Page 25

304 22 2
                                    

Kida ne tashi ,mutane sai rawa suke tayi ,daga gani bikin ya musu dadi ,kasancewa umma tana aurar da jikan karshe ,yan unguwa da abokan arziki sun cika gidan .
Iman na hango taci kwalliya cikin wani shegen lace fari  da touch din dark purple,an mata wani hadadden dauri da head din purple,Sai  takalmin purple yana da tsoho Amma ba Chan ba .
Ga lallen ta sai sheki yake kaman yanxu akayi,itama kanta ji take kaman ba ita ba
Gaskiya babu karya iman tayi kyau sosai,
Tana zaune cikin mutane sai fara'a take
Wayanta ne yayi Karan shigowan sako .shiru tayi tana nazarin waye ya Zai tura mata sako kuma, budewa tayi sai taga number ba suna,da kaman bazata bude ba
Sai dai wata zuciyar tace bude *Alhamdullah ,finally kin zama mata ta , congratulations mrs Ahmad Bello*
Shiru tayi ,jikinta yayi sanyi ,ta fara tunanin waye Ahmad din ,Allah sarki ,dama Mai suna ahmad ta aura.
Tsabar rudewa ta rasa wani Ahmad kenan (kunsan idan mutum na cikin wani hali rasa tunanin sa yake)
Tana cikin wanna tunanin mummy nurse tazo ta jata,suka shiga filin rawa .
Na wajen  ne na hango hajiya umma ,itama tayi kyau ,atamfarta Holland ,tayi kyau sosai
Sun sha rawa har sungaji
///////////////
Su malam ne a kofar gida da mutane cike ,sun gama daurin auren Maryam ,kofar gida ya gama cika sosai sosai.

Daman ance  musu Da an  daura aure babu abinda zaa jira zaa wuce da amare dakunansu, magana aka ma iman cewar iyayen na nakiranta, da sauri anty nurse tace tsaya ki canza kaya tukun wata Holland mai kyau da tsada aka fiddo mata nan da nan ta canza ta zura wanda aka daukomata, Sun kamata sosai kuma  tayi kyau  abunta, sake mata kwalliya akayi da turaruka masu kamshi, aka lullube mata fuska suka fita,

Farko gun malam aka fara kaita ,yata shi mata albarka sosai ,Dan ba ko wace yarinya bace a wanan zamanin zaa masa aure Baisan mijin ba kuma ya yarda,sanan yayi mata nasiha ,Mai Ratsa jiki ,

sannan aka fara bin Yayyen mamanta  kowa saida yamata nasiha sosai sannan daga karshe aka kaita gun babanta,Wanda ya buyo su malam Dan halattar daurin auren Maryam , nasiha yamata mai tsarajiki jinkintane yayi sanyi takara volume din kukanta  shima babanta daurewa kawai yake, Amman tausayi da wata sabuwar soyayyar iman ke ratsa masa zuciya, saida ya lallasheta sosai sannan suka fita tana kuka kamar ranta ze fita don ji take kamar zaa rabata da iyayen ta.

Gun umma  aka kaita sukayi sallamar karshe, iman rungumeta tayi tana kuka sosai kamar zata koma cikin ta, hakan yasa itama tafara kwalla, dakayar aka kwakule iman daga jikin umma  (Dan tana ganin umma kaman hajiyarta ,akayi waje da ita zuwa Inda yan daukar Amarya suka jera mota, acikin motar da tafi kowace kyau aka sakata daga gefe yafendo rabo ce ,ya yar  mahaifinta tace dakuma yayar hajiyarta  mummy barrister babu dade aka hanya zuwa gidan iman.

HAR suka sauka kuka take don alokacin idonta ya rune yako ma ja sosai, bude mata kofa kwanwar maifiyarta tayi tafito ahankali, suka kamata mata hannu suka nufi kofar gidan, tsayawa suka aka ce mata shiga da kafar damar tareda bismillah hakan tayi kamar yarda akace,  suka ce  Allah y sa kin shiga a sa'a,

Falon suka shiga wanda yake tatul da mutane yan tarbar Amarya  kanta a rufe, yan rakiyar amarya na take mata baya,

Wata uwar buda  aka sa ki nan da nan gida ya kacame da buda , Ana murnar zuwan amarya,yayar  mahaifiyarta ce tace inane dakin, nuna musu akayi suka wuce da ita direct,

Nan da aka cikasu da abinci kala da drinks aka hau ci, ahaka suka gama bikinsu dare nayi kowa yafara kama gaban sa , nasiha sosai aka sake mata ita kuma taciga ba aikin kuka.

Kamar wajen karfe Tara kowa ya watse tamike tashiga toilet Alwala tayi, tagabatar da sallar isha'i, takoma kan gado ta Maida lullubinta,

Tana nan zaune shiru har ten Ango baishigo gashi tafara jin tsoro, bata gama tunani ba taji alamar bude gate, dafe kurinta tayi dake bugawa da sauri nan da nan tsoro yashigeta,

Ahmad ne da Mubarak suka shigo, Dan tsayawa Mubarak yayi tareda cewa ni ba saina shiga ba karba, ya mika masa ledar dake hannunsa, ya kara masa nasiha tareda masa sallama.

Kulle gidan yayi bayan Ahmad yafita yanufi hanyar dakin Iman shima gaban sa na fadawa, kaitsaye yashiga dakin tareda sallama, zaune yaganta kan gado ta kundun dune, zama yayi kan gadon shima tareda aje ledar a gefe,

Ahankali ya matsa tareda mika hannunsa zuwa Inda take, Jim alamar motsin hannun mutum yasa takara tsorota sosai jikinta na rawa, ahankali ya yaye mayafin ta tareda kallon kyakkywawar fuskar ta data sha kuka, kura mata ido yayi ganin Tara masa kyau da kwarjini, dagowar dazatayi suka hado da Ahmad Dan zaro ido tayi alamar mamaki tareda kura masa nata manyan idanun, kallon kallon suka shiga yi kowa da abunda ke zuciyarsa..........
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Jamaa yau ga Ahmad da iman a matsayin ma'aurta.
Shin ya zamansu zai kasance ????

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now