Yauwa Iman yanzu abunda nake so dake shine ki kwantar da hankalinki kibar komai a guri na kidena sama ranki damuwa in sha Allah ni zan tsaya Miki har sai su baffa Ardo sun fasa mugun nufin su a kanki, kinji ko?
" Eh Yaya naji
Allah ya albarka ce ki.......
Wait bari in dau waya" hello Baba sannu da huta wa .
Eh bari in zo yanxu,
ni zanje shago baba ya kirani sai kubari sai nadawo Dan muji abinda zece.
To Yaya sai ka dawo,
yauwa.
••••••••••••••••••••••••••••••••Assalamualaikum
Waalaykumusallam, Hamma kazo ne,
Eh baba nazo an wuni lafiya,
lafiya kalau , ya gidan ya amarya ta .
Duk suna lafiya baba duk suna gaishe ka .
Ahhh to Ina amsawa.
Daman Baba uhmm Daman Ina so ......
Yi magana Mana hamma.
"Daman Iman ce tazo gidana yau da wata magana wadda ni a gaskiya a matsayin ta na kanwata ban gamsu da zancen ba shine nace bari in same ka muyi maganar dan asamu a samo bakin zaren.
Eh to a gaskiya Nima da Baffanku Ardo yazo min da maganan banga mutumin ba Amma daga baya na duba Naga nima baya tsari na Amma kuma abunka da abun dangi ni bansan ya zaayi baAmma Baba ai kasan a tsarin gidannan ba a yi ma mace auren dole fa.
Eh hakane kam,
shiyasa na yanke shawarar ta tafi can gurin dangin uwarta kakaninta kenan Dan samun kwanciyar hankalinta Dan kaga ba abun ta zauna a gidan ka ba gudun magana ko?
Gaskiya kam baba yayi babu matsala
Shine kenan , dama kowa da tashi jarabawar , tunda ita mamana haka tata tazo Allah yasa ta cinyeta .Masha Allah baba, naji dadi sosai , shiyasa kullum nake alfahari da Kai a matsayin mahaifi, uba, abokin shawara
Allah ya Kara lafiya da nisan kwana, Allah ya Raba ka da makiya,Amin Hamma , Allah ya Kara hada kanku gaba Daya , Allah yasa ku gama da duniya lafiya.
Tohmm baba a huta lafiya zan karasa gida.
Tohhhh Allah ya tsare
Bissalam•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Assalamualaikum
Waalaykumusallam
Barka da zuwa hamma
Sannu dai Iman
Kinchi abinchi
Ehhh hamma naci, Ina ta Santi dama haka anty ummi ta iya girki, gaskiya zan dawo cin abinchi gidannan😁,Hhhhh, ai ummi ba baya ba , shi yasa duk inda naje bazan chi abinchi ba sai na dawo gida,
Ahhh gaskiya banga laifinka ba hamma
Sannu da zuwa baban heedaya
Yawwa sannu da zuwa , ya gida da aiki
Alhmdllh , ya babana ka sameshi lafiya??
Lafiya qlau yace a gaishe ku
Muna amsawa
Bismilla sakko kaci abinchi
Yawwa maman heedaya•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Yawwa iman munyi magana da babana
Kuma Masha Allah an samu mafita
Yanxu Zaki shirya ki tafi gida da daddare zakuyi maganaMasha Allah, hamma Allah ya saka da alkhairi, Allah yasa ka gama da iyaye lafiya, Allah ya raya su heedaya, Allah ya kawo masu albarka Kuma
Ameen iman
Kema Allah ya Baki miji na gari
Allah ya albarkanchi rayuwanki da karatunki
Allah yasa ki gama da iyaye lafiyaAmin hamma
Anty ummi sai anjima sai nazo cin abinchi dare😅😅
Hhhhh kice sai bayan wasu shekaru dai
Ke Dana sani
Sai kice anty ummi inanan zuwa amma naji ki shiru
Allah ya shiryeki
Sai anjima
A gaida Yan matana idan sun dawo makaranta
Zasuji•••••••••••••••••••••••••••••••••••
Ahmad Ahmad Ahmad Ahmad!!!!!!!!!
Naam hajiyaaaaaaaaaaaaaaa
Barka da asuba
An tashi lafiya ?
Lafiya qlau, ya gida
Lfy qlauDama alhaji ne yace Yana son ganinka wajen karfe 9am
Okhhh tohmm Allah ya kaimu
ka samu ka sakko cin abinchi da wuri
Babu damuwa hajiya Amma
Umma take yau abinchinta zanchi fahh
Ahhhh tohmm babu matsala kam ,
Damuwata kawai kachi abinchin
Tohmm babu damuwa insha Allah zanchi da yawa ma
Allah ya kaimuBarka da safe Yayaaa
Keeeee😏 Ina Kika je jiya Kika dawo wajen magrib
Yaya wallahi ba laifi na bane
Keeeeeee ya buga mata wata tsawa tambayar nayi laifin waye??, cewa nayi Ina kikaje jiyaHaba Nan da nan saiga hawaye ( tasan baya son yaga hawayen mace, asali ma Yana da fada,
Amma bai taba dukanta ba Dan shi baya dukan mata)Yaya wallahi da na dawo daga catering school, shine hajiya tace na biya na siyo mata kayan Miya a kasuwa, shine nayi dare
Uhmmmm sai kawai ya wuce abunsa( dama tunda tace hajiya am gama mgn)
Ya wuce daki abunsa
Dan Yana da abunyiTohmmm masu karatu
Waye Ahmad
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......