Cikin takunshi mai tattare da natsuwa ya kama handle din kofan ya bude,ai kuwa iman tana jin ya taba kofan ta zabura ta tashi zaune ,
Zaune take cikin wani coffee brown hijab,kayan bacci ne a kasan kayan baccin, riga da Wando masu kauri."Assalamu alaikum "cewar Ahmad,da yayi kokarin shigo da , wa irin kamshine ya mamaye dakin ,wani irin farin ciki ne yayi Mara musaltuwa ,
"Wa'alaykumus sallam"cewar iman murya na rawa
Kallonta yayi na kusan second biyu sanna yace mata "kinyi alwala"ya tambayeta
Daga Kai tayi ta kalle sa sanan tace "ehhh nayi "Tohmmm bismillah,
Mikewa tayi kaman wanda bata da laka Ajiki ,a sanyaye tace tohhhh,
Ya mike ya dakko sujud ,ya shinfidaJam'i ya jasu Raka'a biyu sanna ya dafa kanta yayi mata addua da addini ya umurceshi da yi, sannan ya Cigaba dayi ma iyayenshi da nata addua, harda su malam da suka yi sanadin auren .duk cikin harshen larabchi
Tashi yayi ya dakko masu al-qur'an , yace suyi karatu ,
Tambayarshi tayi cikin sanyin murya cewar daga Ina zasu fara ,
Sai yace daga Fatiha Insha Allah,
Haka suka fara karantawa , tun tana yi a hankali murya kasa kasa ,bata sanda muryan ta dago ba ,sanda suka karanta fatiha da bakara sanna yace ya isa ,gobe idan Allah ya yarda zasu ji gaba .Iman kuwa gaba daya natsu yazo mata ,duk wanna sanyin jikin ta Nemeshi ta rasa .(wallahi jama'a karatun alkur'an yana kawo natsu , wallahi ko ranki ne ya baci , kika dakko alqur'ani kika karanta ,zaki nema bacin rai ki rasa, plsss mu yawanta karanta alqur'ani, sannan mu koyawa 'ya'yanmu da kannenmu )
Bayan ya ajje alkur'ani ne ya juyo ya tsare ya da idanu ,sanna ya Cigaba da mata tambayoyi ,game da addini duk cikin harshen labarchi
Tabbasa Ahmad ya birgeta sosai duk da Bata ji mamakin ba ,saboda tasan Ahmad yana da ilimin addini sosai
Itama cikin harshen larabcin take amsawa, inda takeda rauni yakan tunatar da ita, daga k'arshe suka kuma rufewa da addu'a.Sannan yace mata idan islamiyan da take koyarwa sun gama secondary din zata ji gaba da zuwa islamiyya, tunda yaga tayi nisa sosai a ilimin addini, baikamata a dakushetaba.
Tamasa godiya cikin raunin murya, wadda tak'ara tsundumasa cikin wani yanayin shauk'i Na musamman.
Hamma ta fara ,
Kallonta Ahmad yayi sanna yace "mrs Ahmad aje a kwanta ,nasan akwai gajiyar biki"Mikewa tayi ta kwanta ba tare da ta cire hijab din ba ,shi kuwa ahmad bai kwanta ba ya Cigaba da addu'a
Sai wajen 12am ya muke ta tarar tayi bacci ya zare jallabiyan dake jikinsaSanna itama ya cire mata hijab din ,Dan bata San yamma cire ba ,saboda bacci ga gajiyar biki ma,Shima bacci yake ji sosai sosai
Waje ya samu nesa da ita ,ya kwanta nan da nan bacci yayi awan gaba da shi
Asuba na fari//////////////////////////
Kiran sallah farko iman ta farka, tana bude idonta ya sauka akan Ahmad da ke sharan bacci hankali kwance , shiru tayi tana mamaki wai yau gata matan aure,wai yau ita da kwana da Kato a daki daya 🤭😂😂,
Wai yau Khadija da ake mata gorin taki aure ,yau itace tayi aure,nanda danan sai ga hawaye tun suna zubowa a hankali har suka cika fuska ,ta ringa godewa Allah,tana hamdalah .Ganin tana bata lokaci ne yasa ta mike taje tayi alwala , sanna tazo ta tashe ahmad .
Tsare take a kanshi ,ta rasa ta yadda zatayi ta tashe shi shiru tayi tana kallon kyakwan fuskanshi ,
Jin shirun yayi yawa ne yace mata kar ki cinyewa daddy 'da mana ,wannan kallon haka fah
Turkashi dan ,da kasa zai bude da iman tasa ya bude ya shiga ,kunya ce ta tullubeta ta rasa yadda zatayi
Kawai juyawa tayi , ta Kabbara sallahShi kuwa ahmad wani mugun dariya ta bashi ,tun Karan bude bathroom ya tashi ,har ta futo idonshi biyu, da yayi niyar mikewa kawai ,Sai kawai yaga ta nufoshi shine yace bari yaga yadda zatayi . Daman yasan kasawa zatayi😂😂😂😂
Mikewa yayi ,yaje yayi alwala,ya tafi masallachi
Koda ya dawo dakinsa ya wuce ,ya kwanta dan bacci bai ishesa ba ,Itama ma iman tana gama azkar taje ta kwanta ,bata tashi ba sai wajen 9. Bayan ta mike ta gyara dakinta ,ta wuce palour ta gyara da kitchen,sannan ta wanke kayan abinchin da sukayi amfani dashi ,
Ta buda ko anyi refilling gas din,ai kuwa cikin saa taga anyi ,
Ta dakko pot ,ta wanke sanna ta daura black tea ,da Kayan kamshiWajen 10:30
Taji ana buga gida ,daidai da lokacin da gama shirinta kenan ,tayi wanka tasa wata material mai shegen kyau ,royal blue ,gashi tayi daurinta Mai kyau ,Sai tayi kaman yar Tsana 😂😂😂
Gashi sai bazan kamshi take ,ta futo a Amaryata tsaf(Dan kusan babu Wanda ya Kai amarya kyau ,balle idan tayi kwallaiya Mai kyau)
Mikewa tayi taje ta bude kofan
Ihsan ce kanwar Ahmad,"Lah anty iman ,dama kece amarya ya Ahmad,cewar ihsan cikin tsananin farin ciki Mara musaltuwa
"Auta ya Kiki,ya kika Baro mummy da dady?
Amsawa tayi tare da gaishe da iman din ,sannan ta mika mata basket din mai dauke da abinchi
"Ihsan ki shigo mana "cewar iman
"Chab mummy tace karna shigo ,na mika na taho ,kuma da driver nake .ki gaida yaya idan ya futo"cewar insan .
Kafun iman tace wani abu ihsan ta ruga da gudu ya wuce .Dariya iman din tayi sannan ta dauke basket din ta Kai dining area...............

YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......