"Haba ke kuwa beauty , sai kiga wannan zankale luwan matanmu kice mata tsohowa haba de"cewar mubarak yana dariyar mugunta
" mtsweee, Wai beauty kake kiranta??
Bayan tana cewa Matar mu tsohowa , ai itace kayi kama da tsohowa"cewar Ahmad harga Allah yaji haushin beauty din da Mubarak ya fada"Ahayye yarinya Kinga ina da gata" cewar umma tana min gwalo
"Uhm uhmmm uhmmm" cewar malam ya futo daga daki yana gyaran murya
"Ai gaskiya ta fada " cewar malam
"Ehhh mana ai ta tsufa, inba haka ta tashi muyi gudu aga Wanda yafi karfi a jiki"cewar iman, tana murmushi
" ahmadudu ,ka amso ma iman form din islamiyyan kuwa?" Cewar malam
"Aaa , amma na kiran shugaban makarantar yace muje kawai babu damuwa, yanxu su Maryam zasu tafi sai Mu tafi dare"
"Okhhh, babu damuwa, yar albarka tashi ki shirya koh"
"Insha Allah" nace na tashi naje na shirya
Ina zuwa daki naji muryan Maryam a tsakar gida ta shigo, tana cewa tayi latti sai munzo,
Haka na zauna ina kokarin goge kwallina , da dan janbakina , bayan na gama na tashi na daukko hijab dina pink, na dakko takaddun islamiyyana da nazo dasu,
na futo na tarardasu, suna musu , tsakanin malam da Mubarak dan sun saba su,"Iman kin futo " cewar umma
"Ehhh umma "
"Tohmmm Sai mun dawo" inji Ahmad ya fada yana kokarin tashi
Mubarak ne shima ya tashi yana cewa"da yake kashi na muku a gado shine bazaace nazo muje ba"
Nidai murmushi nayi shi kuma Ahmad ya hararesa
Muka kama hanya ,Mubarak sai damun Mu yake da surutu
Amma babu Wanda ya kulasa,
Shi Ahmad fushi yake yi dan yace min beauty,
Ni kuma murmushi kawai nake yiHaka muka Isa islamiyyan da yake babu nisa sosai
Mukayi sallama muka shiga office din shugaban makarantar"Malam barka da rana" cewar mubakar
"Barka dai malam mubakar , kayi wuyan gani tunda kukayi sauka baka kara zuwa islamiyyan nan ba" cewar malam
"Ayi hakuri malam""Ai gwanda kai da malam Ahmad"
"Ayi hakuri malam"cewar Ahmad
" malam dama kanwar Mu muka kawo gata nan "cewar mubakar yana nuna ni
" barka da rana"
"Barka dai"
"A ina kika tsaya a karatu?" Cewar malam yana tambayana
"Uhmm nayi shiru , sai chan nace , nayi sauka haddatar alqur'an"
"Masha Allah , sauran fah" cewar malam
"Alhamdullah , munyi littafai da dama
Fiqhu munyi -ahlari,ishmawi,da iziya
Sai hadith kuma -arba'una hadith, hakkun mubeen, da sauransu
Sirah kuma -murshidul-d'allab
Tauhid kuma-kitabuttauhid etc.""Masha Allah, kice kawai malam aka kawo mana " cewar malam yana murmushi
"Aaa , malam " na fada cikin tsoro
"Tohmmm bismillah bari a miki interview" cewar malam
"Tohmmm malam" nace masa
Mikewa yayi ya kira wani malam yazo
Suka hadu su biyu kenan
Take wani tsoro ya kamani, na d'aga kaina naga su Ahmad ni suke kallo
Haka na daure,
Malam ya muko min alqur'ani
Na girgiza mai kaiBismilla yayi ya fara jawomin aya a cikin suratul tauba
Nayi bismillah na kama cikin zazzakan muryata, haka na cika office din da kira'ata
Haka nayi tayi har saida malam ya tsaidani
Ya kuma gawomin suratul ankabut ,
Na karanta masa, ya koma suratul nisa'i shima na karanta,
Sai dayan malamin ya ringa mun tambayoyi ,a cikin littafai
Ina basa amsa,
Sai naji malam yana cewa,"barakallahu fiki , wa fatahallahu alaiki"
Muka hada baki wajen cewa"amin"
Sai malam yace" tohmmm yanxu gaskiya babu ajin da zaa iya saki , amma muna Neman alfarma ki taimakawa kannen ki kina zuwa koyardasu nan, kafun nan da wata daya insha allahu , zaa bude jss1 , gini ne bai kammala ba"
Shiru nayi bance komai ba
Sai Ahmad yayi gyaran murya yana cewa"malam babu damuwa insha allahu, zata fara zuwa, insha allahu gobe""Masha Allah, Allah yasaka da alkhairu" cewar malam ya fada cikin farin ciki
"Haba malam ai mune da godiya " cewar Mubarak shima
*Alhamdullah aikuwa yau ne zanyi tambayan da ya Dade yana damuna , gashi ban samu Wanda zai amsa min ba,*
Ina cikin tunani naji Ahmad yana ma malam sallama
Sai sukaji ina cewar "malam dan Allah ina da tambaya "Sai gaba dayansu, suka kalloni yace"tafaddal"
Sai naji shiru sanna nace "malam ayi hakuri da tambayan da zanyi, tambayan na Dade ina Neman amsa sa amma Allah baiyi ba , sai yau zan tambaya"
Sai malam yace"babu komai"Sai na fara cewa................
YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......