page 3

659 28 0
                                    

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

G.W.F

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS WE ARE THE BEST AMONG THE REST

  Dawowa wata daga makarnta kenan duk na gaji, saboda ranar da akeyi sosai, ga yunwa na damuna , zuwa na gida kenan naji hayaniyar yan  gidan kaman ana biki,nan take naji kaina na ciwo , narasa yanda zanyi  na saba da halin yan gidanmu,  nace Allah ya kyauta,na wuce sassin hajiyata,ina zuwa na tarar tana karatun novel, muka gaisa ,tace mun ya aiki,nace mata hajiya yunwa nake ji
tace ankai min abinchi daki , ai kuwa Ina zuwa daki naci abinchi, na kwanta . Wani nannauyan bacci ya dauke ni
Cikin bacci naji ana tashina, Ina bude idona Naga hajiyata ce, tace iman ki tashi kiyi sallah sanna babanki Yana nemanki Wai kinyi bako,
sanda na kusan en muntuna Ina tununin Kiran me baba kemu ,haka naje  nayi alwala, sannan nayi sallah, haka na zauna tunanin Kiran me baba yake mun Allah yasa dai lafiya , haka Nan naji gabana Yana ta faduwa,
Chan naji hajiya na cewa halan kin manta babanki na jiranki,nace hajiya gani Nan zuwa,
nan na tashi naje na wanko fuskata , na saka hijab Dina har kasa,nadan fesa turare kadan, Dan d'abiatace bana futa kacha kacha.
na  kama hanyar shassen babana, a tsakar gida naji matar baffa ardo tana gulmana, tana cewa uwar gidan babana Allah yasa wanan ma yace  ya fasa ,Dan na gama dallah a titi, wai wa zai aure ni,
anan take naji hawaye sun tarun mun a ido, naji kaman na fasa ihu a wajen, amma a haka na danne zuciyata,na lallasheta . 
Kawai sai nayi musu murmushi , na gaishesu , saka amsa  cikin tsarguwa,
A haka na wuce su na tafi,
Ina zuwa harabar sashen Naga babana , na gaisheshi  ya amsa cikin sakin fuska,ai a take naji duk baccin Raina duk ya tafi, Dan ba karamin so nake ma babana, sai na cewa babana, hajiya tace kana menana, Allah yasa lafiya ,
sai yace lafiya mamana, dama baffanki ne ardo , yace wani abokinsa ,zaizo ya gan ki, nayi murmushin takaichi, nace toh babana, Allah yasa a dace, yasamin albarka  Kamar yadda yadda yadda saba ,
nayi Masa sallama na nufi sassen baffa ardo, Dan nasan Nan zangansa,Dan da kunya na tambaye babana,
nan na kama hanyar  da zai sadani da palon baffa ,
aikuwa a kofar kawai Naga wasu manyar takalma Suna min sannu da zuwa, harga Allah girman takalman ne suka bani dariya,
😂😂, haka na tsaya nadan dara ,kafin nayi sallama a kofar falon , na shiga tare da sallama , aikuwa Ashe banga abun dariya tukunnan ba , amsan sallaman ma abun dariya ne Dan muryansa abun dariya ne, shi kanshi ma abun dariyane ne,  haka na danne na gaishe shi, ya amsa, sai wani kallon sama da kasa yake mun(irin mutum yaje siyan kaya, Yana bubawa tsab , kafun ya siya),
kawai sai ji nayi wani dariya , har ga Allah ni tsoro ya bani, Dan babu alaman birgewa ga dariyansa, sai ji nayi yace ,babu laifi,
Aikuwa na dago kaina na dubesa da kyau, mutum ne dai babba gashi da tsawo, bakikkirin sosai, ga ido red😒, banji Yana da hakora Dan bakin yayi red sosai.
Ban Kara tsinkewa da alamarinsa ba , sanda naji Yana cewa, shi sunansa alhaji labaran, Ina da mata hudu,da yara 23, Amma idan yaga wacce tayimun
, sai na sake Daya daga cikin matana , haba abun yayi mugun bani dariya, haka naringa dariya harda rike ciki,( oho ni Iman, Wai ni zaa ce zan aura wannan mutum, harda cewa zai sake wata daga cikin matansa ya aureni, uhmnnn da degree Dina ma,ko namasa kama da kalansa uhmnnn, Amma sai yau Kara yarda baffa ardo da matansa basa kaunata sosai,Amma babu komai lokacinsu ne) haba daga dariya , sai ya koma kuka😭😭
Shi kuwa alhaji labaran ya tsaya kaman poster Yana kallon na,

Haka nan naji duk na Raina kaina narasa ya zanyi, a haka zuciyata ta bani shawaran kawai na futa na bar wajen
Ai kuwa ba tare dana Kara kallon inda yake ba nabar palon, kawai tsintar kaina nayi da futa waje ,sai kawai nayi hanyar gidan hamma Mahmud ( danshi baa gidan yake ba, baya son hayaniya), Ina tafiya ne , Amma bansan me nake ciki ba,a haka naje gidan hamma,sallama ma kasa yi nayi, sai kawai na fashe da Kuma Mai karfi, Dan banana cikin hayyacina

Wanna kenan.

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now