Mommy da dady shigewa sukayi ciki Sai auta itama ta wuce tayi wanka
Iman da Ahmad kawia aka bari , mota suka wuce suka kwaso kayan abinchi suka jera a dinning ,Kiran sallah aka fara
Daddy ya futo suka wuce masallachi da AhmadIman ta mike ta shiga dakin su Maryam , nan taga auta wai itama ta girma ta dawo dakin adda Maryam
Alwala tayi , ta sakawa auta hijab
Sukayi sallahBayan sun idar ne , Suka futo ,
A nan suna tarar da mommy ta futo ta shirya cikin Holland viluco dinta , tayi kyau sosia kaman sarauniya .Gaisuwa aka sake yi , Sai kuma su ahmad suka dawo
Iman tace "mommy muje kuci abinchi , nasan kuna jin yunwa",
Kafun iman ta gama magana
Auta tayi charab tace "Wallahi adda kaman kinsan yunwa nake ji "Dariya mommy tayi tace "muje tohmm"
Dinning suka tafi gaba dayansu
Kowa yaja kujera ya zauneIman zama tayi tsakiyar mommy da auta .
Iman ta tashi zata serving dinsu ,auta ta Riga mikewa tace " ita zatayi serving nasu din"Fara bude warmers din tayi taga tuwo ,aiko ta Wani kwabe fuska kaman zatayi kuka ,Saita bude dayan Miyane a cikin wani kamshi mai mugun dadi ke tashi daji ba sai ance maka miyan ciki zai yi dadi ba, wata warmer din ta bude taga jalof din macroni, cikin murna ta bude na papper chicken din ,ta dauki serving spoon ta fara serving dinsu daya bayan daya, mommy da iman ne Kawai suka ce tuwo ,dady da Ahmad macroni suka ci .
Babu abunda ke tashi sai karan spoon .
Gaskiya abinchin ya tafi dasu sosia sosai ,gaskiya mommy taji dadi sosai sosia
Dady ne ya fara Santi ,yake cema "mommy wai Allah tazo taci macroni kar'a bata labari" , itama tace "yazo yaci tuwo kar a basa labari "
Dady yace "shiyasa har Ahmad yayi kiba" haka dai suka ta Tonan Ahmad da iman .Ba su suka bar gidan ba Sai karfe 9
Gidan malam suka shiga sukata fira Sai 10:30 suka wuce gida~~~~~~~~~~~~~~~~
Bayan sun koma gidan ,kowa yayi wanka ya shirya cikin kayan baccinsa ,
Ahmad ya samu iman yake fada mata cewar "wifey zayi tafiya zuwa Dubai ,Jibi "
Kallonsa tayi da wani irin expression tace "tafi kuma qalbee ?"ta fashe da kukaRasa wa zaiyi mata bayani yayi , ya rasa me zaice mata haka ta ringa lallashinta
Yana cema mata "bazai dade ba ,kayansu kawai zasu dakko "(daman tana jiransa yana shirin tafiya bai gaya mata ba )
Duk da haka taki yarda .
Magana ya fara fada mata a kunne
Nima Banji me take cemata ba , kawai dariya naga ta fara ,
Daga nan kuma naga sun kwauce hanya ,
(Sim sim na wuce na basu waje 😏)*BAYAN KWANA DAYA*
Iman ce ke hada musu kaya , saura 1hour su tafi ,
Ita gidan mommy zata tafi har Sai Ahmad ya dawo .
Tana shirya kaya duk cikin ta a mace ,kaman mara laka ,shi kuma ahmad yaje Nemo wasu takaddu a dakinsa ,
Lokacin da ya dawo har Iman ta gama hada kayan .
A bakin gado ya sameta tayi uban tagumi , shima karfin hali kawia yake yi.Zama yayi a gefenta ya rumgumeta , zata masa kuka ya hada bakinsu waje daya😱(Kai shi ahmad dinan zai iya makantar da mutum )
Kissing dinta yayi tayi sanda ya gaji dan kashi ya saketa ,
Wanka suka shiga sukayi ,suka shirya ,
Ahmad ya futo musu da kaya ya saka a booth ,
Suka kashe duk abunda ya Kamata .
Suka wuce gidan daddy🚙🚙.A chan suka samu mubarak , ba wani sallama ahmad sukayi da iman 😭😭 ba daddy yace su wuce ya Kaisu , auta taso raka su airport din , daddy yace daga nan kasuwa zai wuce 😔.
Maganar ido kawia sukayi ahmad ya wuce😢.
Iman daurawa kawia takeyi , mommy ganin iman duk ta damu Sai ta ringa mata fira har Iman ta saki suka tayin fira .
Daga fitan su dady , gidan malam sukaje suka masa sallama , sunsha addua wajen malam da umma sanna suka wuce 🚘 ...................

YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......