🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟
G.W.F
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS WE ARE THE BEST AMONG THE REST
Wa nake gani kaman maman baba, ragowan mgnrs ya tsaya daidai lokacin Daya kalle fuskata, ya tabbatar ma kansa Ina cikin baban matsala ,
Ai a lokacin naji wani marayan kuka ya zomin ,
Hamma ya rasa ya zaiyi Dani kuwa
Matarsace kawai tayi kafin halin zuwa tana patting Dina
Sai chan yace mu zauna ,
yasa matarsa kawo min ruwan sanyi , aikam data kawo nasha naji sanyi sosai a Raina,
sai chan wajen 15min Muna zaune jugun kowa yana tunanin a ransa ,
sai tsintar muryan hamma nayi Yana kirana , Iman nasan abunda zai saki a damuwa ba karamin abun bane,
Dan Allah Kar ki boyemin komai, Allah sarki matan hamma akwai sanin ya kamata,
sai kawai tace bari taje ta duba abinchi(yawanchin mu mata
, Muna da irin wanan matsalan sosai , sai kaga wasu Allah Allah suke suji Mai matsalan , tsakin mijin ki da yan uwansa akwai sirri bada dole ne ki sani ba, watama sai ma mijin yace ki Basu waje zaki samu ki matsa, idan ya gadama ki sani fine da kanshi zai fada Miki)Iman!! Ya Kuma Kira a karo na biyu, na amsa masa
Yace Ina jinki
Aikam ba tare da wani tunani ba ko tsoro na basa lbr tun daga habaichin da ake mun har zuwa abunda baffa ardo yayi mun ,
Aikam abun yayi mugun Bata Masa Rai Kuma abun ya basa takaichi sosai , sai da ya kusan 10min kafun ya dauka waya ya Fara dailing numbern baba.
Ai kuwa baba Kamar jira yake yi ya dauka
Assalamualaikum babana
Waalaikumussalam
Barka da warhaka dafatan ka wuni lafiya
Lafiya qlau
Allah ya karama baban Aisha da Halima lafiya
Allah ya Kara ma baban mamansa tsawon kwana , Allah ya baka saa a rayuwa
Murmushi baba yayi kaman hamma na gabansa yace Amin
Sai yace baba Dan Allah idan babu damuwa inason mgn dai
Amma Dan Allah baba baa gida ba
Sai baba yace lafiya koh
Sai hamma yace lafiya qlau baba
Okhhh ka sameni a shagon cikin unguwa
Angama baban rukayyah 😁••••••••••••••••••••••••••••
Tafiya sukeyi hankalinsu kwance sai musu sukeyi, my man na fada maka bayan aure na , bazan dunga jerawa da Kai ba,
Hhhhh Wai aure,
bayan an daura maka ciwon Kai da wahala dai bazan dunga shiga ciki ba ,
Kai Dan iskane , wallahi aure rahamane fah, bari kaga nayi aure uhmm a dai yi shiru
Nifa ba auren ne baza iya ba, aaaa kawai takuran ne bana so ,
Kaine dai kasan takura .
Mtwsssss Kar ka dameni fah da wani maganar aure tunda kai baka da abunyi ,
Ni banma yi tunanin zaka Kara yin wanan haukan Wai soyayya, bayan chin amanar da rahma tayi maka wallahi ka shiga uku banza😏.
ina tunanin next week zani Dubai , kayan shagunana sunyi kasa,
Uhmm Nima Ina son zuwa amma bana son yin tafiya biyu, bikin maryam ya kusa Kuma hajiya tace ni zanje siyayan, Dan haka idan sun shirya na tafi gaba Daya,
ayyah Allah ya kaimu lafiya,
Mtswwwww ka sani dogon surutu har kaina ya Fara ciwo.
Kaifa man matsalata da Kai kenan ba damar ayi mgn data wuci mintuna 10 sai kace kanka na ciwo, Allah ya kawo maka sauyin rayuwa,
Banza Ahmad yayi Masa, har Allah ya kaisu gida lafiya babu Wanda ya Kuma yi ma Dan uwansa mgn,
Dan mubarak yasan halin abokinsa sosai.
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomansIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......