Page 47

190 10 0
                                    

A mota iman duk ta galabaita ,Sai biyu ana 'tsayawa tayi amai ,duk ta Basu tausayi ,suna isa mubarka ya tambaye iman me  zata ci kafun su karasa gida
Tace "fura "
Ai kuwa suka tsaya suka siya rufaida fura ,tun a kan hanya ta shanye roba daya

Aka siyar ma su mommy da malam

Suna isa aka kiran sallar magriba ,sauke auta sukayi ,Ahmad baya son yaje gidan mommy tace iman ta zauna

Suka bada sakon fura a kai musu da gidan malam

Sai suka wuce gidan mubarak , a chan sukayi sallah suka ci abinchi

Yau babu laifi matan mubarak ta sake da iman ,ba kaman da ba ....
Sai bayan sallah isha'i suka wuce gida

Ahmad yayi da iman ta tashi tayi wanka tace "bacci take ji "
babu yanda beyi da ita ba Amma taki tashi
Mikewa yayi ya tafi toilet, Ruwan wanka maid'an zafi yahad'a, sannan yafito.

     Idon iman  alumshe taji an dauketa  cak.

    Da sauri taware idonta akansa, yad'age girarsa duka yana kallonta, bazata juri kallonba, sai kawai ta lumshe idanunta.
Atare sukayi wankan, konace yamusu, Dan duk Ahmad  ne k'arfin komai, iman  duk batada wani kuzari ajikinta.

     Dakansa yadawo da'ita cikin daki ,  Ya dakko cream dinsa nai suna nivea  ya shafa , yasaka jallabiyya coffee brown color mai gajeren hannu.

Iman  kuwa  goge jikinta Kawai tayi ,tayi cumbing kainta ,ta shafa body spray burinta kawai ta kwanta.

    Tana gamawa Ahmad ya taimaka mata ta sanya  gown na bacci , daya  ajiye mata mara nauyi sosai, fara mai adon bak'ak'en furanni,  me hannun vest , rigar tamata k'yau, iyakarta cinyarsa .

     Ita kanta saikuma kallon kanta takeyi amadubin, tasan rigar tagama amsar jikinta, kaikace saida aka gwadata aka d'inka (su hajiya iman a kwana lafiya babu wani rahotun da zan iya kawo wa😂😂😂😂)

Mikewa Ahmad yayi yace bari ya dakko mata ruwa ,Dan yanxu tashin shan ruwan dare takeyi .........

    yana dawowa yaga  barcinta taketasha ya girgiza kansa, d'aukarta yayi ya gyara mata kwanciyar  , ya  rufeta  da blanket , alwala yaje yayi ,yayi  sallah sanna shima ya  kwanta, yagyarama iman  kwanciya ajikinsa.

    Hannunsa daya  Na saman cikinta yana shafawa, tareda tunanin wai akwia  dan Adam a ciki?,ikon Allah kenan ,yagadai randa cikin iman  zaiyi girma😊.

  Itakam bama tasan yanayiba, tuni barci  yayi  gaba da'ita😂😂😂😂😂...................

~~~~~~~~~~~~
Mommy kuwa tun bayan laasar ta shiga kitchen tana girka na iman abinchi ,Dan wake tayi mata da Tuwon masara miyan karkashi ,Sai kunun aya da ginger drink ,ta girka ma daddy da auta ,jalof din spaghetti

Har daddy ya dawo suna palour suna jiran zuwansu Ahmad (kina ruwa mommy😂😂😂😂)

Tana shiga yin sallah magrib auta ta shigo ,tana idarwa ta shiga dakin auta da zuman ganinsu tare da iman ,Amma taga akasin haka kuwa 😂💔

Zaman jiran auta ta idar da sallah tayi mata bayani ,

Aiko auta na yin sallama mommy ya tambayeta inasu Ahmad ,auta tace "yoooo mommy sun wuce gidansu magrib yayi ,anty iman Sai amai take tayi a hanya ,shine suka wuce ......."

Salati mommy ta fara ,tana tafa hannun irin taga abun mamaki "watohhhh Ahmad ya girma da har zatace abu ,Amma yaki ehhh lallai" cewar mommy cikin tsananin fada

Autan ganin fada zai koma kanta sai kawia ta Kabbara sallah ta fara.....

Mommy ganin auta ta tada sallah ,Sai kawai ta koma falo tana ta fada

A haka daddy ya dawo ya sameta ,tana ta fada ,
Shi daddy dariya ta bashi ,ta dage tana ta fada..

Auta tana idar da sallah ,ta dauki fura ta saka hijab ta wuce ta Kai ma su malam

Bayan ta dawo ta dauki na su mommy ta Kai musu ,mommy tace bata sha ,zama auta tayi ita da daddy suka sha furansu ,
Anan Jan mommy ya kuma baci sosai sosia,
Tashi tayi ta wuce ta kwaso abinchin da ta ma su ahmad ta saka a fridge.
Ta wuce daki abunta😂😂😂😂

A haka su daddy suka gama zamansu shi da auta ,suna gulman mommy 😂😂😂😂(nima gulmanta nayi a zuciyarta,)
Bayan sallah isha'i .
Su biyu suka ci abinchi mommy taki futowa ..........

Sai da daddy ya koma daki ,ya lallabe yar matanshi
Tace zata kira Ahmad ta bashi hukunchi ,da kyar daddy ya lallabe mommy yace ta bari Sai da safe .....

Da sassafe wajen 7am ,mommy ta daga waya ta kira Ahmad................(uhmmmm kaka kaka kaya ,ga Akuya ga kura 😳😂😂.....)
Ga Ahmad ga mommy ahhayyeeeeee💃💃💃💃💃

sabuwar rayuwaWhere stories live. Discover now