*🏌🏼♀ISMAHA ZAINAB💍*
©BY *😘Um Nass🏇🏼*
_FOLLOW ME ON WATTPAD @UmNass_
® *NAGARTA WRI. ASSOCIATION*
_*Ba ko wata soyayya bace ake buɗe ta ta yanda duniya da mutanen cikin ta zasu gaskata hakan tun kafin ka magantu, wasu suna ninke nasu muradin a zuciyarsu ta yanda zasu kalle shi daga nesa suyi murmushi saboda jin daɗin su, akwai banbanci tsakanin abin da ka so da wanda duniya zata kira shi a matsayin wanda kake so, kamar haka nake ji a cikin Labarin Mamarsu bazan kira ta da tawa ba dan har yanzu bata cika ma'aunin hakan ba, amma dai ina son BOSS acikin ko wani labari. Lolx 🤪 thank so much Dear Sadiya Jegal ki sanar da Mamansu akwai mai yinta da babbar murya a cikin labarin Talauci ba madogara bane 🤝🏼*_
BABI NA BIYAR (Page 5)
Basu yi yunƙurin mata magana ba illa rakiyar da suka mata da ido, domin a jikinsu ko wata laka ta sanyaya daga kuzarin da suke da ita, sabuwar Ismaha Zainab suke ga a gabansu wanda take cike da kuzari da surutu maganar ta ta dawo mai sauti da fidda harrufa da ƙarfin su, saɓanin a baya da sai ka kashe kunne ka matso da ko wata nutsuwa gare ka sannan zaka tantance maganar ta. Ɗaki ta shige ba tare data kallesu ba sai can ta sake fitowa tsakar gidan ta makawa Garba Almajiri harara "Kada ka kala duwa nema na kana ƙwala min cila a maƙota." kai ya iya ɗagawa alamun to dan tsoron ta ne yaji ya shige shi sosai.
Kitchen ta shiga ta fara buɗe-buɗen kwanikan da aka wanke can ta fito da ƙatuwar langa da taliya da ɗan-wake a cikin ta, baki ta wage tana dariya sannan ta shimfiɗa tabarma ta zauna "Kai kul kusa min wawa, ku bali kowa zai samu, ai yana da yawa." ta faɗa tana matso da kwanon gabanta, sai faman zumɓura baki take, waiwaye aka fara tsakanin Garba Almajiri da Ruƙayya, suna neman waɗanda take ma magana amma basu ga kowa ba, nan jikin Garba ya fara rawa ƙarshe ya ruga da gudu waje Ruƙayya na kiran sa amma ina bai tsaya ba, dan shi kam ya haƙiƙance ba ƙalau Isma Abu take ba kamar yanda yaga alamomin hakan a tare da ita.
Cikin sanyin jiki Ruƙayya ta ƙarasa kusa da ita ta zauna kanta ta fara shafawa cike da soyayya da tausayinta "Ke da wa kuke cin abincin kike cewa kar su miki wawa?" ta tambaya cikin tsoron amsar da zata fito daga bakin Ismaha Zainab ɗin.
"kawayena ne Luyya." amsar da ta bata kenan tana ci gaba da cin abincin, duk da ba loma take ƙatuwa ba amma cikin abin da bai wuce mintuna biyar ba ta cinyen abincin duk yawan sa. Kamar gunki haka Ruƙayya ta tsaya tana binta da kallo komi na kanta ya tsaya cak ta kasa yin motsi balle tayi magana sai da ido take binta da kallo, maganarta ta sake tsinkaya tana cewa "Yauwala ku jila na ajiye kwanon sai musha luwa." da gudu ta shiga ta ajiye kwanon ta koma ta ɗauki buta ta wanke hannayenta, sanan ta buɗe randar ƙasar da take tsakar gida ta ciko moɗa kamar abin almara tass ta shanye ruwan sannan ta ajiye moɗar "Ayi lige-ligen shiga ɗaki kuma." nan ma ta shige da gudu ba tare data kula da ita ba, kai ta dafe da ƙarfi "Akwai gundumemiyar matsala, tabbas Ismaha Zainab ba ita kaɗai bace." ta faɗa hawaye na sirnanowa daga cikin idonta, wanda na tausayin yarinyar ne da rayuwar da zata shiga, tayi ƙarama ace ta fara fuskantar ƙalubale haka daga mutanen ɓoye, duk da su basa raina ruwan shuka.Tashi tayi ta leƙa ɗaki a nan ta taddata tayi ɗai-ɗai a kan gadon ta tana barci, kinkimar ta tayi ta goya ta ta ɗauko gyalen ta ta rufe gidan, kai tsaye gidan su suka nufa kafin taje ta jiggata saboda nauyin da taji Ismaha Zainab ɗin ta ƙara yi mata.
Da fara'a Innar mu ta tare ta tana kiran "Maraba da baƙi, yau kishiyar aka goyo haka dan abin haushi." ta faɗa tana ƙoƙarin kwanto ta daga bayan, sai dai kamar an jona mata shokin haka taji an jata, da sauri ta janye hannunta "Kai naga ba sanyi a ke ba amma kuma kayan ku ya ɗauki sanyi har yana jonawa mutum wuta." Innar mu ta faɗa tana barbaza idanuwa cikin fargaba da tsoro, kallon ta Ruƙayyan tayi "Wuta kuma innar mu?" ta faɗa cikin mamaki sannan ta sa hannunta da zummar sauƙo da Ismaha Zainab daga bayanta itama ji tayi shokin ya jata da sauri ta ɗauke hannun nata "Ikon Allah" ta faɗa tana yarfe hannayenta, gashi ta gaji sosai da goyon da tayi asali ma ƙirjinta ne yake amsawa da wani irin nauyi."Innarmu na shiga uku" kalmar data faɗa kenan hawaye yana zubo mata daga cikin idanuwanta.
Dafe ƙirji Innar mu tayi "Kaddai kice min Innar su kamalu ne suka rabo ki da gidan ki yau ma?." kai ta girgiza tana hawaye, bakinta ta buɗe tana so ta faɗa mata matsalar da ta sami Ismaha Zainab amma kuma abin takaici da mamaki madadin haka sai ta ji harshenta na sarrafa maganar da ba ita tayi niyar faɗa ba "Ko kaɗan Innar mu da wasa Innar su kamalu ta shiga lamurra na to shari'a ce zata rabamu, ni yanzu banƙi aure na ya rabu ba a kan su rabani da sana'ar da na dogara da ita, dan wasu lokutan gara marar aure tana da pancin kai da yin duk abinda taga dama, amma nifa sai nafi wata uku ban ji labarin Idris ba ban kuma san a ina yake ba, a baki ne yake sanar dani yana zuwa Legas neman kuɗi, amma bani da hujja da shedar da zan kira hakan da gaske, idan ya tafi babu ɗan aike na gaisuwa balle nasa rai a kan zan samu saƙo daga gare shi, faɗa min ba dan sana'ar nan da nake ba ƙila da tuni na dawo gida da zama, taya zan yarda da tirjiya daga gare su bayan basu ɗauka sun bani ba." ta ƙarasa faɗar maganar cikin ɗacin zuciya da ƙunci wanda aƙalla ta daɗe tana danne hakan a ƙasan zuciyarta, amma koda wasa bata taɓa sha'awa da gigin sanar da wani ba balle kuma iyayenta, baki buɗe Innar mu take kallon ta cikin al'ajabi da tausayawa, koda wasa bata taɓa hasashe akwai ƙunci a cikin rayuwar Auren ɗiyar tata ba. Dan babu wanda za yace yau gashi sun zauna sun tatattauna matsalar gidan ta da shi, asali ma kullum cikin yaba daɗin zaman gidan take.Hannunta taja ta zaunar da ita a kan tabarma kana taci gaba da kallon ta "Kina so kice min Idirisu baya baki wadataccan kuɗi idan zai yi tafiya?" Kallon Innar mu take tana son tuna abinda ta faɗa amma ta gaza tunawa "Tambayar ki nake kin min shuru?"
Kai ta fara girgizawa tana in-ina "A'a ba haka nace ba, wanda zai wadace ni har ya dawo ne baya bani." baki ta buge mata cikin fushi da jin haushi "Ƙarya kike min, kina so ne ki kare mijinki, bayan kin fara karanto matsalar sa, duk tsawon wannan lokacin kina zaman haƙuri amma ana miki kallon kitse har ana yada mana magana, ashe zaman ci da kanki kike yi, to wallahi bazan lamunci hakan ba bari Baban ku ya shigo."Dai-dai lokacin ya shigo yana gimtsa fuska alamun yaji duk abun da suke tattaunawa "Yauwa Alhamdulillah gara da ka shigo a wannan lokacin, ashe Ruƙayya nan shashasha muka ajiye, duk tsawon lokacin nan zaman ci da kai take amma bata taɓa faɗar hakan ba sai yau, da Allah yasa zanji, wata ƙila saƙar zuci take ta fito fili, to yasin Allah bazan yarda ba dole a sake zama tsakanin mu da Idirisu da iyayen sa da suka hana tamu ɗiyar shan ruwa."
Kallon ta yake a lalace kafin ya ƙara gimtsa fuska ya kai kallonsa ga Ruƙayya "Da gaske ne abin da Innar ku take faɗa?"
Kai ta girgiza sannan ta gyaɗa kamar ƙadangare, "Baki zaki buɗe ki masa bayani, kin zauna kina cutar kanki a aikin banza." Innar mu ta faɗa kamar ta buge ta.
Hannu ya ɗaga mataa "Ya isa haka Ballu" ya faɗa cikin tsawa da hargowa, shuru tayi tana muzurai sannan ya sake juyawa ga Ruƙayya "Na ɗauka ke mai hankali ce ai da naga kin kame kanki baki taɓa kawo mana ƙara ko suka akan mijinki ba, ashe ke sakarya ce da kike ƙoƙarin butulcewa ni'imar da Allah ya miki, idan mijin ki baya sauƙe miki nauyin da yake kansa hakan da mi ya rage ki? Asali ma Allah ya baki wata hanya ta samu ne da rufawa kai asiri, tunda ya saka miki nasibi a cikin sana'ar ki, dan haka ki tashi ki koma gidan ki kar na ƙara ganin baƙar ƙafarki da sunan kin kawo ƙarar mijin ki, idan kuma kika kuskura kika kaso auren ki to sai dai ki nemi wani sabon Uban amma fa ba ni ba."
Yana ƙarasa faɗar haka ya dira mata tsawa wanda ta sata miƙewa da sauri ta nufi waje "Haba Baban su ya zaka yanke irin wannan hukuncin haka ba tare da kayi bincike ba, wata harara ya wurga mata kafin nan ya juyo da kallonsa saitin ta "Nasan ke kike ƙoƙarin hana yarinya ta kwanciyar hankali a gidan ta, to bazan lamunta ba ko kaɗan, tunda bata nema ta rasa ba a gidan ta mi zai sa ta ɗaga hankalinta, wasu ma da mazajan nasu a gari amma basu ɗauki nauyin suba kuma basu da sana'ar da zasu riƙe kansu, su wannan suce ma Allah mi?" kai ta sunkuyar ƙasa maganar sa akwai alamun gaskiya "Haka ne malam"
"To kinga ita bata kawo mana matsalar ta a kan tana cikin damuwa ba, yau ɗin ma idan ki ka bibiya ba wannan ne ya kawo taba, tunda dana tambaye ta shuru tayi."
"Tabbas da alama bata shirya faɗa ba." Innar mu ta faɗa tana murmushi a ranta tana jinjina ma yarinyar tata da fatan Allah ya cigaba da kare ta da sana'arta.
A nan ya cigaba da kwantar mata da hankali da bata baki dan yasan soyayyar dake tsakanin su da Ruƙayya zai yi wuya idan bata saka abun azuciyarta ba..******
Tunda ta fita a gidan take tunanin mi ta faɗa haka? abinda ya kaita daban wanda ta faɗa daban, mi hakan yake nufi ne?
Turuss taja ta tsaya ganin mutum a zaune a tsakar gidan, cikin mamaki ta murza ido tana kallon sa "IDRISS" shi ma kallon ta yake cikin fuskarsa da babu burbuɗin rahma "Daga Ina kike?" tambayar daya watso mata yana ƙara tamke fuska kenan, sororo tayi tana kallon sa cikin mamaki baki buɗe.🥀🥀🥀🥀🥀
#IsmuhaZainab
#cmnts and share
#NWA
#Da amana🤝©Um Nass
![](https://img.wattpad.com/cover/166166065-288-k414201.jpg)
YOU ARE READING
ISMUHA ZAINAB Completed
AventuraAbubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga...