Page 30

292 15 0
                                    

Ahmad tashi kawai yayi yaji kiran sallah azahar baisan yayi bacci ba, cikin hanzari ya wuce dakin iman ya duba lafiyarta ,
Aiko itama ya sameta tana bacci buga  kofar da yayi ne yasa ta tashi da sauri tana salati ganin babu abunda tayi a gidanta babu shara babu wanke wanke

Zama yayi kusa da ita ya rungumota sanna yace  "wifey , kin tashi lafiya ? Ya jikin naki?"

Kasa tayi da Kai ,Dan har yanxu bata daina jin kunyarsa ba gashi abunda ya mata da safe ,
Gashi idan bata amsa ba zai iya bata wani kunya
Amsawa tayi "lafiya qlau ,y gajiyar biki?"

Kallonta yayi sanna yayi murmushi yace "Ai gajiyar biki yabi jiki ,Ke dai zaa tambaya ,tunda ga tsabaran aure kin samu harda ciwo " ya fada cikin Zolaya da neman magana

Aiko ba karamin kunya ya bama iman ba ,gashi ya rungumeta ,dole ta daura kanta bisa kirginsa ,shi kuwa tsabar neman magana so yake yaga fuskarta ,ita kuma tana dada nokewa( ni kuwa gefe na koma Ina kallonsu , dan abun ya girme kakata Halimatu)

~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Wajen 2:30 iman ne zaune a palour ta samu ta futo tayi dan gyare gyare tunda jikin alhamdullhi ,tana sanye da gown ne , royal blue ,gashi kayan yasha  aiki da stones golden , ta sanya hulan turban golden .

Zama tayi ta kunna tv tana kallon tashan Zee world wanda suke haska film din king of heart ❤️, tana kallon soyayyah sidat da roshni Sai uban murmushi takeyi , irin abun ya tafi da ita lol😂🤣😂🤣😂🤣😂

tana  cikin  kallo Ahmad ya futo , a shirinsa na kanan kaya na shan iska , yana sanye da three quarter na jeans black Sai ya saka top red colour Wanda aka rubuta *I love my girl* a jiki

Iman tana ganin ahmad tayi sauri ta mike taje ta dakko masa ruwa da fruit din data yanka .
Ruwan ya amsa yasha sannan ta ajje fruit din a center table

Zama yayi kusa da ita bece mata Komai ba , ya jawo bowl din fruit din yasha , ba tare da yace komai , ita kuma ta ci gaba da kallon series dinta , itama bata tanka masa ba

Ana gama king of heart kafun ya fara wani yayi maza ya chanza tashan ya maida sunna tv ,turo baki tayi Amma bata ce masa Komai ba . Shima ta wutsiyar ido ya kalleta Sai yayi murmushi kasa kasa dan shima yasan babu dadi mutum yana kallo a chanza masa tasha(who else ya tsani wannan abu ?, naga wani yace abu daya yake bata ma matansa rai dashi shine idan tana kallon ya chanza tasha 😂🤣😂🤣)

Aiko tafseer ake yi Dan haka sai ya maida hankalinsa wajen , daukan bowl din yayi yakai kitchen sanna ya zamo ya kwantar da kanshi saman  ciyarta .

Iman ta zaro idanu waje , Amma bata  Ce  Uffan ba ,shima bai tanka ba duk da yana ganin mamakinta ta gefen idanunsa

A haka suka zauna ,kusan 10 min
Sai ga Kira ya shigo wayan ahmad
Daga wayan yayi ganin mubarak ne.

Mubarak"Alhajin Allah, yanxu fisabillahi Ka samu yarinya mutane kowa ya  jika  shiri"

Ahmad "ehhh din , Ina ruwan ka , Kai da kaki zuwa?"

Mubarak" Ka kirani ka tambaye dalilin rashin zuwana"

Ahmad "Kai dallah ina na wani tuna da Kai , kar Allah yasa kazo "

Mubarak" zakayi  bayani dalla dalla idan nazo ,Ashe ka zama shege  koh , zamu hade , anjima zamu zo da madam Insha Allah "

Ahmad "Allah ya kawo ku lafiya ,Amma ku ciwo abinchi daga gidan ,Dan babu Wanda zaisa Matana wahala , ayheeeee."

Mubarak" ehhh lalle gaye Ka samu waje ni Zaka cima fuska ,wanna ba maganar waya bace ,zanzo na sameka" cewar Mubarak tare da kashe wayan yana murmushi cikin Jin dadi yana murna abokinsa ya samu kwanciyar hankali

Shima ta wajen Ahmad din haka ya faru ,murmushi yayi ,tsakani da Allah yake son Mubarak

Ita iman da take jin firan nasu murmushi tayi
Tana shaawan kallan abokantakan nasu mai shaawa ,babu munafurchi babu ha'inchi da son zuciya

Kiyare kirayen sallah laasar ya saka suka tashi ,daga kallon tv din , iman Kafanta yayi tsami ,tayi niyar tashi taji ba zatayi iya ba , aiko ta koma ta zauna

Shi kuwa Ahmad kaman ya gane , yayi dariya yace dama matata Raguwa ce ,daukarta yayi gaba daya
Yayi daki da ita ................

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now