Bismillahir rahmanir Rahim
[Sun,sep 15]; ameera madobi
Sakkowa ta kenan daga gado, sakamakon hayanir gidan mu Daya Saba tashina daga bacci, indai Allah yasa asuba tayi, ko mutum naso ko bayason hayaniya saiya tashe shi.har ya riga ya zama daily routine din gidan. A kullum ina tunanin shin wai gidan mune ake yawan fadace fadace Dan muna da yawa koko de haka ce take faruwa a ko wani gidan yawa.Muryan hajiyata ne ya dawo Dani daga dogon duniyar tunanin Dana shiga tana cewa iman , lokacin sallah yayi , na amsa da cewa gani Nan hajiya, bayan nayi alwala nayi sallah,na zauna yin azkar sai wajen 6:30na tashi, naje gaida hajiyata, daganan na wuce sassan babana, Dan indai babana yaji sallama da sassafe tohmm yasan tabbasa nice, Dan ko matan sa basa yin sammako zuwa gaida shi ansha Case a Kan zuwa danake yi gaida shi Amma an gaji an kyale ni.
Asslaamu alaikum" waalaykumussalam, Iman kece . Eh baba nice " Ina kwana , " lafiya kalau , kin tashi lafiya? Lafiya kalau Baba . Ya kike , komai de lafiya ko? Eh duk lafiya To Allah ya Miki albarka ya Baki miji na gari kiyi aure , kinji mamar Babata. Ameen Baba nagode da adduarka , a kullum ina alfahari da kasancewar ka mahaifi a gareni. Kaman yanda nake alfahari dake a matsayin yata. Allah ya kawo miki
dauwamammen haske a rayuwanki, Allah ya kawo miki sabuwar rayuwan da nake Miki fata a kullum Mai dauke da farin ciki mamana, Allah ya baki ilimi Mai amfani kaman yadda kike fata kullum, adduan da baba ke min a kullum kenan, Dan harga Allah a cikin yayan babana, mu 17, babu Mai basa kulawa kaman yadda nake basa.Bayan futowata daga dakin baba, na wuce sashin hajiya, na fara gyarawa, bayan na gama wajen karfe 7:30, nayi wanka na fara shirin zuwa makarantar gwannatin dake Nan garinmu da nake koyarwa and it's keeping me busy from the chaos happening in our home each and every day.
Hajiya na wuce nikam. To iman a dawo lafiya Allah ya tsare, na wuce dakin yan matan gidanmu , duk suka gaisheni , kasancewarsu kanne na, daga Nan fita daga gidan a kofar gidan na hadu ba baba samaila da baba sufyanu na gaidasu ba wuce abuna da dare da kula da fuskokin su , ko sun amsa ko basu amsa ba.
Tun daga bakin harabar mkrnt na fara haduwa da malamai da dalibai , suka fara gaishe ni cikin girmamawa , Ina amsawa cikin kulawa.
Ina zuwa na shiga ss3, dan anan nake koyar dasu biology , bayan na gama da su, na dauka register , sakamakon nine form mistress dinsu.Bayan karfe 2pm , na tafi gida ,tun daga zauren gidan mu na fara jiyo mutan gidan a tsakar gda Suna hira Su na shewa Kamar gidan biki ,Ina zuwa nayi sallama , wasu sun amsa wasu gulmace a cikin su .
Suna "aikin kenan daga zuwa koyarwa boko da safe, sai islamiya da yamma ,shine kadai abunda ta iya, maimakon yanzu da yakamata ace tana gidan mijinta da yaranta, amma ta tsaya tallan kanta a Allah dai ya kyauta wannan abun wallahi.
Kasancewar na Saba jin irin mgngun su abun bai dame ni ba, na manna musu hauka kaman ko yaushe nakama hanyar dakin hajiyata,Wannan kenan•
Shin wai Mai dalin da yasa suke mata wannan mummunan furuchin???
Wacece ita iman? Mai asalin sunanta??•••••••••••••••••••••••
Assalamualaikum warahmadullahi wa barkatuhu
Sunana Halima Sani Madobi
Dafatan kowa yana cikin koshin lafiya
Am here with a mind blowing Novel me Suna" Sabuwar Rayuwa" It's all about a Lady trying to find love,and a dwelling peace in her life.Its all about love, destiny, and fate. Don't Miss it
••••••••••••••••••••••
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......