Page 36

263 14 1
                                    

Da asuba , Ahmad ya tashi ,ya wuce dakin iman yayi knocking ,ta tashi tayi sallah be jira amsanta ba ,ya wuce ta amsa ko bata amsa ba ohooo
Shidai yayi gaba abunda (ni dariya suka bani ma 😂🤣😂🤣😂🤣😂)

Ita kuwa iman ,tana cikin bacci taji knoking din kofan , ta farka , Tasha darene yazo ta bude masa kofa ,Sai tayi banza dashi , Sai kuma ta duba wayanta yaga  lokacin sallah ya kusa kurewa, cikin sauri ta tashi ,ya wuce toilet .........

Bayan  tayi sallah tayi azkar ,ta wuce kitchen, tana ta tunanin me zata dafa masa ,
Gashi bata saba masa girki ita daya ba tare suke shawaran me zasu ci

Chan dai ta yanke shawaran
, tayi masa golden yam da liver sauce ,Sai kuma tea .

Sai wajen 8:30 ta gama aikinta

Ta wuce dakin tayi wanka ta shirya cikin riga da Wando na paskintan purple colour .

Futowa tayi takuma zama a palour tana charting gashi kuma ta kunna tv ,shuru Ahmad be futo ba
Sai da tayi 30min sanna ya futo shima ya shirya cikin kanan kaya yayi kyau Shima .

Sallama yayi a palour din , ta amsa sallamar sanna ta gaisheshi  ya amsa babu Yabo ba fallasa .
Kallonta yayi ,yaga tayi masa kyau ,Amma ya basar ,
Kallonta ya kuma yi a Karo na biyu yace"hada min  abinchi yunwa nake ji "
   Yanda yay maganar yana wani cin d'aci sai abin yabama Aysha dariya, tasaki murmushin daya bayyana jerarrun hakwaranta farare tas, batace dashi komaiba tanufi kichin.

      Bin bayanta yayi da kallo shima yana murmushi, yana kallon sanda tasaki murmushin d'azun, bayansa ya jingina da kujerar yajawo wayarsa
Ya Kira mubarak ,Babu dad'ewa yad'aga, suka gaisa,
maganar tafiyansu da zasuyi zuwa Dubai dakko kayansu ,suna shawaran nan da kwana uku ,zasu tafi .
Iman duk yana tsaye tana jinsa , yana shawaran tafiya Amma bai Sanar da ita ba uhmmm su iman manya , yi tayi kaman bata San yayi wani waya ba balle kuma taji me yake cewa.......

Abincin tahad'a masa, yanda take komanta cikin nutsuwa da Jan aji sai ta burge ya Ahmad , harya shagala da kallonta tun yana waya da mubarak , harga ALLAH yanson mace mai nutsuwa,

Sai magana take masa, tagama, amma yana wata duniyar, cikin mamaki iman  tace, "naga ta kaina, me yake tunani ohoooo ?, karma kaci abinchin , Kai ya dama "

   Karaf sai a kunnensa, ya fesar da iskar bakinsa, sannan yakamo hannunta ya zaunar kan kujerar dake kusadashi, "Khadija ! Kalleni nan"
Gaban iman yayi mugun bugawa Ahmad tun farko baya kiran sunanta ,karde yaji me tace aiko data shiga uku ......

Babu musu iman  ta kallesa, amma bazata iya jure kallon tsakkiyar idonsaba, saboda kwarjinin dake cikinsu Na kamala da nutsuwa, tajanye idanunta akansa, amma dukkan hankalinta na kansa.

"Yaushe na fara wasa dake ne ?"cewar Ahmad cikin dakewa , ya koma Ahmad dinsa na daaaaa
"Lahhh nifa bance kana wasa dani ba "cewar iman kaman zatayi kuka ,murya na rawa ,gata da mugun tsoro
"Ya akayi kika rainani "
"Wallahi ban raina Ka ba "
"Tohmm mene kenan kika fada yanxu "
"Kayi hakuri Dan Allah,bazan Kara na Insha Allah "ta fada cikin sanyin murya da muryan nadama ,da shagwaba
Shuru yayi baice mata Komai ba
Karacewa tayi "Dan Allah nisful qalb kayi hakuri " ta fada cikin shagwaba tana kama hannunsa .
  Idanunsa ya lumshe, batareda da sake tankawaba yagyara zamansa, abincin yad'iba yakai bakinsa, lumshe ido yayi Dan dad'i.

Iman ganin yayi Banza da ita yasa tayi maza ta amsa fork din , ta fara basa a baki , Sai kuma ta basa tausayi ,tana bashi yana amsa harya koshi sanna itama ya bata taci , bayan sun gama ta kwashe  kwanunkan ta Kai kitchen .....
Shi kuma Ahmad ya koma palour , ya kunna tv ,ya kunna kallon kallo .....

~~~~~~~~~~~~~~~
Iman tana futowa daga kitchen itama palour ta wuce Direct, chanza Tasha daga kallon kwallo zuwa Zee world ,so take ta kalla silver lining , jiya tayi missing bata kalla ba ,

Murmushi tayi ta kalla ya Ahmad ,ita wai ta rama abunda ya mata kwanaki , shi kuwa gogan nata ko a fuska bai nuna ba
Ita dariya ma ta  bashi .
Zuwa tayi ta zauna kusa dashi ta daura kanta a cinyarsa ........ 🤫
Yatsun hannunta ta dauka yana wasa dasu

Maida hankalinsu sukayi a film din ,
Shuru babu abunda ke tashi sai karan tv din ,
Gaskiya film din ya basu tausayi , ishaaa da eraaah sun basu tausayi ,sunsha wahala a orphanage din
.
Iman sanda tayi kwalla , saboda tausayi
Shi kanshi Ahmad jikinshi yayi sanyi .........
Ni kaina sun bani tausayi , har ya kai da bazan iya kawo muku wani rahoto ba😭🤪.

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now