Page 41

231 13 0
                                    

Doctor yana futo ya Mikewa daddy hannu suka gaisa ,Sai ya kalle Ahmad saura kadan ya tuntire da dariya , kawai ganin daddy ne yasa ya kwaleshi .

Dady ne yace "ya jikin khadijatun ?"
Murmushi doctor din yayi Dace ta samu sauki , stress ne ya mata yawa , gashi ba ita kadai bane , tana dauke da ciki na kwana 21 🙀🙀🙀,
Wayyo zokaga murna wajen mutane 3 nan ,daddy ,mommy da Ahmad . A ciki Sai a rasa waye wanda yafi murna a ciki . Shi kanshi likitan ya taya su farin ciki sosia

Ahmad kuwa , hawaye ne suka fara zoraro masa ( kunsan cikin fari 😅) Sai Maganar zuci yake yi "Allah Na Gode maka , Allah Alhamdullah, ya Allah Na Gode maka ,Allah ka bani mata ta gari , Allah Alhamdullah"
Hawaye ne suka Cigaba da zuba wai  shine za'a haifama d'a, gudan jininsa, wanda dole akakira sunan d'an ahad'a da nasa sunan, zaa kira yaron da Dan Ahmad Bello , wayyo Allah na , kaike bada k'yautar da ko kud'i ko mulki bazasu sayaba, kaike bada abinda babu wani mahaluki aduniya dake ikon bama mutum ko hanashi sai kai kad'ai ubangijin komai da kowa , ALHAMDULILLAH ,

الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتُ
Alhamdu lillaahil-lathee bini'matihi tatimmus-saalihaat.
Sai maimaitawa yake tayi

Mommy da daddy Sai kallonsa suke ,suna cikin farin ciki mara musaltuwa ,
Shikanshi Likita ya tayasu murna sosai ,

Kallon Ahmad yayi yace "malam kazo muje na rubuta maka magani a office Wanda zaa siyo mata ,yanxu an sa mata ruwa ,Sai gobe zaa sallameku idan babu damuwa "

Kai Ahmad ya girgiza masa Dan yanxu baya jin zai iya magana sosai sosai ,
Mommy ce tace "likita zamu iya ganin ta yanxu ?"
Answer yayi tare da wucewa office dinsa ,
Binsa Ahmad yayi ,suna zuwa doctor ya fara tonansa fada
Yana cewa "shegen kaya sanda Ka dirka mata ciki ,kana Ina ,Amma kazo kana mana hawayen karya😂🤣😂🤣"

Kallonsa ahmad yayi sama da kasa sannan yace "Kai dallah malam banda lokacin Ka , lafiyar mamata ce ya dameni ,yanxu "

"Gaskiya abokina na tayaka murna sosai sosai ,Wallahi nasan yadda kaji , balleni Shekara biyu da aure sanna muka samu karuwa,ranar duk Wanda yazo asibitin nan yasan ina cikin murna ,so congratulations nan da 8month da yan kwanaki  ka zama daddy Insha Allah "
Kai ya fara girgiza wa kaman na kadangare sanna yace" thanks so much dear ,gaskiya naji maka dadi sosai soasai ,Allah ya sauketa lafiya "
"Ameen"

Maganin ya fara rubuta mata sanna yace "Sai taci  abinchi sosai sosai ,kafun a bata maganin "

Sannan ya fada masa wasu dokokin , da zasu bi wajen ganin lafiyarta .

~~~~~~~~~~~~~~~
Dakin ya wuce ya ga iman ,nan ya tadda mommy da daddy suna zaune
Mommy ya kalla yace "mommy ga maganin an rubuta mata ,Amma Sai taci abinchi sosai zata sha "
Mikewa mommy tayi tace "bari nayi sauri ,naje na dakko abinchi kafun ta Tashi kuma nasan auta ta dawo ,Amma idan taga bana nan zata wuce gidan malam ne "

Daddy ne yace "ban takaddar naje na siyo magani ,zan wuce da mommy Ka kuma ka zauna anan kar ta tashi baka nan "

Amsawa yayi a kunyace ,sanna suka wuce

Kujera yaja ya zauna kusa da ita ,Sai kare mata kallo yake yi mamakin irin kyawu da farin da iman. tak'ara yakeyi, yakai hannu yana shafa sumar kanta ahankali, gashin gaban goshinta kwance luf-luf, cikin tsanaki yakebin dukkan illahirin jikinta da kallo, shi saiyagama kamar tad'an k'ara k'iba, ga fatarta harwani k'yalli takeyi, kirginta ya cicciko .
Jikinta ya taba yaji ,yayi dumi
Ya kusan 10 minutes yana kallonta sanna ta farka ,
Iman tabud'e idanu da kyar, ledan ruwan tabi da   kallo har k'arshe, ta lumshe ido tareda maida kallonta Kan mijinta  dake sallah, aranta tace ni iman  nice da kwanciyar  asibiti? Me ya faru dani ,yaushe aka kawo ni nan,Banta6a ciwon daya kwantar dani asibitiba, me ya faru aka kawo nan ,tayi tayi ta tuna ta kasa ,
yunk'ura tayi zata  tashi amma saida kasa, saboda jikinta babu kwari, ga wata makauniyar yunwar da take ji ,
Ahmad daya idar da sallah ta kalla tace "qalbee me nake yi a hospital ?"
Kallonta yayi cikin shauki da farin ciki mara musaltuwa yace....................................

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now