ɗora akanta tana shafa hawaye na bin kwarmin idonta.
🥀🥀🥀
#Um Nass
#NWA
#CMNT, LIKE, SHARE
#DA AMANA
ESTÁS LEYENDO
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...