Itama haka iman ba wani baccin kirki tayi ba sai tunane tunane take , rayuwanta na da ,har zuwa na yanxu take tunain ,ga wani mugun zazzabi ya dameta ,ta rasa yadda zatayi ,gashi babu magani .(ni kuma nace allah sarki iman daman haka aure yake)
Sai wajen karfe 3am wani mugun bacci ya dauke su a tashi kaman hadin baki .
Kiraye Kiraye sallah ne ta taga su daga bacci ,Ahmad yayi sauri ya mike yaje yayo alwala Dan lokaci ya Kure masa ,Sannan ya tashe iman ,a tunainsa tana bacciIman tana mikewa wani irin jiri ya de beta ,
Har Ahmad ya kusa baki kofa yayi sauri yazo ya tallabeta ,wani irin sayyan ajiyar zuciya ya sauke ,ta rigada ta sadakar Zata jita a kasa ,
Shi kuwa gogan lumshe ido yayi ,da zaiyi magana tayi maza tace masa sallah ,zaunar da ita yayi a bakin gado ,yayi maza ya tafi masalachi .Haka dai ta lallaba taje tayi alwala ,tayi sallah da kar ,tayi azkar ,ta mike zata tashi ta karasa ,ga wani mugun baccin da take ji , babu yadda ta iya haka ta kwanta kan sallayan , wani mahaukacin bacci ya fizgeta
Shikuwa Ahmad yana dawowa daga masallachi yana tunanin iman , shi mene yasa ta yin jiri ne haka kodai bata da lafiya ne?
Duk hankalinsa ya tashi , yana shigowa dakin ya hangota kwance a bisa sallaya a kasa ,
Nan da nan hankalinsa ya kuma tashi , cikin Hanzari ya karasa wajenta ya taba jikinta yaji zafi , nan da nan kuma basa tausayi , daukarta yayi ya kwantar da iya a kan gado ya cire mata hijab din ,ya lullubeta da bargo
Sannan ya zauna a gefenta yana kallonta ,duk tausayinta ya lullubeshi , tunani ya fara yi me ya kamata yayi yanxu , Sai wani idea ya zo masa cewar yaje ya Nemo mata magani
Haka kuwa yayi cikin gaggawa ya wuce ya siyo mata maganiIman kuwa cikin baccinta taji karan bude gate da kuma karan mota,Sai ta fara tunani Ina ya Ahmad ya tafi da sassafen nan,ko wani abun ne ya faru😱
Sai kuma ta tuna a kasa ta kwanta ,waye kuma ya dawo da ita kan gado har da cire mata hijabSallamar ahmad ne ya dawo da iman daga tunanin da take ba tare da samo amsar ba .
Yana takowa yazo gabanta ita kuma tayi sauri ta rufe ido dan har yanxu kunyarsa take
Jikinta ta taba yaji how far temperature din ,yaji stil akwia zazzabin maganin ya ajje kan side drower ,ya wuce jin Ana knocking, mummy ce ta Aiko da abinci karba yayi ya are kan dining kitchen ya shiga ya dauko plate da cup abincin ya diba dede ya zuba akai ya koma ,
Ajiye plate din yayi akan drowern dake dakin taimakata yayi ta mike daga kwanciyar ta zaune da kar , tana Wani yatsine fuska irin na marasa lafiya ,A haka dai ya talllaba mata taje toilet tayi abunda zatayi sanna ta daura da yin brush , sanan ta futo ,
Zaune ta iske shi akan gado yana jiranta tafito
Wani irin matsyinacin murmushi yayi mata Wanda ba ita kadai ba nida da nake dakko muku rahoto sanda zuciyat ta tsinke tsatttttt.........Kasa tayi da kanta gabanta Sai faduwa yake ga wani shegen kunyarsa da mugun tsoronsa da takeyi
Takowa tayi a hankali har inda yake zaune bakin gado yana ta murmushi kaman an masa bishara da aljannna , wani mahaukacin sonta da Kaunar tane ke shige zuciyarsa , ji yake kaman ya maidata cikinsa Ka wai ya huta ,
Gaisheshi tayi cikin Jin kunya murya na rawa tace"good morning ya Ahmad "
Kallonta yayi yana mata wani kallo hade da kashe mata ido "Haba wifey , wani irin gaisuwa ce wannan Sai kace ana fada "
Dariya yayi sannan ya Cigaba da cewa"zuwa zakiyi kiyi hugging Dina kiyi mun peck sanna kice good morning bla bla bla........Tsungunar da kanta tayi irin taji kunya Sai kuma tayi murmushi ita Wannan moment din ya mata dadi (ni kuwa nace iman da sauran ki)
Riketa yayi ya zaunar da ita a bakin gado , ya dakko tea din zai bata , Amma Sai taki amsa ,
Shi kuwa sanin halin iman yasa ya wani hade fuska ,tana dago fuska da niyar ce masa bata son shan tea ,ya mata wani irinin Matsiyacin kallo
Ai nan da nan ta Hadiye maganarta ba tare da ta shirya baA hankali yadinga bata ta kauda Kai alamun ta koshi, maganin ya dauko ya balla yabata da kyar tashanye shi ajiye wa yayi yace tashi muje na miki wanka, kauda kai tayi kamar bata ji Me yace ba, daukar ta yayi tana wutsul wutsul da kafa akan ya sauketa Amman bai saurareta ba saida yasakata a bathtub, tass ya wanke ta ita kuwa har lokacin idonta a rufe tana mamakin rashin kunya irin na Ahmad,
Towel yasaka ya tsane mata jiki tass bawata kwalliya yayi mata ba don bai iya ba sai turare da saka mata da yar Riga Mara nauhi maidata yayi kan gadon tare da rufa mata blanket yana gamawa ya kalle ta tare da kashe mata ido daya kashe Kwan fitilal yayi yarage mata karfin Ac tare da cewa a huta lpia wifey.
Yana fita shima ya shiga ya dibo abinci yaci yana gamawa yayi wanka ya koma ya haye gado Amman be yi bacci sai tunani daya shiga......
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomansaIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......