*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB 💍*
©BY *😘Um Nass🏇*
Wattpad @UmNass
Page 33
Da hanzari Rabi ta ɗebo ruwa mai sanyi a friegh ɗin dake palon Luyya, aka fara yayyafa ma Ismaha Zainab, amma kuma ko kaɗan bata motsa ba, asalima kamar sun ƙara yayyafa mata wani abun da zai ƙara sanƙarar da ita.
Kai take girgizawa tana ƙara dunƙulewa awaje ɗaya, hannunta kuma duk adunƙule suke awaje ɗaya.
Hawaye ne ya fara sartun zubowa a idon Luyya ga wani tsoro da fargabar da ke shigar ta.
"Hafsat ɗauki waya ki kira min Abbanku yazo mu kaita asibiti." salamatu ta faɗa tana ɗora kan Ismaha Zainab akan cinyar ta, wanda tana ɗorawa take zamewa.
"Anya wanan rashin lafiyar tata yana da alaƙa da asibiti Yaya? Ki kalli yanda take sanƙarewa tana ƙara dunƙulewa awaje ɗaya, kuma numfashin ta na fita akai-akai." Rabi ta faɗi maganar tana nuni da yanayin da Ismaha Zainab ke ciki.
"Mi kike tunani akai?"
Kallon Luyyah tayi wanda har zuwa wanan lokacin tana dafe da kanta, bata ɗago ba, hawaye ne kawai yake zuba a idon ta, haka kuma tana jin wani abu na taso mata aƙasan ranta akan komawar su gida."Ina tunanin Jinnu ke damun ta gaskiya."
Shuru ne ya ƙara cika ɗakin, kowa da abin da yake saƙawa aƙasan ransa.
Shigowar Alh. Isah aruɗe shi ya kawo sauyin shurun da ɗakin yayi, domin tuni Hafsat ta kirashi awaya "Subhanallah! Mi ya samu Zainab ɗin haka?" ya faɗa yana ƙarasawa kusa da ita, hannun sa da ya ɗora ajikin ta yaji kamar ya taɓa shokin ɗin wuta, da sauri ya janye hannun nasa.
Yana kallon ta har awanan lokacin hannunta na ɗunƙule kamar yanda take acure awaje ɗaya, ba ƙoƙarin da Salamatu ba tayi ba akan ta wareta amma abin ya gagara, ƙarshe idan ta kai hannun ta sai taji ana janta da shokin ɗin wuta.
"Abin nata ne sai kurum Alhaji, munyi tsammanin ma suma tayi amma daga baya sai muka ga kamar shafuwar Aljannu." Rabi ta faɗa cikin ƙarfin gwuiwa dan duk an rasa mai bakin magana acikin su, Luyya kuma sai faman sharar hawaye take afakaice, batare data tofa nata batun ba.Da saurin sa ya tashi "Bari to na kira malam Ado mai ruƙiyya, dama yanzu na wuce shi a masallaci."
Bai jira maganar su ba ya fice da saurin sa kamar xai wuntsula baya.*****
Tunda ya bar ƙofar gidan zuciyar sa ke ƙunci da tafarfasa, ƙarshe dai kasa yin tuƙin yayi ya samu gefe ɗaya ya tsaya, ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya, wani abu kuma na ƙara tokare masa aƙasan zuciyar sa._"Minene laifin sa? Wani irin zunubi ya aikata haka atsawon rayuwar sa? Bai taɓa tsammanin fuskantar turjiya da ruɗarwa daga Ismuha Zainab ba, amma kuma gashi komi ya sauya, aɗan ƙanƙanin lokaci. Ta daƙusar masa da ko wani sa rai da yake da shi akan ta da dukkanin wani farin ciki na rayuwar sa."_
kiran sallahr da ake amasallacin kusa da inda yake shi ya ankarar da shi da gabatowar magrib awanan lokacin, fitowa yayi cikin nutsuwa ya nufi ƙofar masallacin, anan ya ɗauki buta ya ɗaura alwala kana ya shiga masallacin.
Bayan an idar da sallah ya daɗe yana xaune har aka samu sauƙin mutane awajan, ya rage daga shi sai Limamin da ya ja su sallah, shima yana faman duba wasu litattafai ne.
Magana ya fara jiyowa sama-sama hakan ya sashi ɗagowa kai ya kalli masu maganar, limamin ne da wani mutum bai ji farkon maganar ba sai ƙarshen amsar da Limamin ya bada "Banƙi ta taka ba Alh. Isah, amma yanzu nabar yin ruƙiyya saboda tsorata iyalina da akeyi, acikin su ma har yanzu idan na uwar gidana ya tashi ƙarshe garin take bari ta yanki jeji."
"To amma Malam Ado baka san wanda yake ruqiyyar ba ka haɗa ni da shi?"
Kai ya girgiza cikin son kawar da batun, dan aƙallah yanzu tsoron duk wani abun da ya shafi Jinnu yake, ba akan karan kansa ba sai akan iyalin sa da ake fanshewa "Gaskiya bana ce maka ga takameman mutum ɗaya ba, amma ka sake bincikawa agaba."Shuru Alh. Isah yayi yana dafe da kansa, tausayin Ismuha Zainab da halin da ya barota kawai yake ji.
Tashi musaddiƙ yayi ya nufi inda suke, wani tausayi da haushin Limamin duk ya cika shi, ace yana da sani akan wanan yace yabar yi, saboda wata barazana ta banza da wofi, mi yasa bai bawa iyalin nasa Addu'ar kare kansu ba? Anya ma ya iya Ruƙiyyar da ake kukutawa ma.
"Idan babu damuwa muje gidan sai na duba yarinyar taka"
Da mamaki Alh. Isah yake kallon sa, ganin matashin saurayi na maganar yin Ruƙiyya ko dai baiji abin da ya faɗa ba "Yaro jeka sha'aninka kaji, magana nake akan cirema ɗiyata aljannu ba wai zana mata jarrabawar makaranta ba."Murmushi Musaddiƙ yayi sanan ya risuna "Eh duka naji maganar da kukayi ai, idan ka shirya nemawa ɗiyarka magani da sa rai da waraka ka wuce muje na ganta."
Cikin sanyin jiki Alh. Isah ya tashi, dan dai kawai ance ba'a ƙin ta mutum, amma banda haka da yaushe xai yi kasadar tunkarar wanan yaron da batu na iskokai, sai da suka fito waje kuma yaga kayan dake jikinsa da kyakkyawar kamannin sa gabansa ya shiga lugudan faɗuwa _"Shikenan ta faru ta ƙare, wata ƙila aljanin jikin Ismaha Zainab ɗin ne ya zo min asuffar mutum"_ maganar da Alh. Isah yayi yana goge gumin da ke fuskar sa.
"Magana kake ne Baba?"
"A'a. Ina duba hanyar ne naga bata da kyau, kada ka ɓata kayan jikin ka."Kallon wajan Musaddiƙ yayi, yaga babu wani rashin kyan sa, asalima bakin titi ne da kwalta malale awajan, "Ba damuwa, idan ya ɓaci na wanke."
"Na gode Allah."
Ya faɗa dai-dai lokacin da suka ƙara so gidan, ido Musaddiƙ ya wara cikin mamaki, domin dai yasan nan ne gidan su Ismaha Zainab, ja yayi ya ɗan tsaya ganin yanda Alh. Isah ke ƙoƙarin shiga gidan.
"Taho mana samari ai nan ne gidan."Shiga yayi yana dafe da zuciyar sa da take bugawa da ƙarfi, fatan sa kada ya haɗu da Ismuha Zainab ta sake sauƙe masa wani kwandon tujarar, ko kuma tayi tsammanin wata manufar ta kawo shi ta daban.
Da tarin tunane-tunane ya shiga gidan ƙarƙashin jagorancin Alh. Isah dake ta masa kuwar ya shigo.
Har sai da suka shiga ɓangaran Luyya yana biye da shi, sai wara idanuwa yake, amma baiji motsin kowa ba, asalima gidan kamar anyi mutuwa babu sautin komi dake gudana acikinsa.Dakatawa yayi daga bakin ƙofar ɗakin sanan ya sanar da Alh. Isah akan ya fara masa iso da mutanen gidan kada ya shiga kai tsaye.
Shiga ɗakin palon Alh. Isah yayi cikin gamsuwa da bayanin yaron, ayanayin daya bar Ismaha Zainab ahaka ya same ta babu wani sauyi da aka samu na ci gaba, kowa yayi jugum-jugum a ɗakin.
"To ku kintsa da mai Ruƙiyyar nake, yana ƙofar palo yana jiranku."Tashi su salamatu sukayi suka bashi waje wasu kuma suka yafa ɗankwalinsu suka lillaɓe jikin su da shi, sai Luyya data saka hijabi ajikin ta, ganin haka yasa su salamatu sake gyara nasu lilliɓin.
"Shigo malam." Alh. Isah ya faɗa yana wara hannunsa da nuni ga ƙofar palon.
Shiga yayi da sallama ɗauke abakinsa, kansa aƙasa yana jin bugawar zuciyar sa na ƙaruwa, amsawa sukayi cikin haɗin baki, amma kuma da mamaki suke binsa da kallo, musamman ganin sa da sukayi matashin saurayi, gashi kuma da ance za'a kirawo malam Ado mai ruƙiyya.
"Wanan ce marar lafiyar?" cikin sanyin muryar sa yake maganar, yana nazarin halin da take ciki.
"Eh itace." suka amsa masa cikin haɗuwar baki.
Kallon Alh. Isah yayi sanan ya kalli tarin mutanen da suke ɗakin "Ya kamata su fita daga ɗakin, kai da maman ta sai ku tsaya ku riƙeta, abani ruwa akofi."
Da sauri hafsat ta fita ta ɗebo ruwa akofi ta miƙa masa, sanan ta fita waje ganin kowa ya fice, ya rage Luyya da Alh. Isah, sai kuma malam Musaddiƙ mai ruƙiyya.
Ruwa ya karɓa yayi Addu'a aciki sanan ya fara yayyafa ma Ismaha Zainab, wanda har awanan lokacin bai fahimci ita ce awajan ba, ƙara ta sa mai ƙarfin gaske tana ƙara miƙewa, sai alokacin yaga Fuskar ta, ido ya waro waje cikin mamaki, kafin ya ankare yaji an bige kofin dake hannun sa ruwan ya zube, cikin hanzari yakai kallon sa ga wanda ya masa wanan aika-aikar Ismaha Zainab yaga idon ta ya rikiɗe ya koma kalar fari da ratsin kore-kore ajikin sa "Ba munce kada ka dawo ba? Ko bakaji tace bata son ka ba? Miyasa komi sai kai? Mi yasa ka takurama rayuwarmu?" wata kakkausar murya ta faɗa cikin ƙaraji da jin haushi.
Nan aka shiga kallon-kallo tsakanin Luyya da Alh. Isah suna kuma kai kallon su ga Musaddiƙ ɗin.
"Mi hakan yake Nufi?"🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
_Taku kaɗan ya rage mu kai ga gaci, koda bance komi ba kun fahimci zunzurutun muhimmanci dake cikin wanan tafiyar, kalma guda mai amo wanda take fita da umarninku ta wadace ni, ku himmatu ku kuma magantu akan dai-dai da rashin sa acikin Kimar da take taku wanda tafi ko wacce, akan hakan zan ɗauko mafi kyau da soyuwar kalma agare ni *GIRMAMAWA*_
#ISMUHA ZAINAB
#NWA
#UmNass
#Cmntns, like, and share
#Da amana
![](https://img.wattpad.com/cover/166166065-288-k414201.jpg)
YOU ARE READING
ISMUHA ZAINAB Completed
AdventureAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...