Sallama nabi daki daki Ina musu, masu bina da fatan Alkhairi suna yi masu sharri suna yi abunka da gidan yawa.
Haka de na gama na koma daki dan hada kayana da suka rage, Wanda baxan tafi dasu ba in adana Su
Nasan hamma zai Kaini,
Da malam yaso suzo daukeni, shine babana yace aaaaa. Kunsan abunka da dangin mamanka, suna sonka sosai.Sanda hamma ya fara min horn , nan ne nasan da gaske barin gida zanyi,
Nan take zuciyata tafara tsinkewa ,
Hawaye suna kokarin zubominA haka na samu na tafi wajen baba yi masa sallama.
"Assalamu alaikum Babana
Barka da rana
Dafatan ka wuni lafiya"Waalaykumus sallam ,
Barka dai
Lafiya qlau. Ya shiye shirye,
Dafatan babu matsala'Babu komai wallahi lafiya kalau, daman nazo in maka sallama ne " cewar iman cikin ladabi
"Toh toh toh madallah, Allah mahalicchimu ya baki saa a rayuwa, ya tsaremin ke duk Inda kike, Allah ya baki miji na gari
Duk da nasan kin kokarin rike mutumchin ki, amma Dan Allah ki kara sosai ,
Duk da nasan kina da biyaya amma ki kara , kiyi ma kakan ninki biyaya sosai ,
Ina alfahari da ke 'yata
Allah ya miki albarka
Jeki hamma na jiranki"Cewar baba da yaji babu dadi, duk cikin yayansa babu Wanda yaji babu dadin rabuwa da su irin iman
"Hajiya na tafi, hamma na jirana"
Cewar iman kenan, tana kokarin boye hawayenta"Toh iman, Allah ya bada saa ,
Ki gaida su malam
Sai Nazo" cewar hajiya , itama duk tayi sanyi"Zasuji insha Allah, sai anjima"
Tafiya nake yi zuciyata a tsinke ,
Ina tafiya ina kallon kowani sashi a, zuciyata kaman zata futo, haka har na futa gaban gida inda hamma yayi packing motarsa
Nayi kokari na share hawayena"Barka da rana hamma, Dan Allah kamun afuwa kata jirana tun dazun" cewar iman tana kokarin boye damuwarta sanin waye hamma
Babu komai , shigo mu tafi
••••••••••••••••••••••••••••••••
"Ahh nifa mallam bangane irin wannan wankan ba kaci wannan uban shadda haka kaman zaka daurin aure" cewar Umma da ke zaune tsakar gida
"Barni inyi amarya ta zata iso yau ai Dole inyi ehe, banson surutu" cewar malam
"Tofah ummah kice se kin tashi tsaye kan amaryar nan tun kan taxo har an fara dokin ta" cewar Ahmad, yana dariyar mugunta
" dannan tayani ganin wannan alamarin fa ai yafi karfi na kwata kwata Allah de ya kawo ta lafiya" cewar Umma
Ameen Umma.
"Nima de zanso ingan ta Dan wannan zumudin da Kaplan yakeyi ba a banza ba' cewar Ahmad yana dagawa malam gira data
"Bawani nan nama fita kyau fa, kawai de malam ne da fitinan sa"
"Au ai se kice kishi kike yi mana"
"Kaji mallam akan me xanyi kishi da kwailar nan "
"Hhhhh wai kwaila zamu gani ai"
•••••••••••••••••••••••••••
Sai wajen karfe 4:00 pm muka kawo garin kano
Saboda hanyar babu kyauMalam yana jin horn ya mike da saurinsa yana murmushi
Yana cewar" barka da zuwa amaryata , marhaban "Nima na maida masa da murmurshi ina cewar" alhamdullah yau gani ga angona, , oyoyo"
Nida hamma muka tsunguna muka gaida malam tsoho, sannan muka shiga cikin gida, cikin farin ciki da annashuwa.
"Salam, amaryata nasan tsohon nan ya hanaki zuwa mun oyoyo, Allah ya fishi" cewar hamma cikin zolaya
"Wslm angona, lallai malam kishi nasa yayi yawa, ko fada min baiyi ba zaka zo, ai dako lalle nayi maka" cewar umma
"Hhhhhh malam naga jikinka har rawa yakeyi "cewar Ahmad tare da mikawa hamma hannu suyi musabaha

YOU ARE READING
sabuwar rayuwa
RomanceIt's all about love, destiny,and fate. life is not always a bed full of roses......